Makalu

Sabbin Makalu

View All

YANAYIN RAYUWA

 •               Short story......1-to end
  Tunda ya shigo gidan yake kalle-kalle musamman yadda kamshi ke dukan hancinsa na turaren wutan. Murmushi yayi na jin dadi, sai dai yana kara kusantar kofar shiga falon kamshin abincin ya daki hancinsa wanda hakan ya k'ara jefasa cikin wani sabon nishadin da Allah-Allah ya shiga dan inda abunda khamis keso baiwuce yaci girkin matarsa Walida ba a koda yaushe.

  Da sallamarsa ya shiga falon ya tadda ta zaune cikin shigarta ta kana nan kaya, wanda tana ganinsa ta tashi cikin dan sauri-sauri cikin murmushin ta me kara daukar hankalin angon nata khamis. Tsayawa yayi yana kallon yadda jikinta ke motsawa duk taku da wannan murmushin nata me kara nitsar dashi cikin soyayyarta.

  Yayi nisa sosai harta k'araso ta rike ledar hannunsa baiji zuwan nata ba. Ganin yadda ya kafeta da idanu yasa Walida murmushi me dan sauri cikin sanyin muryarta tare da shafo hannunsa. Jin lallausan hannunsa cikin nasa ya saki ledar ba tare da ya shirya ba. "N...na...'am". Ya furta a dan firgice tare da dauke kansa dan kokarin nemo nutsuwarsa. "Sannu da dawowa, Habibi". Ta fada cikin sansanyar muryarta tare da dan kara kusantarsa jikinsu na gogar na juna.

  Lumshe idanunsa yayi tare da rungumota cikin sauri saboda dumin jikinta daya dakeshi. Bangaren Walida hakan haifar mata da wani yanayi na tashin hankali yayi. Sanadiyar rasa numfashinta daya kusa daukewa saboda irin tsami da dukan da jikin mijin nata yakeyi. Sun dau lokaci a haka yayinda bata da wani buri irin na ya saketa daga wannan rikon dan ko numfashi ta kasa.

  Gogan kuwa dadi yake ji musamman yadda kamshin jikinta ke tashi ya gama rudewa da fita hayyacinsa a wannan lokacin. A hankali ya soma shigar da hannayensa cikin lallausan fatarta, yayinda yayo kasa da kansa yana kokarin hada bakinsu gu guda. Sai dai the more yake getting closer the more wani wari ke kara kai mata hari tun tana kokarin jurewa hardai ta samu ta janye daga rikon daya mata.

  Sosai hakan bai masa dadi ba sam. Ganin yanayin fuskarsa yasa ta kirkiro murmushi ta daura kan fuskarta. " Habibina, ya kamata muje kayi wanka inyaso saimu ci abincin ko?". Ta fada cikin siririyar muryarta dan karya gane janyewar da tayi da wani abu. Murmushi khamis yayi. " Ae ni yunwa nakeji wankan nan ba yanzu ba Baby". Ya fada lokacin daya ma kansa mazauni da kujerar dake gefensu. Nan Walida tayita fama dashi anma duk kokarinta hakan bai samu ba.

  Bayan sun kammala cin abinci nan ma tayi-tayi sai dai ba sauyi. Haka ya nemeta ba yadda zatai sai dai sam ta kasa sake mishi wanda hakan yasa sam baisama yadda yake so ba. kiss kuwa sam daya kawo take dauke bakinta koya damu ya kama ma bata yarda ta saki mishi yasamu yadda yake so. Walida namai matukar takaici da Mijin nata Khamis sosai wanda duka-duka Auren nasu ko wata ba'ayiba. Kuma da inzaije zance ba haka yake zuwa ba. Bayan haka bata fahimci matsalolinsa ba sai bayan sati da Auren ya fara fito da dabi'unsa kaya kuwa sai dai yayita maimaitawa haka wankan ma.

  Yau tana zaune kamar yadda ta saba tana damne-dannen wayarta taci karo da wani post na favorite online writer dinta a facebook Hafsat Moh'd Arabi na Leadership A Yau kasancewarta columnist dinsu tayi wani paged mai Suna 'Uwargida Sarautar Mata' wanda kana ganin irin hoton dake makale jiki zaka fahimci program ne dake magana kan Ma'aurata. Program din ya soma kamar haka:

  UWARGIDA SARAUTAR MATA

  Kazamin Namiji...

  Assalamu Alaikum! Masu karatu barkanmu da sake kasancewa daku a cikin wani sabon shirin namu wanda muke Kawo Topic daya shafi Ma'aurata domin kawo gyare-gyare da shawarwari. A yau Topic din namu zai tattauna ne akan KAZAMIN NAMIJI.

  Tabbas! Ana samun Maza masu wannan dabi'ar ta kazanta wanda zaka ga wani Namijin sam tsaftar jikinsa bata dame saba bare ta kaya. Wanda hakan baya daga cikin dabi'ar mekyau a musulunce. Dan tsafta abune mekyau a cikin musulunce tana daga abunda ke cika imanin mutum rashinsa kan kawo illa ga dan Adam Ibadarsa, lafiyarsa harma da mu'amularsa.

  Ilar Rashin Tsafta ga Ibada: Tabbas! Yakan yi illa ga Ibadar mutum misali, mutum yakan iya zama kan najasa, ko ya taba kayansa ta hanyoyi da dama wanda inba mai tsaftar kulawa bane tabbas zai iya kallon gabas dashi. Wanda hakan ya kawo akasi me girma gunsa a wannan fanin na ibada.

