Makalu

Blogs » Harshe da Adabi » Wani irin zamani

Wani irin zamani

 • Ga zamanin da kyan hali bai da wani tasiri
  Ga zamanin da mai kudi kadai ke shan kida da kirari
  Ga zamanin da nagartarka sam ba ta zamma jari
  Ga zamanin da gaskiyarka sai ta ja ma sharri
  Ga zamanin da an bar duban wata an koma ga taurari
  Ga zamanin da kai cikin daula makobcinka na ta burari
  Ga zamanin da cin haram shi ke sanya kumari
  Ga zamanin da shagaltuwa ta sa ba a tunano qabri
  Ga zamanin da birgiya na ga wanda ya kunna sigari
  Ga zamanin da fitsara da ita ake alfahari

  Daga Hassan Y. A Malik 

Comments

2 comments
 • Adamu Garba
  Adamu Garba Ubangiji ya Raba mu da Sharrin zamani!!!
  October 25, 2016 - 1 likes this - Report
 • Nura Ahmad
  Nura Ahmad To yanzu menene mafita? Duk da cewa bayanin yayi kama da rubutacciyar waka ta hausa...amma ya kamat ace an fede wannan waka an fidda maanoninta da kuma samo hanyar mafita. Da fatan zaa tattauna sosai akai, musamman in mai turowa ta sanya wata tambaya da...  more
  November 4, 2016 - 2 like this - Report