Rubutu

Blogs » Tarihin Mutane » Takaitaccen Tarihin Marigayi Aku-Ukan Wukari na 27

Takaitaccen Tarihin Marigayi Aku-Ukan Wukari na 27

 • Marigayi (Dr) Agbunshu Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, jajircecen sarki ne a zamanin shi kuma haziki, ya kasance sarki mai daraja ta ɗaya kuma Shugaban majalisar sarakunan jahar Taraba (chairman Taraba Council of Chiefs).

  Marigayin ya kasance shine Aku-Uka na 27 a cikin jerin Aku-Uka da a kayi a tarihin masarautar Aku-Uka. Sannan kuma shi ne mafi daɗewa a kan karagar mulki. Mutum ne shi mai nagarta. Yana da haƙuri, jajircewa, ƙwazon aiki, son jama’a, da kuma iya zama da jama’a.

  HAIHUWA

  An haifi Marigayi (Dr) Agbunshu Shekarau Angyu Masa Ibi a ranar 18 ga watan Afirilu na shekarar 1937 a cikin garin Wukari.

  Shi dai Marigayi Aku-Uka na 27 (Dr Shekarau Angyu) ɗa ne ga Ashumanu II Angyu Masa Ibi, Aku-Uka na 22, wanda ya yi zamani a shekarun 1940 – 1945. Sunan mahaifiyarsa Buvini Awudu. Ya fito daga zuriyar Ba-gya, ɗaya daga cikin gidajen sarautar Wukari.

  Wannan suna nasa Shekarau, suna ne da ya samo asali daga Hausa. A al’adar Malam Bahaushe, idan mace mai ciki ta haura wata tara bata haihu ba, to akan kira abin da ta haifa da suna shekarau idan namiji ne, mace kuma a ce da ita shekara. Wato ana nufin mutumin da ya shekara a ciki. Sunansa na yare kuma shi ne Agbunshu.


  KARATU:

  Marigayi (Dr) Agbunshu Shekarau Angyu Masa Ibi ya fara Makaranta da makarantar Firamari ta Wukari Elementary School a shekarun 1950 – 1954.

  Ya kuma yi makarantar gaba da Firamari ta Mishan ta Lapwe da ke Ibi (Missionary Senior School Lapwe) a shekarun 1954 – 1957.


  AYYUKA:

  Marigayi (Dr) Agbunshu Shekarau Angyu Masa Ibi ya fara aiki ne da Hukumar Gargajiya ta Wukari a matsayin jami’in rarraba wasiƙu (mail officer), daga baya aka ɗaukaka matsayinshi zuwa jami’in sufuri; wato babban direba (transport officer) a tsakanin shekarau 1958 – 1960.

  Ya kuma yi aiki a matsayin Jami’in Taimako (personal assistance) ga ‘executive officer’ na ma’aikatar kula da lafiyar dabbobi (ministry of animal health) na gwamnatin arewa da ke Kaduna a shekarun 1960 – 1962.

  A shekarun 1962 – 1963, Marigayin ya kasance Jami’in Taimako (personal assistance) a ofishin sakataren mulki (parliamentary secretary) na gwamnatin arewa da ke Kaduna a wancan lokacin, Ambasada Jolly Tanko Yusuf shi ke shugabantar wannan ma'aikatar.

  A shekarun 1963 – 1966, ya kasance Jami’in Taimako (personal assistance) a ofishin shugaban ma’aikatar wutar lantarki ta Najeriya (Electricity Corporation of Nigeria), zamanin jagorancin Malam Ibrahim Sangari Usman.

  A shekarun 1966 – 1976, Marigayi ya kasance Jami’in Ciniki (sales manager) a gidan man-fetur na Makurɗi (Texaco filing station, Makurdi) dake jihar Benue.

  SARAUTA:

  A ranar 28 ga watan Agusta na shekarar 1976, aka bayar da sanarwar naɗin (Dr) Agbunshu Shekarau Angyu a matsayin sabon Aku-Uka na Wukari na 27.

  Naɗi na (Dr) Agbunshu Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, ya samu karɓuwa tare kuma da amincewar ‘yan majalisar sarki kuma masu zaɓen sabon sarki guda huɗu, da kuma yarjewar iyalan gidajen sarauta guda biyu; Ba-gya (Kuvyo) da kuma Bama.

  (Dr) Agbunshu Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, ya kasance sarki da yayi sarauta na tsawon shekaru 45 a karagar mulki.

  A zamanin sarautar shi ya kawo cigaba matuka a yankunar da yake sarautar su duk da cewa akwai ɗan wasu tsauko da yayi ta fama da su na faɗace-faɗace na makiyaya da manoma, da na kabilu amman duk da hakan yankin shi ya kasance yankin da ya cigaba matuka a jihar Taraba.

  An karrama sarautar Aku-Uka zuwa sarki mai daraja ta ɗaya a Shekarar 1982.

  MUTUWA:

  An sanar da mutuwan marigayi (Dr) Agbunshu Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II a ranar 10 ga watan Oktoba shekarar 2021 bayan ya fama da gajeruwar rashin-lafiya.

  MATASHIYA:

  An rubuta wannan takaitaccen tarihin ne bayan nazarin wasu littafafan tarihi. Idan har akwai wani kuskure da mai karatu ya samu, to ana iya tuntubarmu da bayanai gamsassu don mu gyara. Ana iya aiko mana da sako ta imel na mu: admin@bakandamiya.com

Comments

2 comments