Makalu

Sabbin Makalu

View All

Rai da kaddara 2: Shafi na ashirin da tara

 • "Hamma zan kirga daya zuwa goma, idan baka bude kofar nan ba zan karya in shigo"

  Yana jinshi, tunda ya karaso kofar dakin yaji takun tafiyar shi, saboda Khalid baya iya tafiya da takalmi baija kafa ba, har mamakin shi yakeyi, bashida wani nauyi balle yace jikinshi na yiwa kafafuwanshi nauyin da ba zai iya daga su yanda ya kamata ba. Daya kwankwasa  daga farko ji yayi kanshi da yake ciwo yana neman rabewa biyu, tun jiya yake damunshi da kira a waya sai da ya kashe wayar gabaki daya. Yazo ya kwankwasa ya gaji ya tafi, shine yau ya sake dawowa. Baya son ganin kowa.

  "Da gaske zan karya kofar"

  Karamin tsaki Salim yaja cikin zuciyarshi, ko tunani Khalid yakeyi ya mutu a cikin dakin bashida karfin da zai karya kofar batare da taimakon wani ba

  "Dan Allah ka bude, ba sai kayi magana dani ba, ka bude ko abinci in miko maka saika sake kullewa..."

  Murmushi ne yaso ya kwace masa amman ciwon da yake tsakanin hakarkarin shi ya rike duk wata walwalar shi

  "Hamma! Dan Allah ka bude, ko ka kunna wayarka kace mun kana lafiya, kuma kana bukatar kaci wani abu"

  Sake juya kwanciya Salim yayi, a kwanaki uku, biscuit ne yake ci, shima dan yasan jikinshi na bukatar abinci, yau da safe yana gama ci har ruwan da yasha sai da yayi amansu, dakyar ya watsa ruwa ya dawo ya kwanta. Zuciyar shi da duk wani abu da take da iko dashi a jikinshi ciwo yakeyi

  "Kuka ma sauki ne"

  Yaji mutane na cewa, sai dai bai taba sanin yana da wahala haka ba, ba wai don yana aiki a asibiti ba, yana zagaye da mutanen da suke da dalilin yin kuka kusan ko yaushe, amman ya zauna da Adee, film ma kuka yake sakata, meye ma baya saka Adee kuka? Ita ta saka shi jin kamar kowa na da iko da hawayen shi, sanda kake so su zubo zasu zubo, sai a kwanakin nan daya tsugunna, ya zauna, ya kwanta, ya tashi tsaye, amman hawayen shi suka nuna masa iyakar shi ta hanyar kin zubowa balle ya samun saukin da yake nema. Bacci ma yayi masa tawaye kamar sauran abubuwa, saboda daya rufe idanuwan shi abinda bayaso ne yake gani, idan bacci ya fisge shi mafarkin ne zai tashe shi.

  Ciwon kanshi yafi alaka da rashin bacci fiye da abinda yake zuciyar shi, ya rasa inda zai tsoma kanshi yaji sanyi, ko wanka yayi bayajin dadi, sai dai tun ranar yasan wani abu ya canza a tare dashi, abu fiye da daya, wani daga cikin abubuwan yayi canjin da har abada ba zai taba komawa dai-dai ba, amman a cikin canjin nan harda sallar da cikin kwanakin nan duk da bai fita masallaci ba yayi kowacce akan lokaci, harma ya daga hannuwan shi da nufin yin addu'a, sai ya rasa abinda zai roka, sai wani irin nauyin na zunuban da yanzun yake jinsu suka danne shi, kunya ta kamashi, a gefe daya kuma wani irin tsoro, tsoro da bai taba sanin akwai irin shi a duniya ba.

  Ko wannan ne maikon zinar da Khalid yake gudar masa? Karshenta kenan? Jin kunya? Idan har kunyar duniya ce wannan, dacin zunubin da yake tare da zina ne yake ciki yanzun, da wanne ido zai amsa laifukan shi a lahira? A gaban bainar jama'a? Faduwa Julde yayi, akan idon shi ya fadi, kuma yasan ba abinda ya danne shi yayi masa nauyin dauka sai tozartar da yayi a gaban idanuwan su. Yasan akwai abinda ya kamata yayi don neman samun sauki, amman kamar an shafe wasu sashi na kwakwalwar shi haka yake ji, sam ya kasa tuna komai.

