Rubutu

Blogs » Zamantakewa » Labarin zuciya 2: Sassa jiki dake bayyana murmushin gaske

Labarin zuciya 2: Sassa jiki dake bayyana murmushin gaske

 • Yadda za ka bambance tsakanin yanayin mutumin da yake cikin damuwa da wanke ke cikin bacin-rai.

  Idan ilimin da zai ba ka damar fahimtar maganar wanda ya ki yin magana da ta kurma kake so. kuma ya ba ka damar lissafa motsin wanda ya ki motsi, to kar ka gaji da bibiyar mu.

  A mukalar da ta gabata mun tattauna game da yadda mai karatu zai iya bambance tsakanin murmushin gaskiya da kirkirarren murmushi ko yaya yake. Kuma ina ganin akwai bayani mai muhimmanci da ya kamata a ce mun yi dauraya da shi kafin mu shiga fage na biyu. Wanda muke sa ran idan har Allah Ya sa mutum mai iya lura da yanayin mutane ne yadda ya kamata, to in ya hada bayanan biyu zai samu tabbacin abin da yake nema cikin sauki da yardar Allah.

  Maganar murmushi, magana ce da masana da ‘yan shaci-fadi suka dade suna kai ruwa rana game da ita. Wato dai, kamar yadda masu hira a layi ko a teburin mai shayi sukan yi musu da juna game da murmushi ko yaken mutum, haka ma masana suka dauki lokaci suna cewa wancan ne alamar murmushi na gaske, wancan kuwa na bogi ne.

  Mukan ga mutum yana dariya alhali mun tabbata an yi wani abu da ya sosa masa rai. A irin wannan lokaci sau da yawa mukan ce, “wannan daga gani yake ne.” Wato ba murmushi ne da yakan zo sakamakon samun farin ciki ko nishadi ba, kawai dai an kirkire shi ne don a danne ko boye ainishin labarin da yake cikin zuciya.

  Wadanne sassa ne ke bayyana murmushin gaske?

  A cikin shekarar 1862 wani Bafaranshe kuma masani a fannonin motsin jiki da na jijiyoyin dan’adam, mai suna Guillaume Duchenne de Boulogn ya samar da wani gagarumin aiki da kuma sahihin binciken kwakwaf dangane da ainihin tsokokin da suke bayyana murmushi na gaskiya. Bayan daukan lokaci yana gwaje-gwaje ya gano cewa fuskar dan’adam tana da rukunin tsokoki guda biyu, wadanda daya daga ciki yake sarrafa motsin da fuska take yi yayin murmushi na gaskiya. Yayin da rukuni na biyun kuma yake sarrafa sassan fuskar yayin murmushin bogi.

  Akwai rukunin tsoka na farko, wanda ya yi kwanciyar migirbi tun daga kan kumatun mutum har zuwa bakinsa, wadda  ake ce mata “zygomaticus major muscle”. Wannan rukuni ne da mutum yake da ikon sarrafa motsinsa duk lokacin da ya so. Kuma dayake tana makale ne gam da tsokokin da suka kewaye baki, a can sama kuma tana hade da tsokar kumatu. Tana iya tabewa ta ja sama, ta bayyana hakora kuma ta daga kundukukin mutum nan take. Don haka, a duk lokacin da muka so bayyana farin ciki ko kyakkyawan yanayi, alhali akasin hakan ne a cikin ranmu, wannan rukunin tsoka kawai za mu motsa, nan da nan sai ka ga waccan alama ta murmushi ta bayyana.

  Rukuni na biyu, shi ne tsokokin da suke kewaye idanun mutum, wadanda ake yi wa lakabi da “orbicularis oculi”. Wadannan tsokoki su ne suke iya janyuwa su haddasa tsukewar idanu, su fitar da ainihin waccan kankancewar idanu da kuma samar da ‘yar karkacewar kwanar nan ta gefen idanu, da muka bayyana a takardar da ta gabata. Wadanda sai motsin kundukuki da na baki sun hadu da nasu motsin ne ake iya samun ainihin cikakkun alamomin sahihin murmushi.  Wani abin sha’awa ga wannan rukuni na tsoka shi ne, su suna yin motsi dan karan kansu ne, ba mu da ikon sarrafa su kamar yadda muke da iko a kan rukuni na farko, wato dai suna irin aikin nan ne da masana suke cewa “involuntarily” a Turance.

  Masana da dama irin su Farfesa Paul Ekman na University of California, San Francisco da Dr Wallace V Friesen na University of Kentucky duk sun tafi ne a kan cewa, ainihin murmushi na gaske yana samuwa ne daga kwakwalwa. Wato yayin da mutum ya tsinci kansa a cikin yanayi na farin ciki, sai sashen kwakwalwa da yake da alaka da ji “feelings” ya motsa nan take. Wanda bayyanar hakan ita ke haddasa irin murmushin da tsokar baki za ta motsa, tsokar kundukuki ta daga, ta idanu ta ja, yadda idanun za su dan tsuke, gira ta dan yi kasa.

  Idan har ka rasa wannan gamayyar motsin sassa yayin da kake kallon mai murmushi, to kar kyan fuskarsa ko girmansa a ranka ya rude ka. Wannan ba murmushi yake yi ba.

