Rubutu

Blogs » Zamantakewa » Yanayin da jikinmu kan kasance yayin soyayya

Yanayin da jikinmu kan kasance yayin soyayya

 • Daga cikin abubuwan da sam ba ma kula da su game da soyayya, akwai yaren jiki (body language), tare da dibbun muhimmanci da yake da shi. Wato wani sashe mai bayyana ainihin labarin da yake faruwa a zukatanmu, wadanda sau da yawa ba ma so su bayyana ga wadanda muke tare da su.

  Masana a wannan fanni, suna ganin daga cikin hanyoyin da muke bi don isar da sako, kaso 7 ne kawai maganganun fatar baki suke isarwa. Amma sauran kaso 93 ana iya fahimtarsu ne ta hanyar motsin jikinka da kuma yanayin sautin muryarka.

  Tuni mun yarda cewa, idan mutum ya daga maka hannu ta hanyar nuno maka cikin tafin hannunsa daya, yana nufin ka tsaya ne. Amma yayin da ya fara damke hannun yana budewa a hankali, to yana nufin ka taho kenan. Muna kuma iya fahimtar murmushi alamar farin ciki ne, yayin da turbune fuska yake zama kishiyarsa. Haka idan muka ga mutum ya yi tagumi, sai mu ce. “Tunanin me kake yi haka?”

  Abin da kawai ba mu cika lura ba shi ne, wannan yaren na jiki, yana taka gagarumar rawa a duniyar soyayya.

  Dabi’unmu kishiyoyi ne

  Daya daga cikin manyan dalilan da suke sawa maza da mata suke yawan samun rashin jituwa, shi ne mafi yawan motsin da suke yi don bayyana ra’ayi ko manufarsu game da wani lamari, sun sha bamban da na juna. Inda za ka taras mace ta yi gabas, shi kuma namijin ya yi yamma, alhali kuma duk muhalli guda suka dosa.

  Misali, tun daga can farkon shigowa duniyar samarta da ‘yanmatanci, za ka taras yayin da namiji ya fara soyayya, to ko da can asali ba mai yawan magana ba ne, yanzu za ka ga bakinsa ya bude. Amma mace ko da mai yawan surutu ce, da zarar ta yi saurayi na farko (wanda kuma take so) to za ka taras bakinta ya rufe. Za ka taras wasu sabbin alamomin kunya sun bayyana a tare da ita, wadanda kuma za su tilasta wa bakinta rufewa.

  Idan namiji yana son ki

  Daga maza har mata dai, duk wanda ya tsaya ko ya jera tare da wanda yake so yayin tafiya, yana yin bakin kokarinsa wurin nuna cewa shi fa lafiyayye ne. Sai dai hanyoyin da suke nunawar sun bambanta, kamar yadda ayyukan da ake tsammanin kowannensu zai yi a cikin soyayyar ya bambanta. 

  Yayin da duk namiji ya tsaya a gaban mace, tsaiwarsa kawai za ta iya bayar da cikakken bayani, cewa yana son ta ko kuma dai kawai karfin hali ne.   

  Sabanin mace, namiji yana ji a can cikin zuciyarsa cewa hakkinsa ne ya ba wa mace dukkan kariya. Ya samar mata da kuma dukkan wasu bukatu da take iya bida. Don haka, yayin da ya tsaya a gaban mace idan har ta burge shi, kuma ta samu karbuwa a ransa, alamomin da za ta yi tsammani su ne:

  • Zai tsaya a mike sosai, tsaiwar da za ta bayyana iyakar tsayinsa.
  • Zai buda ko turo kirjinsa gaba (kadan) ya kuma janye ko dame ko dakale cikinsa.
  • Ya yi murmushi ko ma kar ya yi, amma yayin da zai kalle ki za ki taras idanunsa suna budewa sosai.
  • A hannu guda kuma, yayin da kike tare da namiji amma kika lura cewa babu ko daya daga cikin wadannan alamu, kuma jikinsa ya yi la’asar, wato yana bayyana alamomin shi mai rauni, kamar ke, to kar ma ki raba daya biyu, ba ya son ki!

  Kuna iya karanta wannan makala da ta yi sharhi mai zurfi akan alamomi 8 da mace zata gane namiji da gaske yake son ta.

  Idan mace tana son ka

  Daga tsaiwar da mace ta yi a gabanka, idan zumudi bai yi gaba da tunaninka ba, za ka iya fahimtar cewa lallai tana son ka. Haka nan ma idan akasin hakan ne a ranta, za ka iya ankarewa.

  Ture maganar murmushin da ka ga tana yi. Sassa da dama a jikin mace suna bayar da labarin cewa yanzu tana tare da wanda take so, ko da ta sani ko ba ta sani ba. Daga cikin alamomin da ake tsammanin mace za ta nuna yayin da ta tsaya a gaban wanda take so, ko ya burge ta:

  Taba kai. A mafi yawan lokaci, ko daga nesa ta hango ka, idan ka lura sosai za ka ga zai yi wuya ta karaso inda kake ba tare da ta dan taba kanta ba. Za ka ga ko dai ta taba kan da zummar gyaran gyale ko hijabinta, ko kuma da nufin wata ‘yar shafawa mai kama da susa.

