Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MIJINKI Mijina Ne

MIJINKI Mijina Ne

 • *Masarautar Failura*
  _____Masarautar Failura babban Masarauta ce awani gari ayankin arewacin Nigeria, Masarauta ce mai babban tarihi wanda a qalla sarakuna goma ne sukayi mulkin masarautar har izuwa sarki na yanzu wato Sarki Abdulgafar d'an Yazid, wanda yake adalin Sarki, Masarautar Failura tatara Abubuwan tarihi, sanan gata da al'adu, iri daban-daban, Masarauta ce maitafiya da zamani, yaude cikin Masarautar nafad'a domin kawomuku rahoton abunda ke tafiya acikin Masarautar.
  Tafiya takeyi cikin takun qasaita tamkar hawainiya, wanda taci ado da wata jar atamfa Super Holland, wuyanta da kunenta da hannayenta sanye suke da gwala gwalai, fuskarta kuwa sai sheqi takeyi sbd kyau, jar alkyabba ta d'aura asaman kayanta wanda taji aikin surfani da Farin zare, bayi da kuyangine zagaye da ita, wasu agabanta wasu kuma a bayanta, jakadiya kuma tana gefanta tana mata kirari kamar haka.
  "Taka lafiya Gimbiya 'yar Sarki jikar Sarki tata'ba kunen sarki, matar Sarki, uwar sarki, kakar Sarki, saide har yanzu bakiga yarima maijiran gadon da yadace da keba, ko kuma shi kansa sarkin, ina kuke maza ku baiyana kanku domin Gimbiya TAFISU mai takalmin qarfe taga wanda yadace da ita, domin ita saide taza'ba bade aza'beta ba gaba sallamun baya sallamun 'yar Sarki mai takalmin zinare.
  Itako Gimbiya TAFISU sai wani jiji da kai takeyi, tana shashaqar iskar Masarautar ahaka suka nufi shashin Memartaba Sarkin Failura.
  suna nufan shashin fadawa da suke gadin shashin nan suka farayiwa Gimbiya TAFISU k'irari, su kuma bayi da kuyanginta, suka tsaya anan domin jiranta, jakadiya ce tatakewa Gimbiya TAFISU baya, har zuwa cikin parlour d'in Memartaba.
  Da Sallama abakinsu suka shiga parlour d'in wanda yagaji da had'uwa, Memartaba ne zaune acikin d'aya daka jerin kujerun da yake parlour d'in, kai tsaye Gimbiya TAFISU tanufi kujerar dake kusa da Memartaba, tazauna sanan ta duqar da kanta qasa, tace " gaisuwata a gareka Memartaba"
  Itako jakadiya zuwa tayi ta duqa agaban Memartaba sanan tace " barka da hutawa ranka yadad'e, ga Gimbiya TAFISU nan ta'amsa qiranka"
  Shiko Memartaba Abdulgafar hannu ya d'aga mata sanan yace " angaisheki jakadiya Adama"
  Tashi jakadiya tayi tajuya zata fita amma Memartaba yace " zaki iya jiranta anan jakadiya"
  Dan haka Jakadiya takoma can gefe tatsaya.
  Shiko Memartaba kallon Gimbiya TAFISU yayi, cikin muryarsa ta mutanen kirki yace " Maryama bansan sai yaushe zakiyi hankali ba, ki dubade kiga irin gaisuwar da jakadiya tayimin, amma ke maimakon kiyimin irinta, amma girman kai bazai barki ba, ki gyara halinki maryama ki zama mutumiyar kwarai kiduba fa kigani kece babba d'iya amasarautar nan kamata yayi sauran 'ya'yan cikin Masarauta suyi koyi dake, bawai aringa Allah wadarai da halinki ba".

