Makalu

Sabbin Makalu

View All

MUFEEDA

 •                   EPISODE ONE

     Holma,Adamawa state

  Da tulelen cikinta taje diban ruwa duk cikin yan matan ita ce kadai matar aure idan mijinta na nan ba zai taba bari ta fita deban ruwa ba shekarar su daya da doriya a qauyen da ya zamo garinsu a yanzu ba ta da kowa bata san kowa ba in ba mijin ta ba komai na rayuwrata ya shafe hatta sunanta sai da ya sanar da ita.

  Bata fita ko nan da chan in ba tare da shi ba shi kadai ta sani kuma shi kadai ta yarda da, ba wanda ya san kalar fuskarta duk cikin qauyen in ba qawayenta biyu da take tafiya da su nan ba jumai da laraba.

  Yanzu ma ganin su tayi suna tafiya rafi dake mijin nata ya danyi nisa sai ta   bisu da yana nan ba zai taba barinta fita ba ko rashin lafiya tayi da niqab take fita haka shi ma da zai fita daga gida da hutt yake yawo wanda ba lallai ne ka ga fuskarsa ba,akasarin rigunan sa kenan acewarsa wai "ana neman ran mu ne duk  sanda za a gane inda muke to kashe mu za ayi".......

  Jummai ce ta katse ta da tambaya "mufeeda na jiki shiru kodai mu karba miki ruwan ne kinga baki saba diban ruwa ba amma yau kika bimu kin san halin mijinki amma kika nace ni dai ba ruwana idan ya ganki"

  Ai kia ce haka tunda ku na biyo kuma ma na san ba yanzu zai dawo ba zai kai yamma don cikin gari ya shiga kuma ai........

  Mutum ta ga yana tsaye a gabanta kamar an datsa shi,wani kallo mai firgitarwa yake jifanta da shi maganar da take yi ne taji ya maqele mata a wuya.bata taba ganin bacin ransa kmar wannan ba tsoro ne ya shigeta har sai da yaron cikinta ya motsa, a wurin ta tsaya chak tana neman dauki daga wurin kawayenta ai tana juyawa taga sun arce ruwan na ta zuba a jikin su amma ko kula ba suyi ba suna ta qara sauri Tausayin su ta ji yadda ita ce ta ja musu wannan masifan don ta san ba barin su zaiyi ba sai ya je har gidan su,dama baya son kasancewar su kusa da ita daqer ta samu yana barin ta na muamala da su.

  Ban ankara ba naji bukatin da ke kaina ya fadi passs a qasa tare da zubuwan ruwan da ke cikin,lokaci daya ya fara jan hanun na ina ta tirjewa sanin yau mai kubutar dani daga hannunshi sai Allah.

  Don Allah kayi hakuri na daina daga yau bazan qara fita ba,kuma ma kaga na sa niqaf ba wanda ya ga fuskata,na san ranka ya baci amma na gaji da zama wuri daya na gaji da rashin hira da kowa na..........

  Shut up ,ki min shiru.

  Ai kuwa sit tayi don ta san hali.har suka kai gida.

  Ya turata cikin daki sannan ya sa makulli ya kulle dakin ya fita daga dan qaramin gidan nasu,bai zame ko ina ba sai gidan su jummai,yayi sallama da mahaifinta bayan ya fito ne yace yana son yayi wa yarsa kashedi kada ta qara zuwa gidansa.

  Hakuri mal. garba ya bashi akan hakan ba zai sake faruwa ba,ko sallama bai masa ba ya kama hanya ya tafi.

  Malam garba kuwa yana shiga gida yana tuna irin hirar da ya taba jin jummai nayi akan bakin da suka zo garin su kusan shekara daya kenann da doriya,yadda mijin baya son alakar komai ya shiga tsakanin su da matarsa haka shima in ba gaisuwa ba ba abunda ya taba shiga tskanin su,yar sa akwai zokale zokale ba don haka ba yadda mutumin yayi ta korarsu agidan sa da tana da zuciya da ta daina zuwa.

  amma yau zai korota gobe ta sake zuwa har ya gaji ya barta tana zuwa wurin matarsa ita da laraba amma yau daya matar ta fita shine ya wanke kafa ya zo to ai shima ba son alakar su yake ba kawai dai yana tausayin matar ne don jummai ta na yawan cewa matar ta manta komai na rayuwarta shi bai taba ma ji mutum na manta abu dangane da rayuwar sa ba.

  Da shigar sa cikin gida ya hau jummai da fada,sosai yayi mata fada akan zuwa gidan mufeeda sannan basu san daga inda suka fito ba ba dangin iya balle na baba shima soron mijin yake ace zaman shekara daya amma ba zai iya cewa ga yadda fukarsa yake ba.fada sosai yayi mata sannan ya fita zuwa gun hirar su anan ya hadu da baban laraba suka fara  tattaunawa game da mufeeda da mijin ta.

