Rubutu

Blogs » Zamantakewa » Yadda maza da mata ke fahimtar juna a zamantakewar soyayya

Yadda maza da mata ke fahimtar juna a zamantakewar soyayya

 • A kowace shekara miliyoyin mutane ne suke kamuwa da son juna. A kowace shekara kuma miliyoyin aure ake daurawa. Amma abin takaici kuma a kowace shekarar dai miliyoyin auren ne suke watsewa! Saboda wancan son da suke yi wa juna a baya, yanzu ya gushe! Daga cikin wadanda suka tsaya suka ci gaba da zaman auren kuma, wani kaso mai tsoka suna yin zaman a dosane ne. Wato dai irin zaman da fargabar halin da za a shiga bayan rabuwa ne kawai ya sa ake ci gaba da tattalinsa. Ko kuma irin zama nan da ake yi don masalahar ‘ya’ya.  

  Wani kaso kuma wanda watakila shi ne mafi karanci, shi ne na mutanen da suke zaune cikin wancan yanayi na tsohuwar soyayyarsu tun irin ta farko, ko kuma ma wadda ta fi ta farkon. Wannan kuma yana faruwa ne yayin da mata da mijin suka fahimci bambamce-bambamcen da ke tsakaninsu, kuma suke yin la’akari da su a zamantakewarsu da juna.

  Don haka dolenka ne a matsayinka na mai aure ko a matsayinki na mai aure ku san cewa akwai bambanci kuma ku yi la’akari da bambancin da ke tsakaninku yayin da kuke gudanar da mu’amulolin zamantakewarku. Idan dai har da gaske ne kana so ka yi tsaftataccen zaman aure. kuma ku samu damar ba wa yaranku tsaftatacciyar tarbiyya. Domin idan har ku a karan-kanku (mata da miji) ba ku kyautata zamantakewarku kun tsaftace ta ba, to ba fa yadda za a yi kuma a sami wata tarbiyyar yara. Abubuwan da suka kamata mu sani game da bambance-bambancenmu suna da dama.

  Da farko dai kamar yadda dukkanmu muka sani; halittar maza da ta mata ta sha bamban, tun daga asali. Muna sane da hadisin nan da ke cewa: An halicci mace ne daga kashin hakarkari, wanda yake a tankwashe. Kuma an ba wa mazan tabbacin cewa ba su isa su mikar da su ba. Kuma aka yi musu umarnin tausasa musu a hakan. Wani muhimmin abin lura a nan shi ne: Yadda fa maza kan ganin matan a baude, haka su ma matan ke ganin  mazan ne a baude. Shi ya sa za ka ji kowa na ganin baike tare da zargin kowa. Sai ka ji mazan na cewa: ''Ka san su mata ba hankali gare su ba.'' Matan kuma na cewa: ''Kin san namiji dan kunama ne.''  Da makamantan wadannan zantuka marasa dadin ji.

  Wannan yana kara nuna mana ragontakar mazan da mata, bisa yadda suka yi saurin manta bambancin da ke tsakaninsu. Hakika da dai ba su mance ba, babu abin da zai sa daya ya rika yawan zargin dayan kamar yadda muka wayi gari a yau.

  Watakila da maimakon yawan zargi da jifa da bakaken maganganu da kushe da ake wa juna, sai ka ga tausayin juna ne zai shiga tsakani. Domin a lokacin da mutum ya yi ma wani abu da kake ganin ba haka ya kamata ya yi ba, idan kuma ka kara duban yanayin halittarsa ka fuskanci ai gwargwadon abin da zai iya yi kenan, to za ka ji maimakon jin haushi sai dai ka ji tausayinsa.

  Misali, idan kana da yara uku kana tafiya da su a kan hanya, sai kuka zo wurin wata karamar kwata. Kai kuma don kana ganin karama ce sai kawai ka wuce gaba, kana jira su tsallako ku tafi. Amma da ka waiwaya sai ka ga biyu daga cikin yaran sun tsallako, amma dayan ya tsaya yana kallon ku kamar zai yi kuka. Watakila ma kuma shi ne babba a cikin yaran. Nan take sai ka harzuka, ranka ya vaci, ka himmamtu don yi masa fada ko zagin sa, bisa tolonci ko rashin kokarinsa da kake gani. Amma yayin da ka bude baki don zagin sa, ko ka daga hannu don dukan sa, sai kuma ka tuna cewa, ai gurgu ne! Na tabbata nan take kuma za ka ji tausayin sa ya kama ka. Domin ka tabbata larura ce gare shi, wadda shi ma da a son ransa ne ba haka zai yi ba. Hasali ma dai a ransa ya fi ka son ya ga ya tsallake kwatar kamar yadda sauran ‘yan’uwansa suka tsallake. Ko kuma dai ya fi so bayan ma ya tsallake ya kuma tsallakar da wanda ya ga ba zai iya ba daga cikin kannen nasa. Na tabbata komai rashin hakurinka sai ka yi wa wannan yaron uzuri, kuma sai ka tausaya masa.

  To kamar haka ne kuma, idan muka fahimci banbancin da ke tsakaninmu da abokan zamanmu za mu iya yi musu uzuri, a wurare da dama. Wadanda watakila ba don samun ilimin fahimtar hakan ba, ba za mu yi ba.

