Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Addini da Tarbiyya » Haramun ne mutane su kashe wanda ya zagi Annabi - Sheikh Kabir Gombe

Haramun ne mutane su kashe wanda ya zagi Annabi - Sheikh Kabir Gombe

 • Sakataren kungiyar Izala Ta kasa kuma shahararren mai wa’azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, sabawa Allah da fa?in Annabi Muhammad ? ne jama’a su taru su kashe wani don sun ji ya zagi Annabi ?

  Malamin ya yi wannan tsokaci ne a yayin da ya ke amsa tambayoyi daga Mujallar Zuma Times Hausa a ofishinsa da ke Abuja, inda ya jaddada cewa rashin sanin addini ne ya ke kawo irin wa?annan ?abi’u a cikin al’umma.

  A fadarsa “Babban abunda ke jawo irin wannan shi ne jahilci. Duk lokacin da al’umma ta zauna cikin jahilci kuma ga ta ta na son addini, babu abun tashin hankali kamar mutum yana son Musulinci amma kuma bai san Musulunci ba. Ko wani irin shirme zai iya yi da sunan Musulunci, wanda hakan ya haifo mana da matsaloli da dama a Musulunci kuma har yanzun muna fuskantar hakan.” 

  Malam Kabiru Gombe ya ?ara da cewa ilimi ne kadai zai iya sa Musulmi su gane cewa, ba su ke da ikon yanke hukunci tare da zartar da hukunci ga mai laifi ba face hukuma.

  Ya ci gaba da cewa “Addinin Musulunci bai yarda mutane su dauki doka a hannunsu ba ko da dokar ta Allah ce. Duk wanda ya yi haka ya saba wa Allah da Annabi Muhammadu ? . Hukama ita kadai aka yarda ta yi hukunci sannan ko hukumar ma akwai sharuda da aka gindaya kafin ta dauki hukunci ko ta zartar. Misali, ta yi bincike sosai sannan a samu shaidu da sauransu, kafin alkali ya yanke hukunci sannan a zartar da wannan hukunci.

  Ya kara da cewa “Ba wai kawai da an ce wannan ya zagi Annabi sai a kashe shi ba, to ko da mutum ya ji ba shi ke da hurumin ya yanke hunkunci sannan ya zartar da hukuncin a Musulunci ba. Kai dai naka shaida ne ko ka yi kararsa ga hukuma. Misali in mutum ya yi sata an ce a yanke hannunsa ko in ya yi zina a jefe shi amma ai ba Allah Ya ce ni da ku za mu zartar da wannan hukunci ba sai alkali, kuma dole sai an yi bincike da shaidu kafin a yanke hukunci.

  “Ko a gabanka aka zagi Annabi ? baka da hurumin zartar da hukunci sai hukuma. In har hukumar ba ta dauki mataki ba, babu ruwanka, ita Allah zai tambaya ranar Alkiyama ba kai ba.”

  Rubutawa: Abdul MK, Oktober 2016.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All