Makalu

Blogs » Zamantakewa » Kamuwa da so, da kuma yadda mata da maza ke soyayya

Kamuwa da so, da kuma yadda mata da maza ke soyayya

 • A yau, bayananmu na zamantakewa zai tabo muhimman abubuwan guda biyu game da so da soyayya. Wadannan abubuwan su ne “Kamuwa da So” da kuma “Yadda Maza da Mata Ke Soyayya”.

  Kamuwa da so

  Mafi yawanmu muna faɗa wa rayuwar aure ne kawai sakamakon kamuwarmu da so, wato yayin da kawai muka haɗu da wanda ya ja ra’ayinmu ya burge mu ko kuma ya yi daidai da abubuwan da a kowane lokaci suke ɗaukar hankalimu; waɗanda da zarar mun gan su a tare da mutum, sai mu ji babu tamkar ya shi.

  A wasu lokutan kuma, mukan fara kula wasu waɗanda ba su cika waɗancan sharuɗa ko kamanni da suke burge mu da sunan soyayya ba; a irin wannan yanayin, ba su cika samun kulawarmu sosai ba, domin ana kallon irin wannan ne a matsayin irin abinda Bahaushe kan ce. “A rashin uwa akan yi uwar ɗaki.” Amma sannu a hankali, sai a saba sosai da juna. Bahaushe kuwa da ma yana cewa “Sabo turken wawa.” Saboda haka, a sannu sai kawai mu ji mun shaƙu da waɗannan mutane, har ma mun manta cewa ba su ne nau’ukan mutanen da suke burge mu ba! Yayin da ɗayan waɗannan abubuwa biyu ya faru, sai kawai mu ji ai da gaske son juna muke, saboda haka sai kawai mu fara tunanin yin aure domin dukkanmu mun yarda cewa soyayya ita ce tubalin aure.

  A irin wannan lokacin, kafin mu kai ga yin aure, wata rayuwa muke ji muna yi tamkar a duniyar fina-finai ko mafarki; wata rayuwa ce mai cike da farin ciki da burace-burace, wadda zai yi wuya ka iya yarda da wasu batutuwan a irin wannan lokacin.

  Buƙatar so ba wai ya taƙaita ga ƙananan yara kawai ba ne, haka yake bin mu tun daga lokacin yarintar har zuwa lokacin da za mu girma mu kai munzali, har kuma lokacin da muka zama ma’aurata.

  Batun kamuwa da soyayya da ake yi, musamman tsakanin samari da ‘yanmata, da ma yana zuwa ne daidai da buƙatun zukatansu na lokacin. Ina nufin da ma kowannensu yana cikin tsananin wannan buƙatar ne. Kodayake, abin da ake kira da “kamuwa da so” yawanci soyayya ce da take da iyaka. Ma’ana ba ainahin soyayya ce da take ɗorewa dindindin ba; wata soyayya ce da masana suke ganin tana da iyaka, abar rayawa. Kodayake sau da yawa bayan mutuwa ko ƙauracewar wancan nau’in na so ne kuma idan aka yi dace sai sabuwar soyayya ta gaskiya ta girku. Saboda da ma can muna buƙatar soyayya tun muna yara, haka nan har zuwa lokacin girmanmu da yin aure, kuma za mu ci gaba da buƙatar ta har zuwa lokacin tsufa.

  Wannan dalili shi yake sa wa wata soyayyar ta yi tsayin rai, tun daga lokutan ƙuruciyar can har zuwa tsufa, amma haƙiƙanin lamarin shi ne, mafi yawa ba ainahin wancan nau’in soyayyar ce take ɗorewa ba, ana dai sauyawa ne daga ita ɗin zuwa wata. Akwai gaɓar da za mu tattauna wannan batu a can gaba, in sha Allahu.

  Karanta yanayin so da bukatuwarmu gare shi.

  Yaya maza suke soayayya?

