Rubutu

Blogs » Zamantakewa » Dabarun mallakar mace, kashi na biyu

Dabarun mallakar mace, kashi na biyu

 • Idan akwai wani nau’in karatu da ya kamata magidanci ya wajabtawa kansa, bayan koyon ilimin addini da na neman abinci, to watakila ba zai wuce ilimin da zai ba shi damar zama da iyalinsa cikin lumana ba. Domin a rayuwar mutum mai lafiyayyen tunani, nutsuwa tana samuwa ne daga gida. Wato yayin da ya samu kyakkyawar fahimta da cikakken hadin-kai daga iyalinsa, yayin ne yakan samu cikakkiyar nutsuwar da za ta ba shi kuzarin samun nasara a harkokinsa.

  Wannan shi ne darasi na biyu da muka fara cikin jerin dabarun masana da aka zayyana don mallake zuciyar mace, a bisa mahanga ta babban malami Dr. John Gray. A baya, cikin darasi na daya, mun kawo kusan kashi daya bisa hudun dabarun. Domin mun kawo daga dabara ta daya har zuwa ta ashirn da uku, daga cikin guda dari da daya. Don haka a yau ba tare da tsawaita magana ba, za mu tsallaka zuwa na 24 har mu kai ta 57, da yardar Allah:

  24. Ka ba ta kulawa fiye da yaranku. Yadda har yaran za su fahimci cewa magana ko bukatarta kake fara saurara kafin tasu. Ka sani, babu wani mutum da matarka take so ka ba wa kulawa ko kima fiye da ita, ko da kuwa dan da ta haifa ne.

  25. Ka rika sayo mata kananan kyaututtuka lokaci-lokaci. Kamar wata alewa da ka fahimci tana matukar so, ko turare da makamantansu.

  26. Wataran ka yi muku kaya iri daya, ku yi fita ta musamman da su. Ba wai don ana wani sha’ani ko biki na al’ada ba.

  27. Ka dauki hotunanta a wurare na musamman da ka yi tunanin za ta yi kyau, yayin da kuka fita da ita.

  28. Ka bari ta fahimci hotonta ne a kan wayarka. Kuma ka rika sauya shi lokaci zuwa lokaci. Ganin hoton a kan wayar ya ishi tabbatar mata da cewa lallai babu wani mutum da ya kai ta muhimmanci a wurinka. Kuma kana alfahari da ita. Sannan sauya hoton lokaci zuwa lokaci ya ishi tabbatar mata cewa ba wai a lokaci daya ko a wani hoto daya ta yi maka kyau ba. Kana ganin kyanta a kusan kowane irin yanayi kuma a kowace irin shiga.

  29. Ka tabbata a kalla ka rumgume ta sau hudu a kowace rana. Misali, lokacin fitarka daga gida, lokacin dawowaka daga aiki da makamantansu.

  30. Ki kira ta daga wurin aikinka takanas, ka tambaye ta yaya take, ko yaya gida. Ko kuma ka ba ta labarin wani abu mai dadin ji da ya faru. Ko ma kawai ka ce mata “Ina son ki!”

  31. Ka ce mata “Ina son ki!” a kalla sau biyu a kowace rana.

  32. Wataran ka dauki gavarar gyara shimfida ko share daki da kanka.

  33. Idan ta wanke maka kaya, ka taya ta ko da shanya ne. kar ka bari sai ta yi komai da kanka.

  34. Ka lura da lokacin da kwandon shararku ya cika, ka ce mata “Yau dai da kaina zan je in zubar da sharar nan!” Kar ka raina aikin da za ka yi saboda ita, musamman wanda zai ba ta dariya.

  35. Idan ka yi wata doguwar tafiya zuwa kauyukan da babu sabis, ka yi kokari ka sanar da ita cewa za ka shiga lungun da dabu sabis, don haka za ta ji ka shiru. Haka nan, idan tafiyar ta kasance kasar waje ce, in ka je ka sanar da ita cewa ka sauka lafiya kuma ga lambar da za a iya samun ka. Kar ka manta, rashin sanin halin da kake ciki na mintuna, tashin hankali ne mai girma.

  36. Wataran ka nannade kafar wandonka ka wanke mata mota. Wanda ya gan ta ne kadai zai iya kardadon irin farin cikin da take ciki a lokacin.

  37. Ka wanke motarka, ka tsaftace ciki tare da sanya turaren kamshi mai dadi a ciki. kuma ka sanar da ita cewa ka yi hakan ne takanas don daukan ta zuwa yawo.

  38. Ka goyi bayanta in ana musu da ita. Idan kuma ba za ka iya goyon bayanta ba, ka hakura, kar ka shiga musun. Alabasshi daga baya ka sanar da ita idan an bar cikin mutanen cewa ba ita ce a kan gaskiya ba. In ba a kan gaskiyar take ba.

  39. Ka tabbata kana cikin tsafta, kuma ka rika yin amfani da turaren da take jin dadin kamshinsa, a lokacin da za ka kusance ta.

