Makalu

Sabbin Makalu

View All

Rai da kaddara 2: Shafi na talatin da biyu

 • Nagode da fatan alkhairi

  Nagode da tarin addu'o'inku

  Wanda suka kira, sako ta whatsapp, text, wattpad harma wanda suka turo ta email dina domin tambayar lafiyata, nagani, nagode kwarai, Allah ya saka da alkhairi

  Na kuma gode da uzurin da kukeyi mun.

   

  *

   

  Shekaru goma sha bakwai ana neman hada ta sha takwas din, a cikin shekarun tayi numfashi da sanin adadin shi sai wanda ya bata ikon yi, sai dai a tsayin lokacin, a cikin kowanne shiga da fitar numfashinta akwai kewar ahalinta, wata irin kewa da zatace ta danne ruhinta dan idan tace zuciyarta kamar yayi kadan. Kewace mai cike da taraddadin ya lafiyar su take, duk da wautar tunani bata kawo mata rasa wani a cikinsu ba a tsayin shekarun nan. Ko a tunaninta abune da ba zata iya dauka ba. Musamman da idanuwanta suka sauka kan Daada, da taja numfashi ta fito dashi tana jin wani nauyi da yake danne da zuciyarta ya daga, ta runtsa idanuwanta ta bude su yafi a kirga a kasa da dakika, tana son maida hawayen da suka cika mata idanuwa suna hana mata ganin hoton Daada tar a cikinsu.

   

  Sai maganganu kala-kala suka dinga turereniya a cikin kanta, har tana rasa wanda ya kamata ta fara furtawa, shisa ta zabi

   

  "Daada...Daada Am"

   

  Suna fitowa daga wani lungu na zuciyarta, tazarar shekarun da tayi batare da Daadar ba na hadewa da ita waje daya. Da ta karasa cikin dakin sosai, saita durkusa a gaban Daada, kafafuwanta na gode mata saboda ko da bata taimaka musu ba gab suke da kasa daukar gangar jikinta duk kuwa da yanda take jinta sakayau, kamar fallen takarda. Sai dai har zuwa lokacin ta rasa abinda zata sake cewa,ta sauke kanta, hawayenta suna diga akan kafet din dake shimfide cikin dakin, data dago da kan ma hawayen ne suke zubo mata, tanajin karar hancinta da taja na komawa cikin kunnenta da wani irin yanayi saboda shirun da yake cikin dakin 

   

  "Nayi kuskure"

   

  Ta furta cikin kanta

   

  "Ki yafemun?"

   

  Kalmomin suka biyo bayan wadancan duka a cikin kanta, kuskure ta sani, ta kuma fada a waccen haduwar da sukayi, daga lokacin da taji hannun Kabiru a cikin nata bayan auren da aka daura musu suna sauka garin Kano, ta kalli mutumin da yayi mata wakilci, ta juya ta kalli wanda yayiwa Kabiru wakilci sai Malamin daya daura musu aure da shine cikon mutum na uku, kuskuren da tayi ya danneta, amman ya zatayi da soyayyar Kabiru? Duk da a lokacin bata hango rabon da yake tsakaninsu ba, kuskuren kawai ta gani. Ta kuma sake ganin a daren da suka dorar da auren su zuwa wayewar gari, tayi wani irin kuka, ta wuni tanayi batare da ta samu saukin nauyin da zuciyarta tayi mata a rikon da Kabiru yayi mata cikin jikin shi yanayi mata rumfa ba

   

  "Inajin kamar ya kamata in baki hakuri Yelwa, kamar ya kamata inji ban kyauta ba dana raboki da ahalinki, na so kaina da yawa nasani. Amman zuciyata bata dana sani, haka girman soyayyarki ya rufemun ido, na kasa damuwa da laifin da nayiwa ahalinki na raboki dasu Yelwa, ina taso inji rashin kyautawar nan amman na kasa"

   

  Kanta kawai ta sake binnewa a cikin kirjinshi, hawayenta na cigaba da zuba, saboda in zata fadawa kanta gaskiya, a tsakanin nauyin zuciyarta da kuskuren da take jin tayi, akwai soyayyar shi, akwai kaunar da takeyi masa da bata san yawanta ba. Ko yanzun da take son juyawa ta koma gida, zai wahala yafiya ce abinda zata fara rokansu, idan ta saka gwiwoyinta a kasa a gaban Datti tana da yakinin abinda zai fara fitowa daga bakinta ba zai wuce

   

  "Dan Allah Baba karka rabani da Kabiru..."