  "Hamma dan Allah..."

  Muryar Khalid ta kutsa cikin tunanin da yakeyi, sai dai bayason ko motsa yatsan shi balle ya raba jikinshi da gadon, a kasan duk wannan kuma bayason ganin kowa, bayason magana da kowa, so yake ya zauna shi kadai, yayi jinyar abinda baima san girman illar da yayi masa ba har yanzun. Wajen aiki sako ya tura cewar bashi da lafiya

  "Har yanzun bai fito ba?"

  Yaji muryar Nawfal, ya runtsa idanuwan shi ya bude, kiranshi Khalid yayi, Nawfal ya kira, kuma yasan yafi Khalid din naci. Nawfal zai iya wuni a wajen idan har bai bude kofar ba, kuma ba zai daina kwankwasawa ba tunda yasan bayason irin wannan hayaniyar, yanzun ma daga zuwan shi harya fara jibgar kofar

  "Hamma..."

  Kunnen shi ya juyo masa muryata ta tsakanin bugun kofar da Nawfal yakeyi, zuciyarshi da tayi luf a kirjinshi kamar ta soma gajiya da dokawa saboda jinyar da suke fama da ita tayo wani tsalle kamar zata fito waje, kafin ta koma mazauninta tana cigaba da wani irin dokawa sai kace a lokacin ta fara aiki

  "Hamma..."

  Ta sake kira tana sakashi sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske

  "Hamma dan Allah ka bude"

  Ta fadi cikin wata irin murya da tasa tsikar jikinshi mikewa, sai yaji kamar ta fama masa ciwukan da yakeji, a lokaci daya kuma ta fifita masa su, baisan ya akayi ba, kafafuwan shi suka fara saukowa daga gadon, saiya tsinci kanshi da takawa har wajen kofar yana murza mukullin ya bude kofar, ya kuma yi dai-dai da lokacin da Khalid yayi baya yana kawo duka karfinshi da nufin karya kofar, kaucewa Salim yayi sai ga Khalid din ya fada cikin dakin ya kuma yi wanwar a kasa

  "Hamma..."

  Ya fadi saboda ya bugu sosai, yaji wani abu yayi kara, bai dai tantance kashin kugunshi bane kona hannun daya fadi a kai, koma daya daga cikin hakarkarin shi

  "Kasan ba zan tareka ka sokeni da kashi ba ko?"

  Salim ya fadi yana kallon Khalid da yake mayar da numfashi

  "Ina jin na karya hakarkari"

  Cewar Khalid yana kokarin mikewa hadi da yatsina fuska

  "Koya karye ai ba wata matsala fa Hamma, an rigada an zari na matarka"

  Hararar Nawfal Khalid yayi

  "Dan an zari na matata sai akace bakomai dan sauran sun karye?"

  Numfashi Salim ya fitar yana dafe kanshi da yake sarawa, hannu ya mika ya kamo na Khalid yana mikar dashi

  "Ja numfashi"

  Kallon rashin fahimta Khalid yake masa

  "Bana son maimaita magana Khalid kasani, kaja numfashi"

  Numfashin yaja

  "Fitar..."

  Yanda Salim din ke nazarin shi na saka shi yin duk abinda yace, kafin ya kai hannu yana danna kowanne cikin kasusuwan hakarkarin Khalid din yana kuma saka shi yaja numfashi ya fitar

  "Fitar mun daga daki"

  Wannan karin Khalid din Nawfal ya kalla, kafin ya kalli Salim

  "Daga fitar da iska sai kuma fita daga daki Hamma"

  Yanda Salim ya daga ido ya kalle shi yasa shi rabawa ya fita daga dakin, Nawfal ya kalla, saiya kafe shi da ido

