Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Ilimin Kimiyya » Yadda ake amfani da waya wajen nemo abubuwan da suka bata

Yadda ake amfani da waya wajen nemo abubuwan da suka bata

 • Sau da yawa za mu batar da abubuwan mu da muke amfani da su na yau da kullum kamar su mukullai, waya, wallet da sauransu, ko kuma ma mu ajiye mu manta inda muka ajiye, mu yi ta faman nema.

  Ita wannan fasaha mai suna Trackr Bravo kacokat din ta an yi ta saboda magance wannan matsala.

  An yi fasahar ne a gida biyu. Akwai manhaja (App) na waya da kuma kanana na’urori (wireless devices) da ake makalawa a kan abunda ka iya bata kamar su wallet ko mukulli, kai har abun hawanka ma idan ka so.

  Yadda ake amfani da shi shine: idan abu ya bata, za ka bude manhajar ka ta wayar android ko iPhone ka latsa gurin da aka tanada. Wayarka za ta nuna maka inda abun yake, idan gurin da nisa,  za ta yi amfani da ‘Google Maps’  wajen nuna maka hanyar zuwa wajen. Idan a kusa ne kuma za ka iya sanya wayarka ta yi kira ga na’urar, ta yadda za ta yi kara kamar na kiran waya.

  Bugu da kari, idan ita wayar ce kanta ta bace, latsa na’urar kawai mutum zai yi sai ta fara kara.

  A yanzu dai wannan manhaja da nau’ra ana Sayar da su ne tsakanin dalar Amurka 30 da kuma 120, kwatankwacin adadin na’urorin da mutum yake bukata.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All