Rubutu

Blogs » Ra'ayoyi da Tahalili » A maganar matsalolin da suka shafi aure, yan Arewa muna da sauran tafiya mai nisa

A maganar matsalolin da suka shafi aure, yan Arewa muna da sauran tafiya mai nisa

 • Jiya na iso wurin aiki da safe, sai na iske wani abokin aikina, dan kasar Saudiya, yana gyaggyara Shimag na shi zai shiga aji ya karantar. Shimag shine dan kyallen nan da larabawa ke yafawa a kansu. Cikin raha da zolaya, sai na ce masa, cikin Turanci, ‘getting set?’ ma’ana, ‘yaya ana kimtsawa ne? Budan bakinsa sai yace, ‘kwarai kuwa, kimtsawa na asali ba!’ Fadar haka sai ya jawo hankalina. Labarin da ya bani daga karshe sai ya sani na fahimci cewa lallai mu fa a Arewacin Najeriya matsalar da suka shafi aurenme suna da da yawa, kuma idan ba mun fuskanci gaskiyar al’amarin ba to baza mu kai gaci ba.

  Wannan ba shine kawai labarin da yasa nake rubuta wannan makala tawa ba. Wani abu makamancin haka game da auren wani shima abokin aikina amma dan kasar Ingila ya taba faruwa. Wadannan labaru guda biyu sun sani zurfin tunani game da matsaolinmu a Arewacin Najeriya, kuma shiyasa nake so na yi bayani yau akansa.

  Bari na fara da labari na farko na dan kasar Ingila. Shidai wannan abokin nawa asalin iyayensa yan kasar Pakistan ne amma sun zama yan Ingila, kuma a can aka haife shi, kasarsa kenan. Muna aiki da shi a tsangayar koyar da Turanci a kwalejin koyar da sana’o’i dake Yanbu na kasar Saudiiyya.

  Shi wannan abokina nawa yana so ne ya auri wata yarinya ce diyar wani dan kasar Malaysia wanda shima abokin aikinmu ne. Saboda haka, baban yarinyar abokinsa ne, sun saba sama da shekaru akalla bakwai. Sun san labari da asalin iyalan juna, misali a zaman da ake yi iyaye da yan’uwa kan kawo ziyara, don haka a tsakaninsu duk sun san iyayen juna, sanin da da za’a iya cewa zai gamsar da mai bida ko bayar da aure.

  Karanta: Abubuwa guda uku da ka iya janyo nasara a rayuwa

  Don haka wannan ya sa da ya bayyana wa abokinsa cewa yana so ya auri yarsa, ya amince wato bayan ya tabbar ita yarinyar tana son sa. Bisa al’ada na aure, a tsakanin su iyalan biyu, kowa ya samu labari kuma yan’uwa sun gamsu da juna. To amma me zai faru? Wannan shine abinda ya ja hankalina, kuma shine nake so mai karatu, musamman dan’uwa na dan Arewa ya gane.

  Duk da gamsuwa da amincewa da wadannan iyalai guda biyu suka yi, a dokar kasar Malaysia, duk wanda zai auri diyarsu, ko a ina take a fadin duniyar nan, kuma ko daga ina shi mijin ya fito, sai ma’auratan biyu sun yi tattaki sun je kasar Malaysia, sun je kotu ta amince kafin a yi aure. Wannan bayani da angon ya gaya mini kenan wani lokaci gabannin hutu yana irin shirin tafiye-tafiye da ke gabansa.

  Ba abu kadan kotu ke bincike akai ba kafin ta amince da wannan aure. Daya daga ciki akwai maganar gwaji a asibiti. Gwajin nan kuwa ba ya shafi kawai maganar cutar kanjamau ba ne da sauran cututtuka, alalhakika ya shafi duk wani gwaji na lafiya da zai iya shafar ma’auratan har ma da abinda za su iya haifa, misali kamar gwajin genotype da makamantansu.

  Bari mu koma labarin abokin aikina na biyu wanda shine na fara baku labarinsa a farko. Kuna iya tunawa dama yace mini ‘yana kimtsawa ne na gaske.’ Ashe abinda yake nufi da haka shine, sakamakon gwaje-gwaje ne na shi da na yarinyar da zai aura ya fito, kuma an samu nasara sakamakon ya nuna za su iya auren juna.