  "Ba zan tambayeka ko kana lafiya ba Hamma, amman karka sake boye mana haka, Hamma Khalid yayi kokarin karya kofa ne kawai, kasanni, idan ya kama a sauke bangon nan zanyi"

  Numfashi Salim ya sake fitarwa

  "Baka da hankali"

  Kai Nawfal ya jinjina

  "Nasani, shisa nake rokonka karka sake"

  Ganin yayi shiru yasa Nawfal cewa

  "Hamma"

  Kai Salim ya jinjina masa yana dorawa da

  "Naji Bajjo... Na jika"

  Saboda Nawfal din ya tsare shi da idanuwa, Khalid ya kalla yana masa alama da su bar wajen, saboda Madina tana tsaye a gefe tana kallon su kawai. Tun da Murjanatu tazo bai kwana a gidan ba, duk da yazo jiya, yaune baiyi niyyar zuwa ba, abinda zaiyi da yawa, haka nauyin da yake ji a kirjin shi

  "Zai iya yiwuwa, Bajjo zai iya yiwuwa Babanta ne"

  Kwanaki biyu kenan da Daada ta fada masa maganar da yaji kamar ta kwada masa guduma a kai, yanda ta kalle shi yasa shi sanin duk wani abu da zata sake fadi yana da karfin da zai iya girgiza shi, kafafuwan shi zasu iya yi masa barazana, shisa ya samu waje ya zauna a gefen gadonta. Hasashen shi ya zama gaskiya

  "Lokaci yayi, da ya kamata ku san komai, ba kai da Madina kawai ba, har su Khalid, nasan ko kafin kuyi hankali, fita da kukeyi cikin sauran mutane kun fahimci kowanne mutum yana da ahali, ko da a gidan marayu ya taso kuwa, akwai dangin da bai sani ba a wani wajen suna rayuwa, kamar yanda nasan tunda kuka fara hankali kuka san dole kuna da wasu yan uwan, dole muna da tushen da ba'a garin Kano ya fara ba...Bajjo Kano maboya ta zamar mana, Marake ne asalin mu, Marake ne tushen mu..."

  Sanda ya bar dakinta kamar an watsa masa ruwan kankara yake ji, yasan akwai sirrikan da suke binne a zuciyarta, akwai kuma ciwon da take tare dashi da yafi karfin binciken likita, amman bai hango kaddararta na da girma haka ba, baima dauka mutum daya zai iya daukar abubuwan da suke kan Daada ba, daban yake kallonta yanzun. Ko magana takeyi, ko murmushi tayi saiya dinga kallonta, saiya dinga neman hawayen daya kamata ace tana zubarwa ya rasa. Sai yaji yana so ya riketa a jikin shi, yana so yayi mata rumfa, rumfar da zata zame mata kariya yanda wani abu ba zai sake tabata ba. Yana so kuma ya maye mata gurbin duk wani data rasa take kewa, shima saiya tsallake yayi mata nisa.

  Yau akwai yanda ya tsara zata kasance masa, a ciki banda zuwa nan, Khalid yayi masa text cewar har yau Salim yaki bude kofar, wayarshi a kashe, saiya kira Khalid din, wayarsu Madina taji tace saita biyo shi, yaso yace mata ta zauna, saboda babu komai a zuciyarshi sai son ya nisantata da inda Julde yake, amman yanda ta tsaya tana kallon shi idan yace ta zauna zata nemi sanin dalilin da zaice mata ta zauna, Daada tace bata tambayi ya akayi ta dawo gida ba har yanzun, bata san meya faru ba, gara mutuwa ta dauke shi kafin ya fada mata dalili

  "Muje"

  Kawai ya iya ce mata, ta ruga daki ta sakko karamin hijab ta dora saman riga da wandon da yake jikinta, ko Nawfal yace kayan sanyi. Murjanatu sun fita ita da Adee, yanajin suna fama da Madina tace zatayi wa wasu kunshi, yasan halinta, in da gaske kunshin zatayi ba zatace zata bishi ba, kawai bata son fitar ne. Yaji dadin zuwan nashi saboda zasuyi magana da Khalid, ya bashi labarin nan ko zai rage nauyin da yake ji, ya kuma fada masa abinda yake tunanin aiwatarwa. Tare da Khalid sukayi dakin shi, suna barin Salim da Madina, sai lokacin ya daga ido ya kalleta, wandon jeans ne a jikinta, rigarta ta kusan zuwa gwiwa, sai karamar hijab blue, ya tabbatar ba wannan rigar kadai bace a jikinta

