Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Ra'ayoyi da Tahalili » Rage farashin aure a kasar Hausa: Gyara ko batawa?

Rage farashin aure a kasar Hausa: Gyara ko batawa?

 • A wasu 'yan makonni da suka gushe ne karamar hukumar Dambatta da ke jahar Kano ta ja hankalin 'yan Nijeriya musamman 'yan Arewa a sakamakon wata doka da ta kafa da ta kayyade farashin aure da nufin saukaka yin auren ga matasa da kuma magidanta masu neman kari.

  Tun kafin nan ma, akwai wannan tsari a karamar hukumar Gezawa da ma wasu kauyuka a Kano da Jigawa.

  A gani na, fito da irin wannan tsari na nuna irin rashin fahimtar da mahukunta ke yi wa matsalar auratayya a kasar Hausa.

  Shin rashin aure ne matsalar ko kuma rashin rikon sa?

  Mutum ne Allah ya bashi ikon ya yi aure, duk da cewa ana ganin farashin sa na da tsauri. Duk da haka bai yi shayin sako matar ba bayan watanni shida saboda ba ta gama dafa masa abinci da wuri ba.

  Toh shi wannan mutum shi aka kuma kara saukakawa yin auren. Ka ga kenan an ce masa ya yi ta aura ya na saki.

  Hakika wannan tsari zai taimakawa wasu mutane tsiraru da Allah ya riga ya rufa masu asiri suka san darajar aure, kuma suka iya rikewa. Amma fa a ra’ayi na mafi yawanci an basu damar yin aure kamar saka riga da tube ta.

  Haka zalika an bude kofar kara wulakanta mata ma’aurata a gidajen su a gurin mazajen da ma can ba su ganin darajar su. A maimakon a gyara, wannan tsari ka iya dagula al’amura, saki ya kara yawaita.

  Kuma ma idan ana ganin an saukakawa mai yin aure, shin shi kuma wanda ya ke aurarwa fa? Shin za a iya rage masa adadin kujeru ko kuma farashin gado ko kuma yawan gara?

  A ganina, farshin aure a kasar Hausa ba shi ne matsala ba. Tabbas wadanda suka auri wasu kabilun za su tabbatar da hakan. Ina ganin a fadin Nijeriya ma, babu inda iyayen yarinya ke taimakawa namiji wajen auren ‘yar su kamar yadda Bahaushe ke yi.

  Mafi girma a cikin matsalolin auratayya a kasar Hausa kamar yadda na rubuta a baya kuma wadanda mahukunta suka gaza duba a kai sun hada da:

  1. Rashin sanin daraja da hakkokin aure
  2. Kaucewa koyarwar Manzon Allah (SAW) game da zamantakewar ma’aurata
  3. Girman kai ga maza, rashin kunya ga mata
  4. Aure a bisa dalilan da ba su da karfi (kamar kyau, sha’awa ko kudi)
  5. Karin aure yayin da babu ikon yi
  6. Rashin adalci da wulakanta abokin zama
  7. Rashin bin ka’idojin saki
  8. Jahilci da kidahumanci
  9. Rashin hakuri da fahimtar abokin zama
  10. Baiwa al’adu muhimmanci fiye da addini da sauransu

  Mahukunta a wadannan kananan hukumomi ba su yi kokarin gyara wadannan abubuwa ba, a’a burinsu shi ne su mayar da auren ya zama kamar wani abun wasa.

  Idan an ragewa mutumin da ba shi da karfi farashin sadaki, an kai masa mace da kayan daki da kayan abinci, shin wannan zai rage masa nauyin hakkokin aure da ke kansa ne?

  Idan aka yi duba da wannan, ba abun mamaki bane da yawa a cikin matasa ke yin aure bisa dalilan da basu dace ba, kuma suka gaza fahimtar darajar da aure ke da shi.

  Ina ganin ya kamata a mayarda hankali wajen gyara zamantakewar ma’aurata, a ilimantar da samari da ‘yan mata cewa shi fa aure ba a ana yin sa ne domin a rabu ba, a tabbatar da cewa duk wanda zai yi aure ya fahimci menene ma’anar auren ma, tukunna sai a yi maganar saukaka shi. Kuma a saukakawar ma, sai a bi ka’idar addini.

  Duk wannan tsarabe tsaraben al’adar ba su ke gyara aure ba. A yayin da aka bar batun lefe da karya da nuna iyawa, mutum ya biya sadaki kawai, sannan aka bar shi da cika gidan sa da kayan daki da abinci kafin ya yi aure kamar yadda addini ya tanadar, wannan ma ai saukakawa ne, ko kuwa?

  Idan kuwa aka gaza yin haka, toh gwamnatoci da ‘yan siyasa sai su kara azama wajen shirya auren zawarawa.

  Daga www.alummata.com

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All