Makalu

Sabbin Makalu

View All

SOYAYYAR DA NAYI EPISODE 3

 • ina cikin hawaye raƙiba ta Bini ɗaki tana cewa yar uwa ta na dakatar da ita da hannu

  kin warware kwata amma rabi da kwatan shine misalin nauyin shimfiɗaɗɗen ƙasa da muke takawa kin zaiyyanawa Abdul ƙiyayya a sako da sunan ni na rubuta Abdul yana matukar so na wadda sanadiyar ƙiyayya da nake mishi ne ya ƙaurar da shi zuwa gari mai nisa garinda babu Wanda yasan a ina yake alhali ni ban San yana so na ba wasikar da ya turo min ta karshe kika boye ina so in tabbatar miki da cewa ya shigo hannu na bayan zuwa na gida. abdul ya zaiyyana zafafan kalamai a gare ni,game da soyayya ta. wadda aikaceccen aikinsa neh game da soyayya ta. tabbas ranar wanka ba a ɓoye cibi idan kika yi sanadiya mutuwar Abdul ta wannan hanyar, ki Sani, nima zan mutu.kuma bazan yafe miki ba kamar yadda Abdul ya tafi yana cewa,

  wani irin so ne yake sa masoya suji kanar su tashi a doron ƙasa su koma sararin samaniya, su zamo taurari? shin tsananin so neh yake sa masoya a rudani?, ko-ko tsan-tsan ƙiyayya neh yake haifar da hakan? mai ne-ne tasirin zurfin ciki game da masoyan da suke mutuwar son junan su,amma sun kasa furtawa juna? shin akwai riba a so maso wani, ko ƙoshin wahala ne kamar yadda ake faɗa? wani irin raɗaɗi masoyi ke ji a lokacinda zai yi ban kwana da masoyiyyar sa, ban kwana ta har abada? babu ingantacciyar rayuwa ga masoyinda ya rasa masoyiyar sa. farin ciki yakan nisanta da shi na wani lokaci, yakan shiga ƙunci mai tsanani ya dasa masa bishiyar takaici a zuciya. ingantacciyar rayuwa yana samuwa ne

  ga masoyinda yayi dace da masoyiya na gasjiya.masoyi na gaskiya shine yake jajircewa akan masoyiyar sa ko wuya ko daɗi. shi ke sadaukar da farin ciki ga masoyiyar sa , ko zai dauwama cikin baƙin ciki. shine Wanda so baya ƙaurace wa zuciyar sa, domin yayi dace a so. shine ke ji kamar ya ɗauki masoyiyar sa su koma sararin samaniya, su zamo taurari.

  Allah sarki so a sanadinki na faɗa so maso wani na apka matsananciyar soyayya da zukata ke azaptuwa. ta sanadinki na killace so a zuciya,ta zamo kamar wuta tana min ƙuna. mutunci da mafarin halaƙa ta da ni da ke, kin ban farin cikinda ya faranta zuciya ta. shine makasudin samuwar kishi a kanki.
  Haka ne yasa ko maganar wani ɗa namiji ba na so naji ya fito daga baƙin ki, da zarar kinyi, nakan ji kamar ruhi na zai fita. Nakan yi asarar hawayenda ban san iya adadin sa ba, a wannan lokacin nakan ji na tsani kaina, gami da dana sanin saninki a rayuwa. Nayi iya kokari na domin na kaucewa rayuwar ki, sabida barazanar da kike wa zuciya ta. Kishi a kanki ne, yake auna zuciya ta, yake kokarin fasa ta. Ina matukar daraja ki a cikin rayuwa ta, buri na, a ko da yaushe ki zamo cikin farin ciki da anna'shuwa. Muryar ki ce tafi ko wacce murya daɗi a kunnuwa na. Ji nake kyau, kamar a fuskar ki ne kaɗai ta yada san-sani. Mun saba da ni da ke, sabo na hakika. Tunani na a kullum babu abunda zai kawo rabuwa ta da ni da ke, koma bayan mutuwa.

  Domin, munyi wa juna alkawarin baza mu rabu da juna ba har abada. Duk wannan alkawarin, sai gashi rana ɗaya kince, bakya bukata na a cikin rayuwar ki. Kina bukatar in nisance Ki nisanta na har abada. Ashe duk ƙarfin so, yakan iya zama guba ya gurɓata zuciya? Ina roƙon ki da ki yafe min idan har laifin da nayi miki ne ya sanya ki haka.

  Zan kauracewa rayuwar ki, kamar yarda nayi miki alƙawari tun farkon haɗuwar mu, daga ranar da kikayi fushi da Ni, ya taɓa zuciyar ki, daga ranar zan kauracewa rayuwar ki.

  Na yanke hukuncin hakanne, domin kada halaccin da kikayi min ya zamo butulci. Zanyi nesa da ke kamar yarda kika umurce Ni. Duk da ke halitta ce da ke rayuwa a cikin zuciya ta.

  Sai dai ina taƙaicinda ƙarshen labarin mu, baya sahun cikin labarin da duniyar masoya ke alfahari da shi. Ban kwana na har abada \u270b
  Naki Abdul Nams\ud83d\udeb6

  Na karasa karanta saƙon cikin kuka tare da hawaye mai zafi a fuska ta. Amma raƙiba bata ce komai ba.

  Kinyi mamaki koh? Kinyi mamakin, yarda saƙon ya shigo hannu na koh?
  Ganin yarda raƙiba ta tsorata, idanun ta sunyi tsilli-tsilli. Na kara da ina zanga Abdul?

  Ban san inda Abdul yake ba, a halin yanzu. Amma nayi miki alƙawari, idan muka koma gida, zanyi iya ƙoƙari na, in gano inda yake.

  Wannan kalmar nata suka sa nace" alƙawari fa? Kinyi alƙawari kika ce? Tace eh Mamma nayi alƙawari. Cikin bazata sai Muryar mama muka ji tace, waye Abdul? Duk muka juya cikin tsoro da firgita. Domin mun bar ta a falo. Babu zaton zata biyo mu ɗaki. Sai ta ƙara da cewa" nace waye Abdul?\ud83e\udd7a

Comments

3 comments