  Illar Rashin Tsafta ga Lafiya: wannan shima babban abune wanda zai iya jawo koma baya ga lafiyar mutum. Dan wanda bai kula da tsaftar jikinsa ba taya zaikula da abunda zaisa a baki. Irin mutanen nan ba ruwansu da hannunsu da Datti ko kulawa da wankewa komai suka dauka zasu iya kaiwa baki basai nafada saura ba nasan anfahimta illar rashin tsaftar hannu da lafiya a wannan zamanin da cututtuka sukai yawa Allah yasa mudace ya kara tsarewa Ameen.

  Illar Rashin Tsafta ga mu'amula: Taya zakai magana da mutumin da bazaka iya zama inuwa daya dashi ba saboda tsami da hamami dake faman tashin jikinsa? Ko kaga mutum yana magana ana kakkau dakai meyasa? Amsar wannan shine bakinsa na Warri. Taya zaka jera da mutumin da kayansa a squeezing koma duk dauda wanda kowa na iya gani? Bakanta kenan bama hanyar mu'amula mekyau ga al'umar waje bare azo kan cikin gida wannan kenan.

  A nan nake jan hankalin 'yan uwana mata da maza damu kula sosai da Tsafta. Manzo Allah S.A.W yace "Matan bani isra'ila sun yi zina saboda kazantar Mazajensu, saboda haka kuyi ado ga Matayenku" ya kuma ce "Eh Yiwa Mata ado yana daga abinda yake dasu kamewa, Hakika Mata suna barin kamewa idan Mazajensu basa yi musu Ado". Ko a nan yakamata a kara sanin amfanin Tsafta. Domin idan baka da Tsafta zaka iya jefa Matarka ga mugun abu dan wani kan iya burgeta a waje wanda idan aka sama akasi sai a kaiga abunda za'ayi dana sani. Allah shikyauta.

  Gareku mata...

  Yar uwa idan Allah ya azurtaki da irin wannan Namijin. To kokari zakiyi kisan shi sosai saboda kawo gyara dawuya anma karki gaji koki manta dan Aure dama ibada ne kuma kuma gyarashi kanki kikama.

  Da farko idan yadawo aiki ki zaunar dashi cikin lallami yadda kikasan zai karkato da hankalinsa gareki da wasa kijashi zuwa wankan inta kama ma kuyi tare dama kitabbatar ruwanki na ajiye tunda kinsan lokacin dawowarsa.

  Na biyu: Dasafe idan yadawo masallaci ko yayi Sallah shima kibita lallami wajen sashi yayi wanka. Kafin ya fito kin tanadi kayansa kinsa turare kin ajiye mishi daya fito zaisa.

  Na uku: idan ya cire kaya ya warwatsar kitattare kigyara idan wanki kuke kaiwa akai inkuma ke kikeyi ki wanke.

  Yau da gobe kina mishi haka harsai soma sabawa yaji dadinda randa baisamu hakan ba zaiji badadi sai angwada akansan na kwarai. Shiyasa 'yar uwa ba'aso kiyi sake tun lokacin da kuke Amarci yakamata ki fahimce shi da matsalolinsa ana shaukin Amarci lokacine da zaifi daukar sauyin da zaki iya kawo masa cikin sauri. Ba kibari sai kun tara yara kizo kina kuka ba.

  Ajiyar Zuciya Walida ta sauke tare da ajiye wayarta. Tabbas! Maganganun writer din ya burgeta matuka da haka tasa a ranta zata kawo sauyi a rayuwar Auratayyarsu. Haka zata nemi Marubuciyar dan neman karin shawarwari.

  Da farko da Walida ta soma ta dan sha wahala saboda aikine babba anma kasancewar tana son mijinta baisa ta gajiba ta ci gaba tare da Addu'a. Cikin ikon Allah dan watanni kadan komai ya mata dai-dai. Yau ma kamar kullum khamis ne yadawo ya tarar da ita a kitchen.

  " Wannan kamshi haka Baby". Ya fada yana murmushi tare da rungumota ta baya. Murmushi Walida tayi ta ajiye abunda ke hannunta ta juyo bangarensa. " Ae yau bazaka ciba na babyna ne". Tafada tana shafa dan cikinta wanda ya soma fitowa. Kai idanunsa yayi kan babyn yana murmushi. " Anya wannan babyn bazai kwace mun guba kuwa tun bai fito ba ansoma komai ace nasa kuma ae ba naki bane ke daya dakike babynki". Ya maida mata amsa.

  Nan suka cigaba da zolayar juna na mintuna. " Kinga agajiye nake baby. Hope akwai ruwan wanka dan jikina har wani yam-yam yakemun?". Ya tambaya yana kallonta. Murmushi yayi tare da girgiza kanta. " Yes, waya isa ace bai hadama ruwan wanka ba ae saika yi wujiga-wujiga dani". Tafada tana dariya. Murmushi Khamis yayi ya fice. " Bari naje na watsa". Sosai Walida kejin ranta fari duk sanda ta tuna Rayuwarsu ta farko da yadda ta tarar da mijin nata.

  A nan muka kawo karshen wannan short storyn sai a cigaba da binmu dan samun mu dauke da wasu labaran.

Comments

0 comments