Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Mummunar Dabi'a.

Mummunar Dabi'a.

  • Mummunar Dabi'a. 

     

         04

     

    Malam Tanimu daya ne daga cikin dattawa a cikin Unguwar dufawa dake karamar hukumar kazaure aciki jahar Jigawa, yana da mata guda daya da ya'ya hudu daya namiji biyu mata, dukkan matan anyi aurensu namijin kwa yanzu haka yana makaranta gaba da sakandare dake garin Kano. Malam Tanimu yana sana'ar saida kayan arkomi ne (kayan abinci). kuma makoci ne ga marigayi Badamasi mai sayar da huluna Wato mahaifi ga laminu. Badamasi nada mata guda daya mai suna Altine sunyi shekara da shekaru basu haifu ba sai daga baya Allah ya basu haihuwar laminu, dukkan su suna da masifa domin kwa malam Tanimu da matar sa sunsha wahala a makwabtaka da su, kuma hakan ya biyo baya na sakamakon kin siyarma da Badamasi gidansa da baiyi ba. Hakan yasa tsangwama da cutarwa sakamakon shi mai arziki ne. Bisa ga ikon Allah yayi hatsarin mota ne ya rasu shida matarsa a wani lokaci sun kai ziyara, laminu ne kadai bai mutu ba a motar a Lokacin yana da shekara 11. A yayin da aka gama binciken gawarwakinsu ne sai aka maika yaron ga wata kanwar Badamasi ta karbeshi to ashe kudin gadonsa take hari, data gama cinye kudin sai ta koroshi gidansa babansa ya dawo nan yake. Malam Tanimu ne kadai ke kula dashi sakamakon rashin mutuncin da mahaifinsa ya aikatawa mutanan Unguwar. Har takai ga ya fada shaye-shaye da sace-sace a Duk yayin da aka kamashi shine ke Zuwa ya karbo shi

Comments

0 comments