  Idan so muke mu yi wa lamari kyakkyawar fahimta, sau da yawa asalinsa muke komawa, a haka ne muke iya gano ainahin inda ya samo siffa da ɗabi’a da dangoginsu. Annabin Allah Adamu (AS) ya kasance a cikin gidan Aljanna shi kaɗai lokaci mai tsayi, duk da cewa gidan Aljanna gida ne wanda ya ƙunshi dukkan wani abu na more rayuwa da ɗan Adam ka iya buƙata. Watarana sai ya wayi gari ya kasa samun sukunin more abubuwan alfarmar da ke cikinta; sukuni da walwalarsa su ka ragu, ya fara ji a jikinsa cewa lallai akwai wani abu da ya rasa. Ba komai ya dame shi ba a wannan lokaci face wahasha da ya tsinci kansa a ciki, wato halin kaɗaici, saboda shi kaɗai ne a cikin Aljanna.

  Da Allah subhanahu wa ta’ala ya yi nufin fitar da shi daga wannan yanayi, cikakkiyar fitarwa, bai turo masa aboki ko ɗa ba, sai ya turo masa mace, ita ce uwarmu Hauwa’u (RA), wadda zuwan ta shi ne ya zama sanadin korewar damuwarsa. Wannan tushen shi ne zai haskaka mana yadda rayuwar soyayyar maza har ma da matan takan kasance har zuwa yau, amma fa idan har za mu iya yi masa karatu irin na ta-nutsu.

  A ɓanbagare guda kuma, masana ɗabi’un ɗan Adam suna kwatanta duniyar maza da cewa duniya ce da duk mutanen cikinta suka shiga damuwa a wani lokaci, tare da cewa manyan jarumai ne kuma gawurtattun mafarauta sam ba su da wata fargabar farmaki daga wasu jarumai, haka nan kuma ba su da wani ƙalubale dangane da matsalar abinci, amma tare da haka, sai katsahan suka wayi gari cikin damuwa, komai ya daina yi musu daɗi! Suka koma cikin kogunan duwatsu suka zauna ba tare da sanin mene ne ainahin abin da yake damun su ba, har sai da labarin duniyar mata ya zo musu, suka kuma yi tattaki suka je har waccan duniyar, inda a can ne suka sami cikakkiyar nutsuwa sakamakon zamansu a tare da juna.

  Kafin wannan haɗuwa, masana suna kwatanta tsarin rayuwar maza (a junansu) da cewa tsari ne na ‘win/lose,’ wato ni in samu kai ka rasa, ko kuma ni in ci nasara kai ka faɗi, wanda har yanzu wannan tsari yana nan a cikin wasu wasanni na mazan, kamar a wasan “Table tennis” inda za a ga mutum ba wai so yake kawai ya yi nasara ta hanyar dawo da ƙwallon da ka buga masa ba, a’a, so yake wai kai ka kasa samun nasarar taryo ta, don haka sai ya bugo maka da ƙarfi ko kuma can wani gefe inda ba za ta taryu ba. Shi kuwa ba ruwansa, rashin nasararka ko a jikinsa in dai shi ya yi nasara.

  A duniyar mazan, a tsakaninsu, wannan ba komai ba ne, tsari ne da aka amince da shi. Ko ba komai dai kai ma ka koyi jarunta, yadda za ka iya dogaro da kanka. Amma bayan haɗuwarsu da mata, sai suka fahimci lallai matan ba za su iya rayuwa a kan irin wancan tsari ba, don haka dole tsarin ya sauya. Maza suka koma tsarin ‘win/win,’ wato ni in yi nasara kai ma ka yi nasara, in samu kai ma ka samu.

  Wannan sauyi kuwa ya faru ne sakamakon yadda siffofi da ɗabi’un da al’adun mata suka bayyana ga maza; ba su da ƙarfin dantse da juriya da jarumta da rashin tsoro irin na maza, don haka idan an tafi a kan wancan tsari su ba za su iya kai wa gaci ba kenan. Saboda mazan suna so matan ma su ci gaba da rayuwa, domin idan sun kasa rayuwa, mazan za su koma halin da suka tsinci kansu na damuwa da rashin walwala da baƙin ciki irin na baya kenan.

