Makalu

Kiyaye wadannan abubuwa guda biyu zai taimaka gaya a rayuwa

 • Nazari da kuma lura da rayuwar mutane daban-daban da suka samu nasara a cikin rayuwarsu ta duniya, sun nuna cewa sanya wa kai hadafi da dauwama bisa alkibla na cikin manyan abubuwa da ke taimakawa gaya wajen cimma burin rayuwar da adam. Ko me ake nufi da hadafi da dauwama bisa alkibla?

  Hadafi

  Hadafi, watau ‘goal’ a Turance, yana nufin wani muhimmin kuduri da mutum zai sa a gabansa da nufin cimma sa. Duk mutumin da yake so rayuwarsa ta amfaneshi, duniya da lahira, dole ne ya sanya wa kansa hadafi. Hadafi ga rayuwa tamkar alkibla ce ko kuwa kararrawa wacce a koda yaushe ta ke tunatar da mai rayuwa inda ya dosa a tafiyar da yake yi. A misali, hadafi shike sanya dalibin makaranta ko matashi ya kuduri anniyar me yake so ya zama a rayuwarsa, injiniya ne, likita ne, dankasuwa ne, malamin makaranta ne, mashahurin malamin addini ne, ko kuwa sadaukar da rayuwarsa zai yi wajen yiwa al’umma hidima?

  Mutum na iya sanya wa rayuwarsa hadafi ta haryar lura da magabata wadanda suka yi nasara a rayuwarsu; ta hanyar kula da ire-iren hadafai da suka sanya wa kansu kuma da ire-iren hanyoyi da suka bi suka cimma nasarar wadannan hadafai. 

  A takaice, muna iya cewa sanya wa kai hadafi shi ke haifar da jajircewa, da kwazo, da juriya wajen kokarin cimma burin rayuwa. Duk mutumin da bashi da hadafi, to bai san inda rayuwarsa ta dosa ba.

  Dawwama akan alkibla

  Idan mutum ya san hadafin rayuwarsa, ma’ana ya fuskantar da tafiyar rayuwarsa zuwa ga wata alkibla wacce yake so ya kai gareta, to yana da kyau ya dawwama bisa wannan alkibla. Yawan canje-canjen alkibla shike kawo abinda ake cewa ‘ba wan ba wan karatun dankama,’ watau, mutum ya zama bashi ga wannan bashi ga waccan, ko kuwa yau ya fara wannan, gobe ya saki ya kama waccan. A cikin shekaru kalilan na mutum sai ka ga ya taba sana’o’i sama da goma, kuma babu kwaya daya da ya kware a ciki, ko kuwa za a iya yi masa inkiya da shi.

  Za a iya karanta: Almajiranci da illolinsa cikin al'umma

  Hakika, fadi tashin rayuwa mafi yawancin lokaci kan sanya mutane gwada abubuwa da dama don samun abinda za su dogara dashi. Gwada wani sabon abu idan na farko ya ki, babu laifi, amma mutum ya fara wani abu, bai yi hakuri har ya fahimci menene alfanunsa ba, nan da nan ya yi tsalle ya koma wani abun bai kawo nasara a rayuwa.

  Abinda na san maikaratu zai yi tambaya a nan shine, har tsawon wani lokaci mutum zai iya tsayawa bisa wata alkibla tashi kafin ya canza? Wannan tambaya bata da takamammen amsa a wurina. Abinda kowa ya fi sani shine, duk abu sabo da mutum ya sanya a gabansa, karatu ne, kasuwanci ne, zaman tare ne ko makamantan haka, akwai lokacin ban sha’awa na farko-farko, a kwai lokacin shiga gargada da matsaloli wanda shi yafi tsawo a cikin tafiyar, akwai kuma lokacin koyo da gyare-gyare wanda ya fi duk sauran lokutan wahala, sannan akwai lokacin daidaituwa, lokacin da mai hadafi ke bukata matuka, sannan yana yiwuwa samu lokacin da wannan al'amari zai sauko kasa ya kara shiga gargada (in Allah Ya yarda zan rubuta makala ta musamman akan wadannan lokuta tare da kawo misalai na yadda suke faruwa).

  Duk wadannan lokatai da muka zayyana, zuwansu ya banbanta daga hadafi zuwa hadafi, watau ya danganci irin abunda mutum ya sa a gaba yake burin cimma. Don haka lokacinda mutum zai ga yanzu ne ya dace ya canza alkibla don ganin wannan bata tafiya, ya doru kacokan ga shi mutumin da kuma irin yadda ya fahimci al’amuran da ke tafiya. Magana mafi anan shine, indai mutum yana so ay ci gajiyar abinda ya faro, to akwai bukatar hakuri da juriya wanda shi ke kawo dawwama bisa wannan abin.

  Saboda haka, yana da kyau mu sani cewa nasara bata samuwa sai mutum ya san me yake son cimma, wato menene hadafin da ya sa a gabansa, kana dole ya jajirce da hakuri bisa tafiyar da yake yi, ya dawwama har ya ga cewa ya cimma burinsa. Ubangiji Allah Ya sa tun farko mu yi dace da hadafi mai kyau garemu kuma Ya bamu karfin guiwan jajircew a kai.

  Kuna iya karanta makata na gaba don wani tahalili game da abubuwa guda uku makamantan wadannan dake taimaka wa dan adam wajen cimma burin rayuwarsa.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Sat at 12:17 PM

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All