Rubutu

Blogs » Zamantakewa » Labarin zuciya: Yadda za ka gane murmushin gaske da na karya

Labarin zuciya: Yadda za ka gane murmushin gaske da na karya

 • Jijiyar da take fuskarka, wadda ita ce take sarrafa dukkan wani motsi ko yanayi da fuskarka take bayyanawa, kamar bishiya take. Ainihin tushen bishiyar yana cikin kwakwalwarka, yayin da rassa guda uku suka rankayo cikin fuska: Reshe na farko, shi yake aiki a bangaren hawaye da yawu da abubuwan da suka dangance su. Yayin da reshe na biyu yake aika dukkan wasu sakonni da suka danganci dandano. Shi kuma bangare na uku, shi ne sashen da yake ba wa mai kallon fuskarka damar karanta dukkan yanayin da zuciyarka take ciki. Wato dai, shi ne sashe mai sarrafa yanayin motsin fuskarka, ya bayyana murmushi ko murtuke fuska da dangoginsu.

  Fatu da tsokokin fuskar bil’adama suna da taushi da saukin juyawa ko motsawa kwarai. Wannan yake   ba su damar sauyawa cikin sauri, su bayyana ainishin sakon da yake cikin kwakwalwa. Shi ya sa ma mutane sukan iya isar da sako tsakaninsu ta hanyar bayyana yanayin fuskarsu ba tare da furta kalmomi ba.

  Kaddara cewa, kana zaune a kusa da wani mutum da ya kayatar da kai. Misali, mace ce wacce ta burge ka, amma kana fargabar watakila sanar da ita zai iya zama takura a gare ta, ko ya sa ta ji ta rasa sukuni har ma ta ji zaman wurin ya gundire ta. Kawai yi kokari ka hada ido da ita, ka dan tsaya zuwa wasu ‘yan dakiku, sannan ka yi dan murmushi, ka basar. Ko kuma idan ke mace ce, ki sunkuyar da kanki, cikin wancan yanayi na murmushi. A nan, kai tsaye sako ya dira har can cikin zuciyar wanda aka aikawa, ba tare da furta ko da kalma guda ba!

  Haka nan, yayin da ka so aika wa mutum sakon cewa abin da yake yi ba daidai ba ne, ba ka bukatar sai ka bude baki ka furta wata kalma. Kawai kalle shi, ka hade girar sama da ta kasa (ka dan rage fadin idanunka), ka kuma hade lebbanka gam, sannan ka dan girgiza kai a hankali. Ya ishi wannan ishara cewa lallai ya saki layi, kuma daga nan ba ya bukatar sai ka ce masa ya bari ko ya gyara abin da yake yi.

  Labarin zuciya dai sanannen labari ne kuma bayyanann ne: Yi murmushi yayin da ka hangi bakonka ya doso gidanka gadan-gadan. Ko ka daure fuska yayin da kake karanta sakamakon jarrabawar danka. Ko ki fada wa surukarki cewa kin yi matukar fari cikin ganinta, alhali fuskarki tana yin kamanni da wadda ta tsotsi lemon tsami, ko wadda aka shekawa ruwan sanyi lokacin hunturu. Cikin kowanne daga wadannan muhallan, ko ka yi shiru, ko ma ka yi magana, tabbas ba maganganun ne za su yi tasiri ba domin fuskar ta gama bayar da labarin.

  Kuna iya karanta makala da ta yi Nazari bisa yanayi da jikinmu kan kasance yayin soyayya.

  Shimfidar fuska

  Yayin da duk kake magana da mutum, fuskarka ta kasance tana fuskantar sa kai tsaye; idanunka a bude (budewa ko dai iyakar girmansu da suka saba kasancewa yau da kullum, ko kuma ma su dan kara); bakinka ya kasance a sake (lebbanka ba su hada gam da juna ba); kanka ya dan karkata gefe kadan; kuma shi din kake ta kallo, to ko shakka babu wannan mutum daga wannan lokaci zai samu tabbacin lallai ya samu masauki.

  Mu’amulantar mutum da sakakkiyar fuska da daidaitacciyar murya,  kuma kalaman da suke fita daga bakinka suke tafiya daidai da yanayin fuskar, tamkar ba shi wata gagarumar kyauta ne. Wadda kuma idan ka dauke su, sai ka yi wa mutum wata katuwar kyautar amma ya gaza jin dadinta, sakamakon rashinsu da bai gani daga kan fuskar taka ba. Abu ne mai kyau matuka mu fahimci cewa, murya da yanayin fuskarmu suna bayar da bayani mafi muhimmanci a kan wadda kalamanmu suke bayarwa. Don haka daga cikin kwarewar da ake bukata mutum ya samu a cikin zamantakewarsa da abokin rayuwa, akwai lura da yadda ake tasarifinsu.

  Duk da dai ba mu cika damuwa da sautin muryarmu yayin da muke magana da wasu ba, amma sautin muryar nan yana da matukar muhimmanci a cikin kalamanmu da kuma tasiri wurin sawa a gamsu da gaskiyar abin da harshenka yake furtawa ko akasin sa. Idan kana so ka yi magana cikin sauti lafiyayye yayin da kake cikin wani yanayi, kawai ka ja numfashinka tun daga can cikin cikinka (tamkar mai yin dogon numfashi). Yayin da ka sauke numfashi, ka tashi furta magana, sai ka fara da ‘yar karamar gyaran murya.