  "Mug"

  Ya kira, da duka hankalinta baya kanta ba zataji shi ba, dagowa tayi, ta kalle shi, fuskarshi duk tayi gashi a wajajen da bata taba gani ba, yayi zuru-zuru, idanuwan shi sun sauya launi. Tun data tashi ta ga Daada a kusa da ita take son tambayarta yanda akayi tazo, kallon da Daada takeyi mata kamar tana rokonta karta tambayeta komai, zuciyarta rawa take yi mata tun ranar har zuwa yanzun, ko meye ya faru tasan mai girma ne, saiga Nawfal shima, yana kallonta kamar yayi mata laifi, yana kallonta kamar yana yi mata alkawarin ba zai sake bari wani abu ya sameta ba, duka yanayinsu saiya kara tsoratata. Ta kira Salim, ta kira shi harta bace lissafin ko sau nawa, amman wayar shi a kashe, ba don ta tambaye shi abinda ya faru ba, sai don taji muryar shi, saboda a yar karamar duniyarta, Salim ya zame mata wani waje da zata raba taji sanyi duk idan tana cikin halin kunci.

  Yau tunda tayi sallar asuba wata irin kewarshi take danneta, so takeyi ta ganshi, taji muryar shi, ta fito ta dauki ruwa ta ga Murjanatu da Nawfal a kitchen din, daga inda take tsaye ba zatace ga abinda suke fada ba, amman yana bayanta, ya rike hannunta da take rike da robar ruwa ya fadi wani abu dayasa ta daga kai ta kalle shi tana dariya, komawa tayi, har zuwa yanzun ba zatace ga dalilin da yasa ta koma ba, ta duba zuciyarta ta rasa me taji, koma menene kewar Salim saita danneta, komawa tayi ta kwanta tana daukar wayarta ta kirashi, a kashe har lokacin. Ta sauke wayar, hawayen da ya cika mata idanuwa na shirin zubowa, sallamar da Daada tayi mata na mayar da hawayen.

  Sai dai na wucin gadi ne, komawa sukayi don su tattaro yan uwansu suyo rubdugu wajen fitowa tare da kalaman bakin Daada, da labarin da yayi mata tsaye, labarin kuma daya hade mata tambayoyin da take dasu tun sanda taci karo da wasikar Yelwa. Tayi kuka, Daada ta riketa a jikinta ne batare da tayi yunkurin hanata kukan ba, batasan bacci ya dauketa ba saida ta farka, Daada bata dakin, tayi wanka ta fito ne taga Nawfal, suka taho. Ta dauka hawayenta na yau dai sun gama karewa, sai yanzun da taji sun cika mata idanuwa

  "Mug..."

  Salim ya kira yana dakuna hadi da girgiza mata kai, yau kwana uku da yayi alkawari a cikin kanshi, macen duk da hannun shi zai sake tabawa zai zamana akwa halarcin yin hakan, amman ta tsaya a gabanshi, tana kallon shi idanuwanta cike taf da hawaye kamar tana rike da wata damuwa ne da ba zata iya bari kowa ya gani ba sai shi

  "Daada ta fadamun Hamma, komai..."

  Komai din data fada na dukan zuciyar shi, sai yaji kafafuwan shi na rawa, shisa ya koma cikin dakin yana zama a kasa ya jingina bayanshi da gadon dake dakin yana kallonta, a bakin kofar ta zare takalmanta tana shiga dakin ta zauna a gefen shi itama tana jingina bayanta, ko ina na jikinshi rawa yakeyi, data bude bakinta sai yaji kamar ya katse ta, kamar yace mata abinda zata fada ya sani, abinda zata fada abune da ko lokaci ba zai goge masa ba, sai tayi masa bazata, sai ta fara bashi wani labari da ta kowacce fuska ya shafe shi amman jinshi yakeyi kamar almara, kamar wani abu da ya kamata ace a litattafi ko fina finai ya faru, ba'a rayuwar mutane ba, ba'a zahiri ba.

