Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku Taho Tare

Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku Taho Tare

 • Ku latsa nan don karanta labarin Banza Ta Kori Wofi.

  Wata rana wani Bahaushe wai shi Wawa za shi fatauci, sai ya bi ta kasar Yarbawa, Wawa ba ya jin Yarbanci, mutanen da ya tarar a wannan gari su kuma ba su jin Hausa. Amma duk da wannan Wawa bai lura ba. Yana cikin tafiya, ya kawo kofar gari, sai ya ga wani katon garken shanu fari fat suna kiwo. Wawa ya yi mamakin wanda ke da wadannan shanu masu yawa haka, sai ya tambayi wani mutum nan kofa ya gaya masa ko shanun wane ne wadannan.

  Mutumin ya amsa da Yarbanci, ya ce, “Ni ban ji ba.”

  Wawa da ya ji haka tsammani ya ke “Ni ban ji ba” shi ne mutumin da ke da shanun. Don haka ya ce, “Ni-ban-ji=ba lalle yana da sukuni.” Ya wuce ya shiga gari, sai ya kai ga wani babban gida. Ya daga kai, ya ga lalle gidan nan ya amsa sunansa, samari, wa ke da wannan babban gida haka?”

  Yaron ba ya jin Hausa, shi kuma sai ya ce a cikin harshensa “Ni ban ji ba.”

  Da Wawa ya ji haka, sai ya ce, “Kai, ba shakka Ni-ban-ji-ba ba wanda ya fi shi sule garin nan. Wannan irin gida sai ka ce na Sarki. Da ganin wannan ai ko ba a gaya maka ba ka san wurin nan sule ya zauna da gindinsa.” Ya haura takalmansa ya wuce faram, faram, faram, faram, har bakin kogin garin. Yana zuwa sai ya tarad da wani jirgi ya zo, ana ta fid da kaya daga cikinsa. Wawa ya dubi kaya, ya ce, “Oi! Wannanjirgi ya yiwo kaya!” Ya dubi wani nan kusa gare shi, ya ce, “Dan’uwa, duk ko kayan nan na mutum guda ne?”

  Shi bayarabe bai ji abin da ya ce ba, sai ya dube shi, ya ce, “Ni ban ji ba.”

  Da Wawa ya ji haka sai ya rike baki, ya ce, “masu gari! Hakika Ni-ban-ji-ba ya huce haushinsa. Ina ma Allah zai sa in gamu da wannan mutum, ko wajen adonsa ma in more ma idona!” Sai ya zauna ya huta, ya debi ruwa ya sha, ya kama hanya zai wuce. Ya kai kofar gari ke nan, sai ya ga wani mattacce an dauko shi, za a kai shi a rufe, wadansu na ta kuka. Wawa ya tsaya yana dubansu. Tausai ya kama shi, ya matsa wajen wata tsohuwa, ya ce mata, “Wane ne wannan ya riga mu gidan gaskiya?”

  Tsohuwa ba ta ji Hausa ba, sai ta dube shi, ta ce, “Ni ban ji ba.”

  Wawa da ya ji haka sai ya daffe kai, ya ce, “Allah mai girma! Ka san kowa samun nan na duniya ya ruda, ya shiga uku. Don Allah dubi abin da Ni-ban-ji-ba ya tara. Ga shi yanzu ya zama sai labari, kamar dadai duniya ba a halicce shi ba! Cikin duk abin nan da ya tara, dubi dan kyallen da za a kai shi da shi. Tun da ya ke al’amarin nan haka ya ke, to, ni yanzu me ya ruda ni har da na rabo da gida don rashin wadar zuci? Ga shi Allah bai hana mini abin da zan ci ba. Watau ba dai abin da ya fid da ni gida sai in sami abin alfahari in kara sabo. Mhm, Allah ya kiyashe mu da aikin Shaidan! Na gode Allah da ya kawo ni nan na sami gargadi daga al’amarin Ni-ban-ji-ba. Ba sauran abin da ya fi, sai in koma garimmu, in dangana da abin da Allah ke ba ni wajen ‘yar gonata.

  Da ma an ce, “Gani ga wani ya isa tsoron Allah.”

  Musa ya tashi, har ya bude zauren farko, sai ya ji bayi sun farka. Sai ya kuta, ya koma.

  Da Waziri ya ga kwana biyu sun wuce, kowace safiya bayin nan da ya sa suka dawo sai su ce ba wanda ya ko leko zauren, har abin ya dame shi, ya ce, “A’a! Da ko na yi tsammanin zai fito, dabara.” Ya kira wata tsohuwar baisarsa, ya bayyana mata abin da ya ke so duka game da Musa, ya ce mata in ta yi kokarin ta taimake shi har ta sa Musa ya fita waje, zai ba ta fam goma, ya kuma ‘yanta ta. Ya kawo sule goma, ya fara ba ta ta lasa.

  Tsohuwa ta ce, “Ta kwana gidan Sauki.” Magariba na yi, sai ta shiga gidan Sarki da kayan talla, ta kaikaici idon mutane ta yahuto Musa waje guda, ta ce, “Mahmudu ya aiko ni, ya ce a gaya maka wai kai haka za ka yarda ka lalace cikin matia? Ya ce a gaya maka fa duniya ba ta auren raggo.”

  Musa ya matsa kusa da tsohuwa, ya ce, “Don Allah iya, yana can yana ta yaki ko?”

  Tsohuwa ta ce, “Habe! Yanzu sanisanimmu akwai wanda a ke magana irin Mahmundu? Ni ma fa can na ke sansani, mu ke yi musu abinci. Mahmudu ya shaku da ni, ya aiko ni gare ka.”

  Musa ya ce, “Koma maza ki gaya masa, gobe in Allah ya so ya gan ni.” Tsohuwa ta koma.

  Da dare ya yi, Musa ya saurara ya ji barci ya kwashe bayin nan, sai ya shigo damaru, ya zo wurin aku, ya ce, “Ka ji Mahmudu na can sansani yana ta abin kirki, ni za sa in lalace nan cikin mata.”

  Aku ya ce, “Yallabai, ina ruwana? Ni ban hana ka ba. Yaya barde kamarka zai ce za shi wurin yaki a hana shi? Tun da ya ke niyyarka ka yi abin da zai faranta wa tsohonka rai ne, ai kowane hadari ka shiga Allah ya fisshe ka, yadda ya fid da Auta dan Sarkin noma daga namun jeji.”

  Musa ya ce, “Wane rigima ta kai shi ga fadawa hannun namun jeji?” Aku ya karba: 

  Ku latsa nan don karanta labarin Auta Dan Sarkin Noma Da Naman Jeji.

Comments

0 comments