Ko a lokacin da ba a shiga irin kuncin rayuwar da ake fuskanta a yanzu ba, akwai wadanda al’adarsu ce kullum su yi korafi.
A lokacin da aka tambaye su da lokacin da ba a tambaye su ba, kullum a cikin kuka suke. Wasu na yin haka ne saboda neman a tausaya masu, wasu kuwa riga-kafi ne na kada su ma a yi masu kuka ko a tambaye su wata alfarma.
Ko ma menene dalilin, wannan dabi’a ta korafi da mutane da dama ba su gani a matsayin komai, ba karamar illa take yi ga rayuwar dan adam ba.
Shi mai korafi a kullum abin da yake mayar da hankalin shi a kai shi ne abubuwan da ba su tafiya daidai a rayuwar shi, kuma ya yi ta furta su da harshen shi.
Duk kuwa abin da mutum yake yawan furtawa da harshensa, ba karamin tasiri yake yi a rayuwarsa ba.
Duk da cewa akwai rahamomi da dama da ya kamata mutum ya gode wa Allah a kansu, sai ka ga mutum ya manta da su.
Illolin hakan su na da dama:
Rashin godiyar ubangiji da yawan korafi su na haifar da kuncin rayuwa da bacin rai sannan su haifar da rashin wadatar zuci.
Saboda duk wanda yake da wannan hali, a kullum ya na mayar da hankali ne a kan abubuwan da za su bata masa rai, wato abubuwan da ba su tafiya daidai a rayuwar shi.
Za ka ga mutum mai godiya duk da cewa ba shi da shi da yawa, a kullum a cikin annashuwa yake. Hakan na faruwa ne saboda yadda yake mayar da hankalinsa ga rahamomin Ubangiji, kullum yana yi wa kansa tuni da su, kuma yana gode wa Allah.
Wannan yana sanya haske a zuciya ya sanya farin ciki.
Illa ta biyu ita ce dawwamar talauci a rayuwar mutum.
Duk wanda ba shi da godiyar Ubangiji to tabbas Allah zai bar shi a yadda yake, ya yi ta fama da rayuwa babu ci gaba.
Shi kuwa mai Godiya, alkawarin Ubangiji shi ne zai ci gaba da kara masa.
Illa ta uku ita ce rashin samun kuzarin fuskantar kalubalen rayuwa.
Yawanci lokuta kalubalen da muke fuskanta a rayuwar mu wata dama ce na mu inganta ta, mu samu ci gaba daga inda muke.
Yayin da wanda yake da godiyar Ubangiji zai yi saurin fahimtar haka, wanda ba shi da godiya korafi zai ta yi ya kasa katabus. Maimaikon ya yi yunkurin neman mafita ga kalubalen na shi, bacin rayuwa zai shiga saboda a ganin shi, kullum rayuwa ba ta kyauta masa ba.
Na hudu akwai illar da korafi yake haifar wa zamantakewa. Mutane masu yawan korafin ba su da dadin zama. Kullum yadda ka san su kadai ke da matsala, da dai sauransu.
Mu sani cewa, duk abin da ya faru da mutum a rayuwar nan, mai kyau ko mara kyau na da dalili, kuma idan muka yi natsattsen nazari a kai, za mu ga cewa akwai wata rahama ta Ubangiji a ciki.
Shi ya sa a kowane hali mutum ya samu kan shi, mai kyau ko mara kyau, to yana da kyau ya kasance a cikin godiyar Ubangiji.
Allah ya bamu ikon mayar da hankalinmu ga rahamominsa da suka cika rayuwarmu.
Mai karatu na iya duba: Abubuwa guda 5 dake hana dan adam ci gaba
No Stickers to Show