  Wannan taba kai yana isar da sakonnin ba tare da ita kanta ta sani ba. Yayin da hannunta ya daga sama, idan a can bangaren Turawa ne da sauran kasashe masu wayewar kai irin ta Turawan, kamar kasashen da Faransawa suka raina, wadanda ba su cika rufe jiki kamar yadda muke yi a nan arewacin Najeriya ba, za ta karas yayin da ta daga hannun, wasu sassa na can karshen hannunta suna bayyana. Wani lokacin ma har zuwa hammatarta. Kuma wannan sahen yana daya daga sassa masu daukar hankalin namiji, tare da cewa da yawa daga mazan ma in da za ka tambaye su abubuwan da suke daukar hankalinsu sam ba sa ko tuno wannan. Hakan yana nufin shi ma nan take za ta fara kayatar da shi, kamar yadda ya kayatar da ita.

  Za ta karkata kanta. Mawuyacin abu ne ka ga mace ta tsayar da kanta a tsaye car, kamar yadda namiji yake yi, yayin da yake gaban wanda yake so.

  Kodayake, karkata kan yana zuwa ne a nau’uka mabambanta. Amma duk ma yadda za ta yi shi, yana dauke da sakonni da dama. Wadanda za mu ambaci biyu kacal daga ciki a wannan darasin:

  Watakila ta karkata kan gefen hagu ko damanta, ya kusanci dayan kafadunta, wanda yawanci hakan ya fi alamta rashin kuzari ko rauni da shagwaba da dangoginsu. Ko kuma ta sunkuyar da kan, ta kalli kasa, wanda shi kuma ya fi alamta kawaici da kunya.

  Ala ayyi halin dai, duk wanda ta yi daga ciki, yana iya bayyana rauninta. Cewa ita ba ta da karfin halin dadewa tana kallonka, kamar yadda kai ka daure ka iya kura mata ido. Hakan sai ya sa ta sunkuyar da kanta. Haka nan, ko da dai yayin da ta karkata kan gefe tana iya kallonka, to a lokaci guda kuma hakan yana mayar da ita wata ‘yar karama kuma rarrauna, kalar tausayi.

  Wani muhimmin sako da karkata kai ya kunsa shi ne, yarda. Wato shi wuya yana daya daga cikin manyan muhallai masu hadari, wadanda mutum yake matukar taka-tsantsan da su. Kullum rufe su ake yi. Ba a bayyana su. Yayin da duk ka ga an bar wuya ya bayyana, yadda ba zai yi wuyar a dake shi ko a sare shi ba, to a gaban wani mutum ne da aka amince da shi. Don haka, duk ma dai inda mace ta karkata kanta ta bayyana maka wuyanta, to alama ce ta ta aminta da kai.

  Amma yayin da ka ga mace ta yi tsaye kyan-kyan a gabanka, kamar wata soja, babu  alamar rauni ko ta kunya, to ka zunguri keyar takalminka kawai, ka kara gaba.

  Karanta wannan makala da na yi cikakken bayani game da yadda mata ke soyayya.

  Ankare da kafarta

  Wata muhimmiyar alama da ya kamata maza, musamman ‘yan samari masu tare ‘yanmata a kan hanya su rika lura da ita, ita ce sakon kafa. Yanayin da kafafuwan wadda suke tsaye da ita sukan kasance. Dayake ita kafa ta yi nesa kwarai da kwakwalwa, mawuyacin abu ne ta tsaya sai abin da kwakwalwar ta shirya, ya zama shi za ta gabatar sak. A mafi yawan lokaci, takan aiwatar da abubuwan da yake cikin zuciyar mutum ne kai tsaye. Don haka ita idan har zuciyar mutum ba ta son wani yanayi, ba ruwanta da tsayawa sai kwakwalwa ta gama shirya yadda za a yi kara ko karya (pretending), kamar yadda fuska takan yi, wadda ko ba ta jin dadin magana da mutum, takan iya kirkirar musmushi na jabu, ta nuna kamar so take yi. Sabaninta, kafa kawai za ta bayyana ainihin labarin da ke cikin zuciyar ne.

  A yayin da ka tsaya da mace kuna magana, daga mafiya girman abubuwan da zaka lura da su, ka yi saurin fahimtar tana jin dadin tsayawa da kai din ko ba ta so, akwai kafarta. Kawai ka dubi ina kafar ta fuskanta. Idan har tana so ko tana jin dadin wannan tsayuwar da tattaunawar da kuke yi, za ka taras kafarta kai take fuskanta, kai tsaye. Haka kuma idan har ba ta jin dadin tsyuwar, zaka taras kafar ta baude ta nufi wani wuri daban. Kai idan ma so kake ka yi mata fahimta ta kwakwaf, ka lura da inda kafar ta kalla, kai tsaye kana yin sallama da ita, to wurin za ta nufa.

  Ku dai bi mu a sannu don fahimtar abubuwan da jikkunanmu suke bayyanawa, ba kuma tare da mun sani ba, a lokutan soyayya da sha’awa.

  Kuna iya karanta wannan makalar da ta yi bayani akan yadda ake sauraren mace.

Comments

1 comment