Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Mummunar Dabi'a

Mummunar Dabi'a

  • Mummunar Dabi'a.

    Marubuci:Garba Sidi.

    01.

    Tafiya yake yana raba hanya kamar zai fadi sakamakon kwalabe biyar ya hada da kwarya guda na farin kashi, yazo daidai wata siririyar gada yayinda yake kokarin takawa sai ta zame ya fada cikin kwatanin. Saboda rashin karfin dake tattare dashi Duk iyaka kokari sa na fitowa hakan ya gagara dole ya zauna aciki, wasu matasa biyu suna tafowa sai Dayan yace da abokin nasa "Sadi kamar fa mutum ne acikin kwatar kofar gidansu najib". Sadi ya zubawa gurin idanu domin ya ga ko abinda abokinsa ya fada hakane, da gaggawa yace da abokin nasa "Eh Wlh zo muyi sauri muje gun yanzu haka yaran Nan ne masu saurin idanu da iyayensu basa kula dasu". Gaba dayansu suka danyi gudun karasawa gun, sai suka ga laminu ne dan gidan yawale. "Sadi nikam Gaskiya bazan dauko shi ba, tunda shine ya dorawa kansa masifar shaye-shaye." Yana fadar haka ya ja hannun jamilu suka fara tafiyar su. Laminu yana dago hannu alamar su taimaka masa yayinda bakinsa ke motsawa maganar sa bata fitowa. Tafiyar su Babu jimawa saiga wani dattijo yazo shima zai wuce tagun da sauri ya taimaka masa ya fito, yace "Sannu laminu". Ya kama hannunsa ya jashi Zuwa kofar gidansa ya debo ya ajiye masa a gabansa, yayinda yayi yunkurin daukar wannan ruwa saiya jiri ya debeshi ya fadi, ganin haka sai malam Tanimu ya fara diban wannan ruwa yana wanke masa jikinsa,

Comments

0 comments