   

  Da kalamai kwatankwacin wannan, sannan ta roke shi ya yafe mata ta kara daya taimaka ya fahimci girman son da take yiwa Kabirun da yasa ta tsallake su ta bishi. Ko yanzun ma da take durkushe a gaban Daada, dana saninta baya jingine da auren Kabiru, kewar su da tayi tafi komai yawa. Hannu ta dago ta share kwallar da ta riga ta gangaro mata, ta dan juyar da kanta ta kalli Kabiru da yake tsaye, idanuwan shi akanta, kamar zubar hawayenta yake jira yagani su bashi izinin karasowa yayi irin zaman da tayi a gefenta, cikin son nuna mata yanda ba zai taba barinta ita kadai ba. 

   

  A tsayin zamansu, tun tana jiran ranar da Kabiru zai nuna mata halinsu na maza da akafi yi musu tambari dashi harta daina, tun tana jiran alhakin bijirewa iyaye ya kamata ta wannan fanni saida ta daina, ba zatace basu taba fada ba, za dai tace a kowanne lokaci laifin nata ne, zata kuma ce na rana daya Kabiru bai taba biye mata ba, karshen abinda zaiyi ya nuna mata ranshi ya baci shine ya saka takalman shi ya bar mata gidan, da zuciyar shi tayi sanyi idan ya dawo bayan sallama, lokutta da dama yakan dora da

   

  "Kin huce in shigo? Ko in har yanzun bakya son ganina?"

   

  Wasu ranakun kuma

   

  "Yunwa nakeji Yelwa, in shigo ki taimaka ki bani abinci ko fushin bai bari kin girka mana ba?"

   

  Mazan da ta sani a rayuwarta basu da yawa, a tsakanin kawaici irin ma Hammadi da sanyin hali na Bukar, zatace Kabiru ya hada duka ya kara da wasu halayen nagartattu. Zai wahala kaga fuskar shi babu wannan murmushin da kyallin shi yake haskawa har cikin kananun idanuwan shi. Shisa a hankali ya koya mata kwantar da hankalinta, natsuwar da yake tare da ita kullum tayi mata inuwa harta mike kafafuwanta, saboda ta dauka kalubalen su daga bangarenta ne kawai kuma sunyo masa nisa.

   

  Tunda da sana'arshi ta fitar da dabbobi suka dogara, tafiye-tafiyen shi basu taba damunta ba. Ta hadu da nagartattun makotan da ko a barin da tayi na farko da Kabiru baya nan bataji rashin yan uwa a kusa da ita ba, sunyi mata taimakon da sai da yasa ta hawaye saboda batayi tsammanin a zaman su tayi musu wani abu da ta cancanci wannan karamcin ba. Sai dai mutanen arziki ba sunayi maka kirki bane dan kayi musu, karamcin ne cike da zuciyar su shisa rarrabashi baya taba yi musu wahala. A kowacce tafiya idan zaiyi tana ganin damuwar nisan da zaiyi mata cike da idanuwan shi

   

  "Ina ta duba garin da masu irin sana'ata basu yawaita ba mu koma, bana son yanda nake barinki ke kadai"

   

  Ya fadi kamar a lokacin yasan wannan tafiyar tashi zata zama sanadi na farko na jirkicewar lamurran su. Murmushin da tayi masa cike yake da kokarinta na karfafar shi. Bata hango tsakanin wannan murmushin nata da wani akwai wata tazara mai nisa ba, sai dai satika hudun da yakanyi duk idan yayi tafiya suka shige babu amon shi balle kuma labari, sai ta daina lissafi da kwanaki lokacin daya hada watanni uku, cikin jikinta kuma ya shiga watan da lissafi ya nuna cewa yana gab da fitowa duniya.