  ******

  A hanyar sa ta zuwa gidan su laraba yake tunanin da yau wani ya ga feeda ai da ya shiga uku ya san asirin sa zai tonu za a san tana wuri shi yadda hotunan ta ya yadu a social media hatta wasu daga cikin yan kauyen wanda suke riqe manyan woyoyi sun san labarinta kuma sun san kudin da aka sa ga duk Wanda ya san inda take, ya san haka ne lokacin da yaje sayan abu a shago yaji samrin wurin suna hirar kudin da aka sa da sauri kuwa ya bar wurin dadin sa daya tunda ba wanda ya san fuskarta sai yan mata biyun nan sai kuma yau bai san adadin mutanen da suka ganta ba,lallai lokaci yayi da za su bar garin pasa zuwa gidan su laraba yayi don kamar qara tona wa kan sa asiri ne kada ya qara dora musu zargi dama ya san suna zarginsa daga kallon da suke masa tun da ya shiga ciki qauyen.

  Wanan qauyen suka fi dadewa sauran suna yin wata biyu uku zai chanja musu,inda iyayen mufeeda zasu san tana wurinshi da tuni an gama da shi.

  Lokacin da ya shiga cikin gida ,bai nemeta ba don ta bata masa rai yau ya san idan ya shiga zai iya yi mata abunda zai yi nadama daga baya.

  Abinci ya dora a karamin resho din da suke anfani da,abinci mai sauki ya dafa kasancewar ya dan iya,sai da yayi sallah mangariba kamin ya doshe dakin da take

  *******

  Tunda ya fita take kuka,ta kasa gane inda hamma ya dosa(yaya sunan ka kuma kai waye dina" tamabayar da tayi masa kenan lokacin da ta bude idon ta ta ga shi kadai ne wanda yake wurinta a kuma dakin da ta gansu"ki ce min hamma kuma ni minjin ki ne"shine abunda ya gamata kalmar miji ne ya saya mata a rai ko yaya tayi tunanin mijin da yace sai ta ji kanta ya tsara a take zata kawar da wannan tunanin .

  Kuka tayi mai isarta sannan tayi baccin whala ko cikinta da yake kukan yunwa bata yi kokarin sa masa komai ba.

  Bude kofar da yayi ne ya tayar da ita da ga baccin wahalar da tayi,bata matsa daga inda take ba,kwano taga a hannun sa,wanda a take ta ji dan cikinta ya motsa wanda bazai rasa nasaba ba da yunwar da shima yake ji ba.

  Ki tashi kiyi sallah ga abinci in kinidar.

  Bata mutsa ba ta tashi da qer don nauyin da cikinta yayi.bayin da ke bayan dakin ta zagaya  sannan ta yi alwala, a dakin ta shifida sallaya tayi sallah yana nan zaune inda ta barshi tana idarwa ya turamata abincin da ya shigo da shi

  Yi tayi tamkar bata gani ba tana nade hijabin ta nufi kan gado.

  A harzuqe ya miqe dama tunda da safe yake haduwa da abubuwan  da yake bata masa rai yanzu kuma tana son qara masa bacin rai.

  Ki tashi ki ci abunci ko kuma in miki dure,bata motsa ba balle ya sa ran samun amsa ai kuwa dai ranshi ya qara baci,hannun ya miqa don ja wota ta tashi,

  Da sauri ta tashi tana mai cewa kar ka qara tabani bana son kana tabani,na tsaneka,ban sa me kake nufi da ni ba da ka kawo nan ka mayar da ni gun iyaye na, na san qarya kamin da kace kai kadai gare ni "kalaman sa na wattannen da suka shude ne ya dawo mata"baki da kowa iyayen ki sun mutu haka ma dangin ki nine komai naki ki ajiye wannan cikin dakikin kwakalwar ki. Lokacin ne sukayi fadan su na farko a lokacin ne kuma ta samu cikin da ke jikinta watanni takwas da suka shude kenan.

  Na san ina da dangi ko da ban iya tuna su ba ka kaini inda suke in ba sato ni kayi ba.ban yarda da kai ba, Ban san dalili ba amma ina jin wani abu da ba daidai ba a tare da kai, wanda na kasa gane ko menene,haka ma jummai tace min kowa na da dangi.qofa na leqa sai ka hukunta ni akan wani dalili in ba sato ni kayi ba?

  Ni kike gayawa wa haka,yana mai nuna kansa,ni mufeeda.

  Shiru tayi ta gara amsa masa don qwarjin da yayi mata a ido.

  Cikin fushi ya fita daga dakin yana mai buga kofan da qarfi har ta tsorota.

