Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Mummunar Dabi'a

Mummunar Dabi'a

  • Mummunar Dabi'a.

    Marubuci :Garba Sidi.

    02

    Ana cikin haka saiga wasu mutane biyu sunzo wucewa ta wannan hanya ganin abinda malam Tanimu keyi sai daya yace " malam Tanko kaga mutumin naka can yana wankewa yaron sa kwata". "Rabu da mutanan banza, kawai sanayya tasa ana gani ana cutar da mutane. Kaima ai laifinka ne Mudi kasa wannan dan gidan dan uwan nan naka yazo ya kame su mu huta". "Uhm kaidai kullum maganar ka kenan shifa kamu anayinsa ne da hujja bawai haka kawai Za'a kama mutum ba". "Ah! Hujja ta wuce shaye-shaye da yaron nan yakeyi kuma kaga ai sai a kara da cewa yana dan sace sace acikin unguwa". "To yanzu dai kaga salular tawa ta mutu ba caji" ya dauko wata kodaddiyar salula daga aljihun sa daure take da kyauro "Yawwa idan kayi caji kawai ka kirashi yazo mu huta, kaga maga tsiyar karyar jarin kasuwar da ake mana idan aka kama mai sato masa kudin mutane yana Karbewa". "kai dai bari Mudi Ashe bani kadai abin nan ke batawa rai ba. Shike nan mu hadu idan an jima a majalisa". Suka rabu Tanko yayi kudu Zuwa gidansa shima Mudi yayi arewa.