   

  Sauran lissafin da take tare dashi ya karasa kwacewa ne ranar da ta fito daga bayi tana kokarin zama dan daura alwala wata mata ta shigo mata gida babu ko sallama tana kallonta da fadin

   

  "Yelwa ko?"

   

  Tana da yakinin mamakinta ya bayyana akan fuskarta

   

  "Baki sanni ba nasani, matar Kabiru ce"

   

  Abinda yayi saura na zuciyarta da baya tare da Kabiru taji yana barazanar fitowa daga kirjinta

   

  "Kin dauka kinyi nasarar rabamu zakiyi rayuwa dashi ke kadai ne? Ke kin isa yayi mun saki uku ke ki rayu dashi? Waye ubanki?"

   

  Kafafuwanta Yelwa taji suna rawa wannan karin

   

  "Ki nemarwa cikin jikinki uba idan rabon shine ya hada hanyarku, amman in dai Kabiru ne, ni kuma ina da sauran numfashi yanda nabar shi ya barki kenan. Na so in barki ki cigaba da duban hanya, amman ina son kallon idanuwanki ne kamar yanda nake son kiga fuskata"

   

  Ko da ta fita bayan

   

  "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

   

  Da ta furta wani zazzabine ya danneta, kafin tashin hankali ya fara barazana da rayuwarta. Ba kirga kwanaki takeyi ba ballantana a lokacin tasan kwana nawa ta hada kafin tunanin komawa Marake ya dirar mata, ta dai san in tayi numfashi sai abinda yake cikinta ya motsa mata kamar yana tuna mata da yanda take wata rayuwa a tsakanin duniya da lahira. Sai wani sabon firgici ya sake danneta akan wanda take ciki. A wajen Kabiru ta koyi rubutu da karatun hausa tunda gatan da Datti ya nuna musu bai barsu sunyi karatun ba duk kuwa yanda Dije taso su dashi, haka kawai safiyar data tashi da nufin tafiya Marake wani abu yake fada mata ba zata rayu da abinda yake cikinta ba, wannan abin na sake tabbatar mata da macece, a lokaci daya kuma yana sakata rubuta wasikar da bata da yakinin zata isa inda take son isar da ita.

   

  Sai dai ganin Datti a kwance ya kara birkita mata komai, daren nan da ta kasa mantawa har yau na dawo mata, muryar shi bayan ta roke shi daya yafe mata, raunin da yake cikin muryar lokacin daya furta

   

  "Soyayyar da nayi muku laifi ce Yelwa? Me yasa kuka kasa gane kune gabaki daya duniyata? Ko dan nima ban kara tabbatar da hakan ba sai da kuka zabi kuyi mun nisa naga fadinta? Na jini ni kadai? Komai ya tsayamun yana sakani tunanin inda na kuskure a tawa soyayyar..."

   

  Ya karasa muryarshi na karyewa tare da wani abu a zuciyarta

   

  "Na yafe miki..."

   

  Hawayenta suka zubo

   

  "Zuciyata na ciwo, sosai..."

   

  Kai ta daga hawayenta na zubowa, tasan itace silar komai, saita dauka tunda ta tafine ya kwanta ciwo, ta bude bakinta da nufin sake rokon shi ya yafe mata sai yaja wani irin numfashi da bataji ya fitar dashi ba, kafin zuciyarta ta buga tare da bayanta daya amsa

   

  "Kin kashe shi"

   

  Wata murya ta fada mata a cikin kanta. Kuma ko da ta fadawa Daada ta kashe shi a lokacin batayi kokarin musa mata ba. Ta san ta haihu, saboda ko mahaukaciya ta san da, balle kuma ita da ta haihu cikin hayyacinta. Zata tuna wankan da Daada tayi mata, kayan da ta saka mata, yarinyar da ta damka mata a hannunta don ta shayar da ita. A cikin wannan firgicin ne wani irin abu ya tsirga mata daya sakata ajiye yarinyar tana mikewa tsaye. Wannan abin daya tsirga mata shine yake tunkudar zuciyarta da wani irin karfi daya shallake ikonta. Ko yarinyar da kukanta ya isa kunnenta da wani yanayi batayi tunani ba balle takalmi da mayafi, saboda abinda yake fisgarta yana gaya mata ta bi hanya kawai.