  Jingina yayi a jikin dakin yana mai mayar da nufashi cikin sauri.

  Ina zai sa kansa ya ji sauki,ina zai je ya samu tsira da kuma kwanciyar hankali.

  A kofar gida ya zauna har goman dare kamin ya shigo gidan.

  Lokacin da ya shigo dakin tayi bacci amma tana jan zuciya da alama tayi kuka sosai,gyramata rufuwa yayi.

  Chan kuriyar dakin ya zauna a kan tabarma. ba daki daya suke kawana ba amma tunda ta shiga watan haihuwarta ya dawo dakin ko da wani abu zai faru.bisa kuskure ta samu cikin ba zai kuma bari wani kusre ya qara faruwa ba.

  ***********

  Byan sati daya yana zaune a dakin da ya zama nashi,ta shigo tana mai tafiya da qer riga da zanice a jikinta fuskarta feu ba komai sai kumburin da yayi tun jiya yake gani chanje chanje a jikinta,idon sa ya saukar a kan kafafunta su ma tumbusss suke har takalmin kafarta baya shigar ta sosai.

  Hamma,marata tun jiya nake jin ciwo.

  Cikin tausayi ya dubeta "sannu insha Allah komai ya kusan zuwa qarshe zo in matsa miki kafar na ga ta kumbura sosai,takardar da biron da ke hannun sa ya ajiye

  Zama tayi a kan gadon da ke dakin shi kuma ya zauna a kasa.

  A hankali yake matse mata kafar  har bacci ya fara fisgar ta anan ta bingare ta kwanta.

  Lokacin da ta faraka ba kowa a dakin,wanka tayi sannan ta gabatar da sallar azahar,tana zaune a wurin ya shigo da leda a hannunsa, ajiyewa yayi ya qara fita,kwano ya dauko ya zo ya hada mata fura ya miqa mata.

  Dadi taji sosai dama tunda ta tashi take jin yunwa amma tana tunanin yadda zata fara hura murhu har ta dafa abinci duk da dai kwanan nan hamman bai cika barinta tana wasu ayyukan ba shi yake yin komai har abincin kuwa.

  Shi mutum ne miskili bai cika doguwar magana ba a iya yadda ta fahimce shi yawanci ita ce ke masa hira.

  Yanzu ma da yake zaune a gaban ta ido ya zuba mata,tana shan furar sau da yawa a ido take gane abunda yake son fada

  Ki sha a hankali kar ki kware in bai ishe ki ba sai in kara miki wani

  Hamma velo (yunwa)

  Murmushi kawai yayi ba tare da ya tanka ba yana tuna mufeedan da ya sani shekarun baya,ba wannan da take zaune a gaban sa ba.

  Da yamma ma shi ya girka musu abinci tana zaune suna hira,tun bayan shiryawar su ranar da ta fita ba su sake samun sabani ba dama kullum akan fitan ta ne suke samun matsala da kuma qawayenta da take kawowa shi ke hada su kullum,yasan muddin suna zuwa ko tana fita wata rana asirinsa zai tonu.abunda kuma bazai taba bari ya faru ba. To yanzu duk sun daina zuwa kuma abun yayi masa dadi sosai.

  Cikin bacci ya fara jin nisshinta cikin sauri ya iso inda take

  Mufeeda ya qira cikin tsoron da ya dira masa lokaci daya.

  Hamma bayana ciwo, wayyo hamma (bawo am)

  Da sauri ya riqeta a jikinshi, mufeeda ko muje asibiti ne?tashi muje, bara in dauko miki hijabin ki sai mu tafi

  Hamma bazan iya tashi ba, shafamin bayana hamma.

  Cikin kidima ya dawo yana mai shafa mata bayan cikin ikon Allah ta ji sauki.

  Hamma don Allah ka kaini gun iyaye na kamin in mutu don Allah. Ko ka gayamin inda suke i thought i was dying sai hawaye sharr akan fukarta,ta damu kwarai ta san ita din wacece kuma su waye iyayenta me yasa suka watsara da lamuranta ba wanda ta sani sai mijinta shi din ma bashi da dangi balle aboki su biyu kadai suke rayuwarsu.tana kukan har bacci ya sake fisgarta.

  Hmdala yayi sanda yaga ta samu bacci.to me zai kawo ciwo yanzu a lisafin da aka basu saura sati uku ne haihuwar. Tsorata yayi sosai  da haihuwar ne ta ina zai fara gashi suna da nisa da asibitin uwa uba ba abun hawa. Gashi tana kukan iyayenta bai san ta inda zai fara gayamata ba. ina ma yana da qwarin guiwar fada mata ko ita din wacece da kuma alakar da ke tsakanin su ba wanda ta sani ko take tunani bane......

  Too fa mu je zuwa..

  Mami ishrat

Comments

0 comments