  Kuna iya karanta wannan makala da yayi binciken akan dalilai 11 dake sa namiji ya so mace matuka.

  Yaya mace take soyyya?

  Yayin da mata suka shiga damuwa suna cikin neman mafita, sai suka yi mafarkin maza suna kan hanyar zuwa duniyar tasu, waɗanda za su ba su kariya da kuma kulawa ta musamman. Da zuwan mazan waɗanda ƙarfafa ne, nan take kyan matan da ɗabi’unsu suka ƙayatar da su matuƙa, suka kuma yarda cewa tabbas ƙarfi da dabarunsu da ma ba su da wani amfani in dai babu wanda za su taimaka da shi. Wannan kuma shi ne abin da matan suka fi buƙata a wannan lokacin, wato a taimake su. Don haka sai yarjejeniyar zamansu ta kasance tamkar an yi ta ne bisa alƙawarin mazan za su ba su kariya, su samar musu abubuwan da suka gagare su na buƙatun rayuwa da kuma ba su kulawa ta musamman. Daga wannan lokaci sai dukkan wata damuwar mata ta ƙaura, suka fahimci ashe da ma shigar su ƙunci a baya ba komai ya janyo ba illa kaɗaici da rashin masoya.

  Maza da yawa ba su san ƙarfafar gwiwar mace abu ne mai matuƙar girma a wurinta ba, musamman daga wani mutum da yake da daraja a wurinta. Mace tana tsintar kanta a farin ciki kuma hankalinta ya kwanta da zarar ta sami tabbacin cewa wannan buri nata na samun wanda zai ba ta irin wannan kulawa zai cika.

  Yayin da duk mace ta shiga cikin tashin hankali da damuwa ko ƙuncin rayuwa, ko ma ta sami rashin nasara a wasu harkoki da take aiwatarwa, babban abin da ta fi buƙata shi ne a jiɓance ta, a shiga cikin lamarinta… ta ji cewa an damu da halin da take ciki… ta gamsu cewa ba ita kaɗai ce a duniyarta ba… ta sami tabbacin cewa ana son ta, kuma an damu da komawarta cikin farin ciki. Kusantar ta da ba ta cikakkiyar kulawa a wannan lokacin shi ne abin da zai dawo da ita hayyacinta.

  Amma maza ba su san wannan ba, saboda su a tasu duniyar, mutum ya fi so a bar shi, shi kaɗai yayin da yake cikin damuwa, don haka yayin da mace take cikin damuwa, kawai sai ya yi tafiyarsa ya bar ta ko kuma ma ya ƙara rura wutar damuwarta ta hanyar cewa zai warware mata matsalar. A wurin mace ba gwaninta ba ne da zarar ka ji matsalarta ka kama faɗi mata yadda za ta warware matsalar, domin babu kulawa ko nuna damuwarka a ciki. Abin da kawai za ta yi tsammani shi ne, ka katse ta, ka hana ta bayyana damuwarta. Maza ba su san yadda taya mace shiga cikin alhininta yake da matuƙar muhimmanci ba.

  Yayin da namiji ya ba mace dama, ya tsaya yana sauraren ta, tana bayyana damuwarta, sai baƙin cikinta ya rinƙa tafiya a sannu a sannu, tana ji a ranta cewa lallai burinta na fita daga wannan yanayin yana daf da cika. Ƙarfin gwiwarta zai rinƙa ƙaruwa a hankali har ta rinƙa ji a ranta cewa an karrama ta fiye da tsammaninta, sakamakon kulawar da ta samu. Idan ta sami wannan, abin da za ta ji tamkar an ba ta fiye da abin da ta cancanta ne.

  Ku karanta banbaci dake tsakanin maza da mata a zamantakewa.

Comments

1 comment