  Itako Gimbiya TAFISU kallon Memartaba tayi tace " kayi haquri Memartaba amma ni nafison ka qirani da Gimbiya TAFISU, nafiji jin dad'in wanan sunan fiye da Maryaman da kake qira"
  Kallon ta Memartaba yayi yace " Allah ya shiryeki Gimbiya Maryama, qiran da namiki kema kinsan akan miye, nagaji da kallonki hakanan a cikin Masarautar nan, sbd haka ina fad'a miki da babbar murya nabaki lokaci qanqani kifitar da mijin aure, kafin raina yagama 'baci akanki tabbas idan kika bari hakan tafaru zanyenke duk hukuncin da naga dama"
  "Allah yahuci zuciyar ka Memartaba, amma ni har yanzu banga wani d'a namiji da yayi min ba, amatsayin mijin aure ba"

  "Ashe ke mutumiyar banzace bansani ba, to kijirayi hukuncin da zanyenke miki, shekarunki nawa kina zaune ba aure mulki haukane ko akanki akafara zama 'yar Sarki toni bashashashan sarki bane dole ne kifitar damiji koni nahad'aki dako waye kuma dole ki zauna domin kuwa yau kika cika shekaru 32 da haihuwa dan haka ko wata biyu bazan bari ki qara akaiba sai kinyi aure kuma kitashi kificemin anan karki qara zuwa gurina har sai kinsamu madafa" sosai Memartaba yake fad'a ransa a'bace itako Gimbiya TAFISU hawaye takeyi sbd jin zafin fad'an da Memartaba yake mata, sanan tatashi tanufi hanyar fita, Jakadiya ce ta dafata suka fice a shashin Memartaba, shiko Memartaba ransa 'bace yayi shirin fita fada.

  Gimbiya TAFISU kuwa tafiya takeyi zuciyarta na quna sbd fad'an da Memartaba yayi mata, bayi da kuyangi kuwa dake aiki, afilin gidan suna ganinsu suka shiga kaucewa domin sunsan Gimbiya TAFISU bata da kirki ko kad'an, wata kyakyawar yarinya ce qarama da baza ta wuce shekaru 16 ba, amma daka ganinta kasan baiwa ce, domin kuwa yanayinta da kayan jikinta yanuna hakan, tafiya takeyi baiwar tana rangaji tamkar iska zata d'auketa, kanta duqe yake aqasa domin haka take intana tafiya, hanayenta kuma d'auke suke da wani kwandon saqa mai kyau, wanda yake cike da kayan marmari irin su Apple da lemo da inibi da sauransu, kwata-kwata baiwar bata lura da kaucewar da sauran bayi 'yan uwanta sukeyi ba, domin ita kanta aduqe yake, tana cikin tafiya kawai taji tayi karo da mutum, ai kuwa kayan hanunta yafad'i ya watse ko wanne yabi nashi hanyar, cikin sauri ta d'ago kai dan taga dawa taci karo, tana d'ago kai taga Gimbiya TAFISU atsaye agabanta tana huci ga jakadiya agefanta tariqe ha'ba alamun mamaki, da sauri baiwar ta dafe qirjinta, kafin tayi wata-wata, kawai sai sauqar maruka hud'u lafiyayyu akuncinta taji, da sauri baiwar tasa hanunta dukka biyu ta tallafe quncinta tana hawaye domin taji zafin marukan, hakan baiyiwa Gimbiya TAFISU sai da tasa qafarta takwarfe qafar baiwar, ai kuwa baiwar tazube aqasa, Gimbiya TAFISU kuwa takata tayi tabi takanta tawuce, wanda baiwar tasake wani ihun azaba sbd da wuyanta da Gimbiya TAFISU tataka da takalminta mai tsini, ai a take baiwar ta sume Agurin.

  Itako jakadiya duqawa tayi kusa da baiwar tace " kad'an kika gani 'yar talakawa jikar talakawa wanda zata qare abauta ita da uwarta har abada, sauran hukuncin kima sai kinfarfad'o ki kar'bi laifinki"
  Sanan jakadiya tatashi tabi bayan Gimbiya TAFISU.
  Itako Gimbiya TAFISU ranta 'bace tanufi shashinsu, da sauri gudu-gudu tashige parlour d'inasu wanda ya qayatu da kayan ado, wata hamshaqiyar matace fara tas, take zaune akan daya dake cikin kujerun dake parlour d'in bayi ne da kuyangi zagaye da ita wasu suna mata tausa wasu kuma suna wanke mata qafa, matar tana ganin shigowar Gimbiya TAFISU, saita d'agawa bayin nata hannu, ai kuwa duk sukabar abunda sukeyi suka watse, a parlour d'in, Gimbiya TAFISU ce ta qaraso da saurinta ranta a 'bace tafad'a akan qafar matar tana kuka.