  Dole ne mu yarda cewa:  Kasancewar mu a hakan, kowane jinsi yana ganin dayan a bauÉ—e, ba fa laifin kowa ba ne daga cikinmu. Hikima ce kawai ta Allah, (SWT) da Ya so Ya yi mu a haka, kuma Ya tsara mu zama abokan zaman juna. Don Ya jarraba mu ya ga wadanda za su yi juriyar bin umarninsa cikin wannan rayuwa mai cike da sarkakiya. Kamar yadda Yake cewa: ''Li yabluwa kum, ayyukum ahsanu amalan.'' (Malik)

  Ku karanta: Yanayin da jikinmu kan kasance yayin soyayya

  Sarkakiya

  Daya daga manyan korafin da mata suka fi yi game da maza shi ne, maza ba sa saurarensu. Wato ba sa ba su isasshen lokaci yadda suke so yayin da suka tashi bayyana abin da yake damun su. Wai da zarar sun fara magana sai mazan su katse su. Abin da kuwa yake faruwa shi ne, yayin da mace ta fara magana game da wata matsalarta, sai mijin ya yi sauri kafin ta kai inda take son tsayawa ya katse ta ta hanyar ba ta shawarar da yake tsammanin za ta zama warakar matsalar. Yakan cika da mamaki shi ma kuma yadda matar take nuna rashin gamsuwa da yadda ya tunkari maganar tata, amma abin da shi bai sani ba shi ne, ita fa ba wai shawara ko mafita take bukata a wannan lokacin ba. Abin da kawai ta fi bukata shi ne a tattauna game da matsalar. Domin tattaunawa sosai game da matsalar, ko ba ta isasshen lokaci a saurare ta ta zayyana dukkan damuwarta, tamkar  yana tabbatar mata ne cewa an damu da damuwa ko matsalar da take ciki. Wanda ita a wurinta hakan wata babbar hanya ce ta magance radadin abin da ya dame tan.

  Daya daga manyan korafin kuma da maza sukan yi game da matansu shi ne, suna son canza su. Wato suna nuna kamar suna son tursasa su dole sai sun canza wata dabi’a ko halayya tasu. Abin da kuwa yake faruwa a nan shi ne: Ita mace idan har tana son mutum to a kullum burinta ta taimake shi. Ba ta da wani abu da kullum take kallo a matsayin abin da take son ba wa gudunmawa kamar shi. Shi ya sa za ka taras tana kokarin yin kaka-gida a cikin dukkan  al’amuransa.  Duk kuma irin togewar da zai yi wurin kaucewa ko watsi da shawarwarinta ba za ta gaji ba. Za ta ci gaba da ba shi shawarwarin da tsammanin wataran za tai nasara ya karba. Domin ta yarda har cikin zuciyarta cewa wannan mutumin fa babu wani mai muhimmanci a rayuwarta tamkar sa. Kuma nasararsa nasararta ce, haka nan kuma akasin nasaras dukkansu zai shafa. Tamkar dai shi jagora ne na wani kamfani ko masana’anta da suka bude ko assasa tare, wadda idan ta yi fushi ta kau da kai ana yin ba daidai ba a masana’antar daga baya aka zo aka samu matsala, to dukkansu ne za su yi asara. Don haka babu abin da zai sa ta gaji da kawo shawarwari da hanyoyin da take ganin idan an bi su za a samu nasara da riba gwaggwaba a wanan masana’anta.

  Sai dai abin da mata ba su sani ba shi ne, shi namiji yana kallon wannan alakar ne ta wata mahnaga daban, sabanin tata. A wurinsa, idan har bai samu cikkakiyar damar sarrafa akalar gidansa a matsayin shugaba mai cikakken iko ba, to ba zai taba jin sa a matsayin cikakken magidanci ba. Don haka ba zai taba yuwuwa ya zama yana tafiyar da rayuwa ko akalar gidansa a bisa doron tsare-tsarenta ba. Domin damka mata hakan, tamkar damka mata akalar gidan ne.  

  Don haka shi ma sai ya riqa tirjewa ya nuna abin da kawai yake so a gare ta, shi ne, ta karbe shi a yadda yake kawai. Wannan shi ne alamar ta yarda da kaifin hankali da hangen nesansa. 

  Domin gane me yasa wannan sabani kan faru tsakaninmu, wato me yasa kullum maza suka fi son samar da mafita maimakon doguwar tattaunawa game da matsala, da kuma abin da ya sa mata suka fi son ba wa mazan shawara cikin dukkan lamarinsu, kamata ya yi mu koma baya mu dubi ainihin halayyar kowannensu tun daga tushe. Wato mu bibiyi ainihin halayya da dabi’un kowane bangare (mata da mazan), sannan  daga bisani mu yi duba zuwa ga abubuwan da suke haddasa sabanin. Musamman sakamakon irin yadda wadancan dabi’u suka saba.

  Kuna iya karanta makamancin wannan makala da ta yi nazari akan banbancin dake tsakanin maza da mata a zamantakewa.

  Mu hadu a makala ta gaba, in sha Allahu.

Comments

0 comments