Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Addini da Tarbiyya » Tsarabar Jumma’a: Farillan alwala, sunnoninta da mustahabbanta

Tsarabar Jumma’a: Farillan alwala, sunnoninta da mustahabbanta

 • Farillan alwala
   
  Farillan alwala guda 7 ne:
  1. niyya
  2. wanke fuska
  3. wanke hannaye zuwa gwiwar hannu
  4. shafar kai
  5. wanke kafafuwa
  6. cuccudawa
  7. gaggautawa
  Sunnonin alwala
  1. wanke hannaye zuwa wuyan hannu
  2. kuskure baki
  3. Shaka ruwa
  4. fyacewa
  5. juyo da shafar kai
  6. shafar kunnuwa
  7. sabunta ruwa agaresu
  8. jeranta tsakanin farillah
  Mustahabban alwala
  1. yin bismillah
  2. goga asuwaki
  3. Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye
  4. farawa daga goshi
  5. jeranta sunnoni
  6. karanta ruwa a bisa gabobi
  7. gabatar da dama kafin hau.
  Bayanin tsarki
   
  Tsarki kashi 2 ne:
  1. tsarkin kari
  2. tsarkin dau’da

  1. dukkan su basa inganta saida ruwa mai tsarki, mai tsarkakewa shine: wanda kamarsa bata jirkita ba, ko dandanon sa, ko qamshinsa, da abunda yake rarrabe shi marinjayi. Babu laifi da kasar gishiri da kasar kanwa da makamancinsa.

  2. idan najasa ta fito fili sai a wanke gurin, idanta fantsama sai a wanke tufar gabadaya. Wanda yayi kokwanto acikin samuwar najasa, to sai yayi yayyafi da ruwa ajikin kayan.

  3. Idan kuma wani abu ya sameshi sai yayi kokwanto acikin najastuwarsa, to ba sai yayi yayyafi ba.
  wanda kuma ya tuna da najasa yana cikin sallah sai ya yanke sallar, saidai idan yaji tsoron fitar lokaci. Wanda yayi sallah da ita yana mai mantuwa sai ya tuna bayan yayi sallama to ya sake sallah idan da lokaci.

  Allah ya karbi Ibadunmu ya sa mu cika da Imani

   
  Daga www.alummata.com

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All