Makalu

Abubuwa 10 da ya kamata a sani game da marigayi Abu Ali

 • Mutanen Nijeriya, manya da kanana na ci gaba da jimamin rasuwar jarumin kwamandan sojojin sashe na 272 mai kula da tankokin yaki wato Laftanal kanar Abu Ali wanda ya rasu a ranar juma’ar da ta gabata yayin da mayakan Boko haram suka kai masa farmaki a garin malam Fatori tare da wasu sojoji hudu a gurare daban daban.

  Ga Abubuwa guda 10 da ya kamata kowa ya sani game da wannan jajirtaccen soja:

  1. Kanar Abu Ali Banufe ne dan asalin jahar Kogi kuma da ga Brigediya janar Abu Ali wanda ya rike mukamin gwamnan jihar Bauchi a lokacin mulkin janar Ibrahim Babangida tsakanin shekarar 1990 zuwa 1992, kuma wanda a yanzu haka shi ne Etsun garin Bassa Nge da ke jahar Kogi

  2. Shekarunsa 36, an haife shi ne a watan Agustan shekarar 1980 a jahar Lagos.

  3. Ya bar mata guda daya mai suna Samira da ‘ya'ya guda uku.

  4. A watan Satumbar shekarar 2015, marigayi kanar Abu Ali ya samu karin girma daga mukamin manjo zuwa mukamin laftanar kanal duk da cewa bai kai matsayin a ba shi wannan mukami ba, ya samu karin girman ne a sakamakon namijin kokari, da jarumtar da ya nuna a wasu hare-hare da rundunar ta kai wa mayakan Boko haram.
   
  5. Shi ya ja ragamar rundunar da ta karbo garin Baga, Gamboru Ngala, Mungonu da sauran garuruwa daga hannun mayakan Boko Haram.

  6. Ana yi masa lakabi da Sarkin Yaki (lord of War) a sakamkon rashin tsoro da halin jajircewarsa. Duk da cewa yana da karamin jiki, ‘yan uwansa sojoji da dama na kwatanta shi ne da zaki, dodon mayakan Boko Haram.
   
  7. An yi masa shedar cewa mutum ne mai kamala, mutunta mutane, kirki mai kuma matukar kishin kasar sa, da a koyaushe a shirye yake ya mutu domin ya ga ta zauna lafiya, sannan kuma ba ya burga.
   
  8. Shi ne matukin tankar yaki kirar T-72 wacce aka yi hasashen ta fi kowacce kira kyan aiki a Arewa maso gabashin kasar nan, a don haka ne illar da ke yi wa mayakan Boko Haram a lokaci daya ta fi karfin wanda sojoji guda 300 za su iya yi.
   
  9. Ya samu lambar yabo daga shugaban rundunar sojin Nijeriya na kasancewarsa abin kwatance wajen jarumta, karfin zuciya da iya aiki.
   
  10. Saboda matukar iya shugabancinsa da iya karfafa gwuiwar na kasa da shi, da kula da bukatunsu, da shiga gaba a duk inda aka dosa, daya daga cikin sojojin da suke tare ya taba hasashen cewa kanar Abu Ali shi zai zo ya zama shugaban rundunar sojojin Nijeriya a nan gaba
   
  Allah ya jikansa da rahama, ya sa jarumtarsa ta zama a bar koyo ga ‘yan baya. Allah ya biya shi da gidan Aljanna, ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashinsa, idan ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.
   
  Daga www.alummata.com

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

  Posted Fri at 4:38 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wan...

 • Yadda ake hada spring chin-chin

  Posted Thu at 10:16 AM

  Assalamu Alaikum. Barkan mu da warhaka. Ayau na sake zuwa mana da sabuwar makala ta girke-girke wacce ciki za mu koyi yadda ake soya spring chin-chin. Abubuwan hadawa Flour (4 cups) Baking powder (1 teaspoon) Butter (125grms) Mangyada Gishiri (1 teaspoon) Ya...

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

View All