Makalu

Blogs » Ra'ayoyi da Tahalili » Illoli guda 5 da almajiranci ke haifarwa a kasar Hausa

Illoli guda 5 da almajiranci ke haifarwa a kasar Hausa

    1. Ya na hana yara samun kulawar da za ta tabbatar da sun girma sun zama mutanen kirki da za su zama abun alfahari ga al'umma
    2. Ya na kashewa yara zuciya ta hanyar sanya su yin bara, wannan mutuwar zuci ka iya binsu har girman su
    3. Ya na kara yiwuwar koyan muggan halaye a wajen yara, kamar su shaye shaye, sata da sauransu, musamman duba da yadda yara ke gararamba a gari babu kyakkyawar kulawa
    4. Iyaye na daukar zunubi a sakamakon yasar da hakkokin da Allah ya dora masu na ciyarwa, tufatarwa, ta tarbiyantar da 'yayansu
    5. Ya na dakilewa yara damar samun ilimin boko, wanda idan aka hada shi da na islama, na matukar inganta rayuwar dan Adam

Comments

1 comment