   

  Hanyar kuwa tabi, hanyoyin da ba zata iya gane su ba, saboda ba'a cikin hankalinta take tafiyar ba. Bata kuma san ko wani yayi nufin taimakonta da abinci inta karba sai dai taci shi tana tafiya saboda inta zauna sai taji wannan abin yana fisgarta komin zugin da kafafuwanta sukeyi mata na alamun gajiya. Kamar yanda bata san ta shafe shekaru biyar a wata irin duniya da ko makiyinta bata fatan ya shiga ciki. Kafin wata safiyar juma'a data canza mata komai, tana tafiya kawai ta tsinci kanta a gefen titi kamar wadda take yawo a mafarki saboda karshen abinda zata tuna shine ta haihu, shine tana cikin dakin Datti, sai kuma rasuwar shi, sai ta ganta a gefen titi a tsaye, kafafuwanta babu ko takalmi cikin wani yanayi daya nuna gararambar da ta sha.

   

  Haka kuma bata san cewa a wannan juma'ar ake taron suna a wani gida, a daya daga cikin sababbin unguwanni masu tasowa a lokacin a garin Kano, sanadin wannan sunan da za'ayi sun kira me majalisi don shagali a kofar gida, katon dutsen da tunda suka siyi filin, har akayi gini yana nan gefe, samari suka taru suka saka karfi wajen mirgina shi don a kara samun wajen da mutane zasu tsaya su kalli majalisin da za'ayi, a kasan dutsen kuma suka ga katuwar layar da basu tsaya dogon tunani ba suka warwareta, daya a ciki ya bada shawarar a kone zaren da layar duka, suna jinjina neman duniya irin na mutane, da kuma tunanin wa akayiwa wannan mugun abin aka danne da wannan dutsen da Allah kadai yasan shekarun da yayi a wajen.

   

  Da yake Allah ya yanke mata wahala, sai sanadin samun saukinta ya biyo ta hannun mutanen da ko a titi zai wahala kaddara ta hadasu balle tayi tunanin gode musu. Da taimakon mutanen kauyen da take gararamba aka dorata a motar Kano, da tambaya da komai ta gabo Bachirawa, unguwar da gidansu yake, unguwar da taga ta canza mata gabaki daya saboda gine-ginen da akayi, da wata tambayar da taimakon Malam Malami mai almajirai da suke layi daya a wancen lokacin ta gano gidanta, gidansu ita da Kabiru. Harta karasa ta kwankwasa kofar gidan batayi tunanin za'a bude ba, har yau kuma ba zata manta yanayin fuskar Kabiru ba.

   

  Ba zata manta yanda bai iya ce mata komai ba sai hannunta daya kama yana janta zuwa jikinshi yayi mata wani riko tamkar an mishi alkawari karuwar kwanakin shi a duniya idan ya riketa. Haka ba zata manta dumin hawayen shi da suka sauka akan kafadarta ba. Sun kwana a gidan, shi yana da labarin bayarwa, ya fada mata yana son dawowa gida amman saiya kasa, da yayi yunkuri sai yaga wani duhu da tunanin shi na dawowa gida yake bacewa a ciki, abokin cinikayyar shine ya kula da hakan, ya kuma tsaya kai da fata wajen karbo mishi taimako wajen wani Malami har abin ya karye, sai dai daya dawo ya nemeta bai ganta ba saiya koma, ya nemi abokin shi inda cikin rashin sa'a suka tarar Allah ya amshi rayuwar Malamin, zargin abinda ya same shi shiya sameta yasa shi bin duk wani Malami da zaici karo dashi wajen neman ya taimaka masa da addu'a akanta, amman karshen abin baizo ba.