  A wannan rana ne na samu hujjar cewa, a nan kasar Saudiya idan ma’aurata za su yi aure, dole ne sai sun je hukuma ta yi gwaje-gwaje kuma ta amince. A takaice dai wannan doka ya yi daidai da irin dokar kasar Malaysia wanda ya shafi daya abokin aikin nawa da ya yi nufin auren diyarsu.

  Kada ku yi wani kokwanto, ga dukkanin wadanna kasashe guda biyu, idan gwamnati bata yi bincike ta amince da aurenku ba zai taba yiwuwa ba.

  Amma abin mamaki da takaici, irin wannan gwaje-gwaje na kafin a yi aure, yana daga cikin babban kalubale dake fuskantarmu musamman a Arewacin Najeriya. Ma’aurata, iyaye da hukumomi sun kasa amanna dashi; dukka wadanda abin ya shafa ba sa ma son su yi maganar ko don al’ada ko wani dalilai.

  Bai ma dace a kawo zancen addini ba saboda addinin Musulunci shine ma yace a yi bincike ba don komai ba sai don kawo gyara da kuma gudun cutar da dan adam. Wannan shi ya sa a sigar karba da bayar da aure waliyai ke tambayar lafiyar mai aure da wacce za’a aura.

  Ba sai na yi bayani ba, kowa ya sani aure baya yiwuwa a coci-coci sai an yi kyakkyawar bincike da ya shafi lafiya, kuma rashin sakamakon da ya dace yakan iya wargaza wannan aure.

  Don haka, kada mu danganta wannan matsala da addini, sai dai kawai kamar yadda aka saba a kullum muna zaben abinda ya dace ne kawai da son ranmu a cikin addini, mu yi amfani dashi. Abinda kuma zai kawo mana cikas a burinmu sai mu sakaye shi cikin al’ada, mu ki fadar gaskiya akai.

  Ire-iren wadannan abubuwa mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Allah ya kara masa lafiya, ke ta fada da Arewacin Najeriya a kai, abubuwan da suka shafi yawan aure-aure ba ka’ida, da sake-saken aure barkatai, da rashin kulawa da abinda aka haifa – duk mai hankali ya san wadannan manya-manyan kalubale ne a Arewacin Najeriya. Su suke haddasa talauci da matsaloli daban-daban da muke ciki, harma da wanda ke shafar kasar baki daya.

  Abin dubawa anan shine, gwaji kafin a yi aure muhimmin abu ne da zai taimakawa ma’aurata wajen rage hadura. Rashinsa na iya jefa su da abinda suka haifa cikin matsaloli da zai iya dawwama cikin rayuwarsu. Likitoci sun sha yin bayanin abinda ke kawo cutar sikila ya hada da rashin dacewar genotype na mata da miji.

  Ba dole ne bayan gwaji ace aure ba zai yiwu ba, amma idan aka san yanayin da Allah ya yi wa kowa, Likitoci na iya bada shawarwari ta yadda za’a samu saukin duk matsalar da za’a iya shiga ciki.

  Mai karatu na iya duba: Kiyaye wadannan abubuwa guda biyu zai taimaka gaya a rayuwa

  Wadanda nauyi ya rataya akansu su tabbatar da wannan gwaji sune shuwagabannin al’umma, yan siyasa da kuma taimakon malamai. Tabbas gwamnati ce ke da babban gudumawa. Ko shakka babu, hukumomin gwamnatocin da na yi bayani a kansu ba wai don mutane na so ne aka sanya musu dokan gwaji gabannin aure ba, sai don su gwamnatocin sun san da cewa hakkokinsu ne su kare yan kasa.

  Gyaran al’umma da ya shafi gyara al’ada ba abu ne mai sauki ba. Muna sane da tarihin yadda Shehu Usman, Allah ya gafarta masa, ya kawar da zalunci ya kuma jaddada adalci da Musulunci a kasar Hausa. Kana muna da labarin irin gwagwarmayar da manyan malamanmu irinsu Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma’ila Idris suka sha wajen dawo da al’umma bisa hanyar Allah da Manzonsa, duk da cewa irin hikimomi da suka yi amfani da su sun sha babban da irin hikimomin da malaman sunnanmu ke amfani da su a yau.

  Don haka, hakki ne da ya rataya ga jagororinmu na yanzu su tashi. Akwai matsalolin da dama da suke tattare da maganar aure a Arewacin Najeriya, babba daga ciki gwajin ma’aurata gabannin aure. Ko mu fuskanci gaskiya mu gyara – daga shugaba har talaka – ko kuma yaki ya ci mu. Allah ya sa mu gyara.

Comments

4 comments