  Lura da mai fuskar-shanu

  Kodayake, akwai wasu mutane wadanda halittarsu ce a haka, kawai za ka ga mutum kullum idanunsa kasa-kasa (ba ya bude su sosai). Bakinsa ya dan karkata gefe kadan. Habarsa kuma ta dan yo kasa. Duk lokacin da ka gan shi sai ka ga kamar a fusace yake.

  Irin wadannan mutanen sai ka dauka kamar mutane ne da ba su da dadin mu’amula, ko wadanda kullum suke cikin tsananin tunani ko dai mutane ne masu karancin farin ciki a rayuwa, ko da kuwa a lokacin da suke ba ka labarin nasara ko gagarumar ribar da suka samu a kasuwancinsu ne. 

  Idan mutum mai irin wannan halitta ko dabi’a yana labarta maka batun nasararsa, abin da zai iya tabbatar maka cewa da gaske ne lamarin ya faranta ransa, shi ne ka dube shi da kyau. Za ka taras kai yake kallo kai tsaye, kuma idanunsa sun dan bude fiye da yadda suka saba. Sannan ‘yar fata ko tsokar nan ta wajen idanun nasa ta dan tattare ta daga kadan.

  Murmushi ko yake?

  Wani abu da ba mu cika lura da shi ba game da dariya ko murmushi ba, shi ne ba baki ne kadai yake yin su ba. Aiki ne da yake tasowa tun daga goshin mutum har habarsa. Kodayake, mafiya muhimmancin wurare a yayin murmushi, su ne idanu da baki da kundukukki (tsokar gaban fuska da take geffen hanci). Lura da kyau, da za a nuna maka idanun mutane biyu (ba tare da sauran kasan fuskar ba) a tabbatar maka cewa daya daga cikinsu yana dariya ne, yayin da dayan ya bata rai, sannan a tambaye ka ka bayyana wanne ne me dariyar a ciki, zai yi wuya ba ka bayyana shi ba, tun daga kallon farko. Domin abu ne mai sauki rarrabewa tsakanin yanayin da idanuwan suke ciki. Sai dai ko idan rashin sa’a aka yi ka hadu da mutane irin su Bill Clinton, wadanda suka nakalci yadda ake yin jabun motsi.

  Karanta manya-manyan kura-kuarai da ma’aurata ke yi bas u sani ba.

  Murmusin gaske

  Dayake mutane sun kware wurin boye yanayin da suke ciki, don yaudara ko boye ainihin yanayinsu na hakika saboda wasu dalilai, akwai bukatar ka iya bambance tsakanin murmushi na hakika da dan jabu. Akwai abubuwa da dama da ya kamata ka lura da su, wadanda su ne ainihin dabi’un fuska yayin da take bayyana murmushi na gaske, wanda ya taso daga cikin zuciya, ba wanda kwakwalwa ta kirkira don wata manufa ba.

  Idan yanayin farin ciki daga cikin zuciyar mutum yake, babu bukatar sai ya kirkirar wa fuskarsa yadda za ta bayyana shi. Kai tsaye, ba kuma tare da shawara da shi ba, za ka ga idanunsa sun dan kankance, ‘yar tsokar da take kewaye da gefen idanun ta dan dago, kuma wannan ‘yar tsagar ta can kwanar idanun ta dan karkato kasa kadan. Kundukukansa biyun duk za su dago sama, su yi tudu fiye da lokacin da fuskarsa take a sake. Lebbensa biyu duk za su rabu da juna, su ja baya (gefe da gefe) kuma su dan daga sama kadan, dagawar da za ta iya ba wa hakoransa damar bayyana. Haka nan, daga can gefen bakinsa karshen tsagar lebban biyu, in ka lura za ka iya fahimtar tsagar ta karkata sama kadan. Yayin da duk ka samu gamayyar wadannan alamu a fuskar mutum, kar ma ka yi kokonton farin cikinsa.

  Jabun murmushi

  Ba kawai tabewar lebba ko dagawarsu da bayyanar hakora ne ke nuna cewa mutum murmushin gaske yake yi ba. Idan wani ya so ya bayyana maka cewa a cikin halin farin ciki yake kuma har ya yi yunkurin bayyana maka hakoransa don tabbatar da haka, akwai bukatar da lura da sauran sassan ko muhallan murmushi don tabbatar da ikirarin nasa.

  Idan lebbansa suka kasa samun daidaito da idanun – wato lebban suka matsa daga jikin juna, amma tsokar da ke kewaye da idanun ba ta yi ko gezau ba, balle idanun su dan ja ciki har tsagar ido da risina kasa. Haka kundukukan ko dai ba su daga ba, ko kuma dagawar ta kasance kadan din gaske. To kar ka karbi wannan a matsayin murmushi, yake ne kawai ko jabun murmushi da aka kirkira don wata manufa. Ka lura da kyau, yawanci mai jabun murmushi bai cika so a hada idanu da shi ba.

  Idan ka kasa gane tsakanin yanayin fuskar mutumin da yake murmushin gaske da wanda yake yin kirkirarren murmushi, ka je wurin masu daukar hoto. Za ka ga yadda fuskar mutum take yi yayin da aka ce masa “Yi murmushi.” Da kuma bayan sauke kyamarar in an ce da shi “Kai haka ake yin murmushi?”

  Mu hadu a takarda ta gaba.  Sannan kuna iya duba makalata da ta gabata akan yadda maza da mata ke fahimtar juna a zamantakewar soyayya.

Comments

0 comments