   

  Ya koma Marake kuma, labari ya samu na taje can, harta haihu, sai dai babu wanda yasan inda take daga nan, haka ma su Daada, a 'yan uwanta yaji labarin Yelwa data haihu ta gudu ne saboda abin kunya, Daadar ma saita kasa zama, anman anfi kyautata zaton Kano ta gudu inda Julde yake da zama. Wani zance daya daki zuciyar shi, bakinshi yayi masa nauyi wajen fada musu abinda Yelwa ta haifa ba ta hanyar da suke tunani bane ba, saboda idan ya fada wacce shaida zaiyi amfani da ita wajen gamsar dasu gaskiyar shi? Daya dawo Kano saiya rasa gabas zaiyi ko arewa, garin Kano da girma, ta ina zai fara neman su Daada? Idan ya gansu kuma bai samu Yelwa a tare dasu ba ya zaice? Wanne labari zai basu? Ya gudo musu da yarinya ta kuma bace a karkashin kulawar shi?

   

  A cikin labaran shi duka da ido Yelwa ta dinga binshi, saboda ita bata da labarin bashi, yasan ta haihu, yasan mace ta haifa, yasan mahaifinta ya rasu. Ina taje? Me yasa ta tafi? Me takeyi a wannan shekaru biyar din duka bata sani ba, mahaukaci koya warke bashi da labarin bayarwa tunda hankalin da zai rike faruwar abubuwan ne gabaki daya ya kubce masa. Ta dai fada masa tsohuwar matarshi tazo, ta kuma fada masa maganganun da tayi mata wanda har yau suke mata yawo

   

  "Sahura?"

   

  Ya tambaya da mamaki shimfide a fuskar shi, ranar taji sunanta, sunan da bata so ta sakeji ko a mafarki. Sun sake kwana a garin Kano, sai dai Kabiru ya tsorata, shisa suka bar Kano 

   

  "Fadan nan ya wuce ayi cacar baki, ko a ware aji karfin juna Yelwa, fadan da Sahura ta dauka damu fadane da in ba imaninmu zamuyi nisa dashi ba Allah yana iya sake bata nasara akanmu dan ya sake jaraba mu, gara muyiwa Kano nisa, muyi nisan da sai dai a buga kasa a bata labarin mu wanda zai iya zama gaibu za'a gaya mata, idan wani abin ya sake samun ki ba zan iya yafewa kaina ba"

   

  Yanda ya karasa maganar, ramar da tagani a tare dashi da yanayin da yake cikin idanuwan shine abinda yayi galaba akanta ta bishi, bayan tarin alkawurran da yayi mata na cigaba da neman ahalinta da kuma alkawarin yanda ya rabota dasu zai sake sadata dasu cikin hukuncin Ubangiji. Sai gashi ya cika mata wannan alkawarin a lokacin data cire rai da samuwar hakan. Dan har suka hawo mota jinta takeyi kamar a cikin mafarki take yawo, mafarkin da bata farka ba sai yanzun da ta ganta a gaban Daada, sai yanzun da taji hannun Daada rike da nata. Sai ta dan karkata kai tana kallon Madina da ta zuba mata ido ta cikin gilashin da yake makale da fuskarta.

   

  Yarinyarta

  Yarinyar da rabonta yasa ta tsallake komai a karo na farko

  Yarinyar da ta haifa kaddara ta sata tsallaketa tare da komai a karo na biyu

   

  Sai wani abu ya tsirga mata, ta sake kallon Daada da tambayar da bata iya furtawa ba, Daada ta daga mata kai kamar ta karanci tambayar

   

  "Madina..."

   

  Daada ta furta muryarta a sarke saboda kukan da yake son kwace mata, sai Yelwa ta rigata, saboda bayan hawaye sun zubo mata, da taja numfashi tazo saukewa saiya taho da wata irin shessheka da ta kasa dannewa

   

  Gata a cikinsu

  Gata a gabansu

  Amman agogon da take ji cikin kanta na tuna mata lokacin da ta rasa a tare dasu da kuma wanda bata dashi a yanzun.

   

  *

   

  Comments da likes din karku gaji, idan kunyi like ku daure da comment din, sai mu koma whatsapp mu sha hirar acan, na fada zan kara tuni ne kawai, da su zan samu a biyani. Nagode da tarin goyon bayanku. 

   

  Idan kana da account sai ka sake yin sign in zaka iya yin comment da like, sannan ka dawo ka danna kan link din.

   

  #SonSo

Comments

13 comments