Makalu

Blogs » Girke-Girke » Yadda ake tatsar man kwakwa

Yadda ake tatsar man kwakwa

 • Abubuwan da ake bukata

  1. Kwakwa kamar guda uku ko fiye da haka
  2. Ruwan mai dan zafi

  Yadda ake hadawa

  1. Za’a samu kwakwa a fasa ta a bambare ta daga kokonta, sai a wanke sosai a yayyanka kanana kanana yadda injin nika zai iya markadawa a saukake

  2. A dafa ruwan zafi, amma kar yayi zafin da zai iya kona jiki, kuma ya fi ruwan dumi zafi. Amfani da ruwan zafi na taimakawa wajan fitarda mai da yawa.

  3. Daga nan sai a zuba yankakken kwakwan a cikin Blender a kwara ruwan zafin, sai a markada shi har yayi laushi. Idan kwakwar da yawa sai a raba kamar gida biyu ko uku.

  4. Idan ya markadu, sai a tace shi da rariya, a mayarda dusar cikin Blender kuma a kara zuba ruwan zafi a markada don a samu karin madarar kwakwar.

  5. Sai a kara tace madarar da rariyar laushi ko abin tashe shayin domin fitar da kamu kamun dusar da ta ki fita da fari.

  6. Daga nan sai a saka ruwan da kika tace a firji ya kwana. Da safe za a ga man ya yo sama yayi fari sal a daskare abun sha’awa. Za a ga ya raba kanshi da sauran ruwan kwakwan.

  7. Sai a tsame man a tace sauran ruwan domin tabbatar da cewa duka man ne ya fita (kar a zubar da ruwan, za a iya dafa shinkafa da shi).

  8. A sanya man a cikin tukunya a dafa shi na tsahon awa daya da kamar minti ashirin akan wuta mara zafi sosai (low heat). Za a na yi a na juyawa, kar a bar gurin har sai ya yi.

  9. Idan yayi, za a ga man ya rabu da dusar. A tace shi a cikin kwalba da dan karamin abun mataci. Idan bai tacu ba da fari, a sake yi.

  Za a iya amfani da man kwakwarki wajen yin girki, gyaran fata ko na gashi, ko kuma a yi na sayarwa.

  Sannan mai karatu za iya duba: Hanyoyi guda 5 ta yadda kwakwa ke amfani a jikin bil adama da sauransu.

Comments

1 comment