  40. Ka yi mata tausa, a wuya ko baya ko kafa, lokaci zuwa lokaci. Musamman a lokutan hira.

  41. Ka ba ta dama ta yi barci a jikinka, musamman a wani yanayi ko lokaci da ka tabbata tana cikin ‘yar damuwa. Domin lokaci ne da ta fi tsananin bukatar a nuna mata kulawa da gata.  

  42. Ka yi hakuri a lokacin da take yi maka bayanin abin da yake damun ta, ko ya vata mata rai. Kar ka rika kallon agogo ko tsaki da waige-waige a lokacin.

  43. Kar ka zama kai ne mai rike masarrafin na’urar kallo (remote control) yayin da kuke kallon talbijin da ita. Balle ya zama kai ne mai sauya tasha.

  44. Ka nuna mata kana son ta a cikin mutane. Ta hanyar aikata ko furta wani abu da idan ka yi ko ka furta wanda duk ya ji ko ya gani zai yarda cewa lallai tana da kima ko girman daraja a wurinka.

  45. Ka yi kokari ka fahimci nau’in lemon ko alawar da ta fi son sha. Ta yadda idan ka tashi sayowa, ko ba ta zavi a cikin lemon ko alawar da za ka sayo mata, sai ka jero mata wadanda ka san tabbas tana son su. Haka nan yayin da b aka samu uzurin tambayar ta ba ma, ba ka da fargabar za ta so abin da ka kawo mata.

  46. Ka rike mata hannu yayin da kuke tafiya. Daya ne daga cikin abubuwan da suke sawa ta ji cikar ta macen da ake so.

  47. Yayin da ka yi niyyar fita da ita zuwa wani wurin cin abinci. Ka tabbata ka tanadi wuaren da suka cancanta da irin fitar. Kar ka bar ta da sake-saken ina ya kamata ku je. Kasaancewarka jagora, kai ne ka fi dacewa da ka samo hanya a yayin da duk bukatar tafiya ta tashi.

  48. Ka lura da wasannin da ta fi so. Wataran ka dauke ta takanas don zuwa kallon irin wannan wasan a fili. Maimakon a talbijin.

  49. Ka samar da wani yanayi ko shagali wanda zai ba wa dukkanku damar cava kwalliya ku fita tare.

  50. Ka zama mai hakui, kuma mai fahimtar yanayin mace, yayin da ta ce maka za ta sauya kayan da suke jiinta, alhali kun gama shiri za ku fita tare.

  51. Ka nuna ka fi mayar da hankali a kan ta, fiye da sauran mutanen da kuke gaisawa a hanya, in kuna tafiya. Maza da yawa ba su san yadda mata suka yi matukar damuwa da sakacin kulawar da ake ba su yayin da ake kula mutanen da ake gaisawa da su a kan hanya ba.

  52. Ka dauki dan gajeren hutu, musamman don nuna soyayya. Misali, ka nemi hutu a wurin aiki takanas, ko da na kwana daya ne. Ka sanar da ita cewa yau za ka ki zuwa wurin aiki, za ka zauna kawai ka wuni a gida don soyayya.

  53. Yayin da duk wata tafiya ta kama ku, ko kuka fita wani wuri don yawon shakatawa ko bude ido, ka yi kokari ka samar mata da wani abin sha ko (da) abinci wadanda ba su ta saba ci ko sha ba, a lokacin da take gida. Domin da abin da mutum ya ci da wanda ya sha duk suna iya saurin tuna masa cewa lallai fa ba a gida yake ba. Don haka ko ba wata tafiya mai nisa kuka yi daga gida ba, abin da ta ci ko ta sha sun isa su tabbatar mata cewa lallai ba a gida take ba. Amma fa ka yi hankali, idan mai sakakken ciki ce, kar ka ba ta abin da zai sa ta tsure!

  54. Ka yi wani rubutu ko zane (drawing) na musamman, a lokutan da wani abu da ya shafi rayuwarta ya zo. Kamar ranakun da take tuna ranar haihuwarta, ko zagayowar ranar daurin aurenku. Rubutun ko zanen ya kunshi wasu kalmomi ko alamu da suke tabbatar da yadda kake son ta, da (ko) alfahari da ita.

  55 Ka yarda ka tuka mota da kanka yayin wata doguwar tafiya, ko da kuwa kana da dire ba. da ita a gaban mota.

  56. ka yi tuki a hankali, ba tare da ganganci ba. irin tukin da ba za ku kasa samun damar yin hira cikin nutsuwa ba. Kar ka manta tana kusa da kai a zaune.

  57. Ka rika lura da yanayin da take ciki, ka kuma rika yin magana a kansa daga lokaci zuwa lokaci. Kamar “Yau dai da alama kina cikin farin ciki!” ko “Ga dukkan alamu kin gaji.” Ko tambaya, kamar “Ya ya dai, ko akwai wata damuwa ne?”

Comments

4 comments