  Fuskar da take cikin bakin ciki

  Idan cikin sauri kake son fahimtar yadda fuskar mutumin da yake cikin damuwa ko bakin ciki take, kawai duba ‘yan hotunan aljanun nan da suke wayarka, “emojis”.  Za ka taras yayin da mutum ya tashi nuna maka cewa yana cikin damuwa, sai kawai ya jefo maka irin wannan hoton wanda karshen bakinsa ya karkata kasa. Koma ka kara kallon hotunan da kyau, za ka fahimci cewa, wanda yake murmushi can karshen bakinsa yakan daga sama ne.  Yayin da karshen na mai bakin cikin kan yi kasa.

  Dubi fuskar mutumin da yake cikin halin damuwa da kyau, za ka taras fuskarsa duk ta saki (kamar yadda jikin mutum yakan saki yayin da alamun tsufa suka fara shirin cim masa). Idanunsa sukan dan rage haske, wato ba sa iya yin kar-kar kamar yadda yakan kasance yayin da yake cikin kyakkyawan yanayi. Sannan tsakar karshen bakinsa za ta karkato kasa. Da zarar ka taras da mutum a cikin irin wannan yanayi, to idan har da wani abu da za ka iya yi masa da zai rage masa radadi, yi sauri ka fara.

  Fuskar da take cikin fushi

  Dayake yanzu yawancin mutane a kofa-kofa suke, ma’ana kadan suke jira a tabo su, su yi wa mutum wankin-babban-bargo. Cin karo da mutumin da yake cikin yanayin fushi ba shi da wata wahala.  Duk da haka abu ne mai matukar amfani mu fahimci ko mu iya karanta yadda ainihin fuskar wanda yake cikin tsananin fushi yake. Ka ga watakila idan a wani lungun ne ka ga mutum ya doso ka cikin irin yanayin, sai kawai ka yi sauri ka kira lambar ‘yansanda masu kawo daukin gaggawa.

  Yayin da duk ka lura girar mutum ta yi kasa, idan ma mai irin rami ko kurmin idanu ne, sai ka ga  girar kamar za ta shige cikin kurmin idon. (Lura da irin wannan yanayin yana  daga cikin dalilin da ya sa idan Bahaushe zai ba ka labarin wanda ya bata rai, cikin takaitattun kalmomi, kawai sai ya ce da kai “Ya hada girar kasa da ta sama.” Yana nufin girar ta yo kasa har tana nema haduwa da gashin idanunsa.) To wannan kasan da girar takan yo yana daya daga cikin muhimman alamomin da za ka tsammaci gani daga wurin wanda yake cikin tunzuri ko bacin rai. Abu na biyu shi ne za ta ga fatar goshinsa ta dan yi wata ‘yar tattara. Wato yayin da girar ta yi kasa, ita kuma fatar goshin sai ta dan tattare ta bayar da wani dan layi wanda idan ka kalla za ka iya fahimtar cewa tabbas kafin bacin ransa ba shi da wannan tattarar. Sannan akan samu damewar lebban baki, da kuma waccan karkatar baki kasa da muka bayyana cewa mutumin da yake cikin yanayin damuwa yana yi. To haka shi ma bakin mai fushi kan karkata kasa. Hakora sukan hadu su hau kan juna, wato irin abin nan da Bahaushe kan ce an cije hakori.

  Sau da dama wasu mutanen ma idan suka tunzura, ko ransu ya kai matukar baci. Kofofin hancinsu kan kara budewa fiye da lokacin da suke zaman lafiya. Harwayau, fuskar takan sauyawa ta yi fari (fari irin na dashewa), sakamakon saurin janyewar jini daga jijiyoyin da ke kan fuskar.

  Kodayake, a tsakaninmu bakar fata, idan mutum ba fari sosai ba ne bambance irin wannan sauyawar fukar yana da matukar wahala. Amma hakika lura da sauyawar launin fuska abu ne mai matukar muhimmanci.   

  Sauyawar launin fuska

  A ganin wani Ba’ingile masanin halayyar dabbobi, Desmond Moris, sauyawar launin fuska tamkar wani ma’auni ne na fahimtar irin sauki ko tsananin tunzuri ko bacin ran da mutum yake ciki. Idan mutum mai haske ne (fari), fuskarsa takan iya sauyawa iri biyu. Ko dai ta dashe ko ta yi ja. Moris yana ganin mutumin da ya tunkaro ka da dasasshiyar fuska (wadda ta kode ko ta yi fari-fari), ya fi hatsari a kan wanda ya nufo ka da jar fuska.

  Domin yayin da ka ga fuskar mutum ta yi ja, to ya kai matuka wurin tunzura. Don haka ya ma wuce matakin kai farmaki. Sau da dama abin da kawai wannan zai yi ba ya wuce surutu, ko ma tsananin bakin cikin ya hana shi ko da yin magana. Amma wanda ya nufo ka da wannan kodaddiyar fuskar, yana kan ganiyar tunzurin ne. Don haka yana zuwa inda kake zai iya hada maka naushi.

  Idan kare ya taba cizon ka, ka lura da kyau, watakila za ka iya tunawa, wanda ya fi damunka da haushi da ban, wanda kuma ya duma maka fikar daban.

  Mu kara tarawa a takara ta gaba. 

Comments

0 comments