  "Cikin tashin hankali Matar tafara shafa bayan Gimbiya TAFISU sanan tace " lafiya Gimbiya TAFISU menene ? wanene yasaki kuka mekika nema baki samu ba arayuwarki har kike kuka fad'amin yanzunan?"
  Cikin shesheqar kuka Gimbiya TAFISU tace " Memartaba ne"
  "Me ya miki Memartaba d'in Gimbiya?"
  Matar tatambayi Gimbiya TAFISU.
  "Cewa yayi nafitar da miji ko kuma ya had'ani da ko waye"
  Cikin masifa matar tace " qaryane wlh ni sarauniya Kaltum qaryane ayiwa 'yata d'aya tilo auren dole sbd haka dolene ajiraki harkifitar da wanda yamiki domin kuwa kece babbar d'iya awanan Masarautar, sbd haka qaryar magauta suyi nasara akanmu"
  Jakadiya ce tashigo cikin tashin hankali, sanan ta dubi Sarauniya Kaltum tace " hutawarki lafiya Sarauniyar Failura uwar Gimbiya TAFISU, yaude kam infad'a miki Sarauniya ran Memartaba ya'baci matura akan har yanzu Gimbiya TAFISU bata fitar da miji ba, kuma tabbas Memartaba zai aikata abunda yace. Idan har lokaci yacika Gimbiya TAFISU bata fitar da miji ba"
  Qarya kikeyi jakadiya!!!!!!!!!!!!
  Sarauniya Kaltum tafad'a da qarfi Sanan tace " ni bazan bari hakan tafaru ba, dolene Memartaba Abdulgafar yajira Gimbiya TAFISU har tafitar da gwaninta"............
  Hhmm muje zuwa, domin kuwa wanan somin ta'bine!
  Wacece Gimbiya TAFISU?

  Anya Memartaba zaijira Gimbiya TAFISU har tafitar da mijin aure kamar yanda Sarauniya Kaltum tace?

  Hhmm shin wanan baiwar da Gimbiya TAFISU tataka mata wuya zata rayu kuwa?
  Sharhinku shi zaibani kwarin gwiyar ci gaba da
  typing.


  Tsarabar Mummyn Minal zuwa gareku my really pants, domin gyaran aurenmu, please wanan sirrin iya matan aure keyinsa banda 'yan mata.
  Kenemi allonki da tawadarki mai kau 'yar uwa, Kirubuta suratul fatiha qafa daya, amma idan kinzo rubuta hakuri da minjaye to ki budesu suyi fadi, sai ki rubuta sunan mijinki aciki da larabci, idan rubutun yabushe sai wanke da ruwa maikyau ki shanye, wlh 'yar uwa zaki qara daraja agurin mijinki sanan zai qara jin sonki da sha'awarki, zakiyi farin jini sosai a gurin sa, Sirri ne mai kyau kugwada ku gani ba mallaka bace, kawai kara danqon soyayya sirrin yakeyi tsakanin ma'arauta, idan mijinki yana wulaqanta kine, ko yana neman matan banza insha Allah idan kinawanan sirrin fatihar zai dawo zuwa gareki, inma zaman lafiya kukeyi zai qara girmamaki da sonki, ku gwada kugani domin nima nagwada kuma naga amfaninsa idan baza ki iya rubutawa ba sai kinemi almajiri kibashi sadaka yarubuta miki kuma dan Allah idan kinsamu dama banda wulaqanci kede kiriqe mijinki tsakaninki da Allah, Allah yasa mudace, bawanda zai kwashi wanan gara'basar sai mai karanta Littafin nan, shi yasa nasaka aqarshen page, Allah yaqara mana zaman lafiya da mazajenmu Amin ya Allah.

  Dan girman Allah in kun karanta kutura zuwa wasu groups d'in nagode.

  Idan kina son shiga group d'in ki tuntu'beni awanan number d'in 09065120158
  Mata zalla.  *ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

Comments

2 comments