Ga addu’ar nan kamar haka :
ALLAHUMMA AKTHIR MALIY WA WALADIY, WA BARIK LIY FEEMA A’ATAITANEE.
FASSARA : “Ya Allah ka yawaita dukiyata da ‘ya’yana. Kuma ka albarkaceni a cikin abinda ka bani”.
Albarkacin wannan addu’ar da Manzon Allah (saw) ya yi wa Sayyidina Anas bn Malik (ra), Sai da Sayyidina Anas ya rayu kusan shekaru ?ari (100) a duniya. Kuma da idonsa sai da ya ga fiye da ?a?a ?ari daga cikin zuriyarsa.
Haka nan sai da ya zamanto dukiyarsa ta yi albarka ta yawaita sosai. Har ma bishiyoyin dabinon gonarsa sau biyu suke haihuwa duk shekara.
Daga Zauren fiqh
No Stickers to Show