  Sai dai ita kanta Madina bata san Daada ta tace wasu abubuwan daga cikin labarin ba, balle kuma Salim da yake jinshi daga bakinta

  "Ina so in gansu Hamma, su duka biyun, bansan me zance musu ba, amman ina so in gansu"

  Ta karasa tana kai hannu ta goge hawayen da take jin sun zubo mata

  "Daada tace Adda Murjanatu taga wani a Abuja, tace sunan shi Kabir...tace muna kama..."

  Kai yake girgiza mata, duka yau suka ji labarin nan, idan ita ya gama zauna mata, shi kam zaiyi karya idan yace ya gama zauna masa, sannan bashi kadai bane abinda yake damunshi a yau, abubuwan sunyi masa yawa shi kadai

  "Karki je wajen nan yau, kar muje wajen nan yau Madina, bari mu numfasa da duka abubuwan nan tukunna...idan bashi bane bafa?"

  Ya karasa yana kallonta, idanuwanta sun sake cika da hawaye

  "Idan shine kuma fa?"

  Ta amsa tambayar shi da tata tambayar

  "Hamma ka dubamun, dan Allah ka dubamun... Ba zan daga burina ba, nayi alkawari, amman ina so in sani..."

  Kai yake daga mata, ba Abuja ba, yanda tayi masa maganar, ciwon da yake cikin idanuwanta, idan a karkashin duniya akace anganshi, zaiyi kokarin dagata ya duba mata shi, alkawarin da yayiwa kanshi sai ya bace masa lokacin daya kama hannunta ya rike a cikin nashi, hotonta akan gadon a kwance, da Julde a tsaye ya dawo masa, yana saka shi kokarin cire hannunshi daga nata, sai yaji ta dumtsa, ta sakala yatsunta sun zauna a ciki kamar an halicce sune kawai don su sarke cikin juna, da idanuwan shi suka sauka cikin nata sai kalaman Julde suka dawo masa

  "Ban mata komai ba..."

  Sai son kareta daga faruwar komai din ya cika zuciyar shi, sai son samunta kafin ta haramta a wajen shi ya lullube shi kamar bargo, ya dago hannunta da yake cikin nashi yana kallo, ya sake kallonta

  "Ina son ki"

  Kalaman suka subuce masa, a karo na biyu daya fada mata, karon farko batayi mamaki ba, saboda tasan ko bai fada ba yana sonta, ko bata fada ba tana son shi, akwai wanda zaice baya son dan uwan shi? Jinin shi, amman yau idanuwan shi a cikin nata suke, kuma idanuwan Salim, a gabanta basa boye abinda yake ji, zuciyarta ta yunkuro tana komawa cikin idanuwanta da take kallon shi, saboda itama tana son fahimta sosai, asalin ma'anar kalaman shi

  "Nasan da yawa, son da nake miki, amman bansan yana da girma haka ba sai da naga kamar na rasaki..."

  Wannan karin mazauninta zuciyar ta koma tana bugawa, sautin bugun da take ji har cikin kunnuwanta

  "Bai faru ba, babu abinda ya faru, daga yau zan tabbatar da babu abinda ya tabaki, kina jina?"

  Tsintar kanta tayi da daga masa kai

  "Ina son ki..."

  Ya sake fada kamar yana so kalaman su zauna mata fiye da yanda soyayyarta take zaune a kowanne gurbi na zuciyar shi...!

  *

  Comments da likes din karku gaji, idan kunyi like ku daure da comment din, sai mu koma whatsapp mu sha hirar acan, na fada zan kara tuni ne kawai, da su zan samu a biyani. Nagode da tarin goyon bayanku.

  Idan kana da account sai ka sake yin sign in zaka iya yin comment da like, sannan ka dawo ka danna kan link din.

  #SonSo

Comments

12 comments