Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Rayuwa da Zamantakewa » Abubuwan dake ruruta wutar fyade cikin al'umma

Abubuwan dake ruruta wutar fyade cikin al'umma

 • An bayyana fyade da amfani da karfi wajen tilasta wa mace ko na miji jima'i ba tare da son su ba. Fyade dai akasari ana yi wa yara mata ne wadanda suke tasowa, ma'ana wadanda ba su balaga ba, ko shekarunsu bai kai goma sha takwas ba. Fyade ya kasance babbar laifi a fiskar shari'a wanda kan kai ga yanke wa wanda ya aiwatar da ita hukuncin daurin rai-da-rai a gidan yari. Fyade dai, har ila yau ya kasance babbar masifa a yankin kasashe masu tasowa.

  Masana sun bayyana rashin kulawa ga yara mata da abu da yake kawo lalacewar 'ya'ya mata wanda kan kai su ga fadawa ga ukubar fyade. Ya tabbata da in aka ilmantar da yara mata ta yadda za su yi mu'amala ingantacciya cikin al'umma ba a samu yawaitar fyade cikin wannan al'ummar ba.

  Da wannan za a iya cewa rashin ilmi na daya daga cikin ababen dake janyo yawaitar fyade cikin al'umma. Masana sun kuma bayyana yawan mu'amala tsakanin yara maza da mata da abu da yake haifar da fyade cikin al'umma. Ko shakka babu, shiga da wasu 'ya'ya mata ke yi na daya daga cikin ababe da yake jefa su ga bala'i da ukubar fyade.

  A duk lokacin da mace ta sanya kaya wanda yake nuna tsiraicinta to ko shakka babu wannan mace na tallata kanta ne ga masu fyade. Har ila yau an bayyana yawan shaye-shaye cikin al'umma da abu da yake janyo afkawa cikin bala'in fyade, dama sauran muggan alfasha.

  Sannan mai karatu na iya duba: Sababbin hanyoyin yi wa mata fyade da matsalar fyade ga 'ya 'ya mata da sauransu.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
 • Ku latsa nan don karanta babi na takwas. Ga ɗaurin Zahra Buhari. Ni dai ban iya ɗaurin ba. Yayata ke kafa min in zan je biki. In kuwa fita yawo ne ɗaurin 'yan Hausa na ke yi mai lankwasa a gaban nan. "Mama!" Ta furta cikin mamakin ganin ta. Bata saurareta ba bare ta amsa, cikin hanzari ta isa bak...
 • A kwanakin baya na ga wani tattaunawa a social media game da zuwa aiki ga mata, musammam matan aure da kuma mata masu yara. Abinda na lura shi ne yawanci mazaje ba su fiya son matansu na zuwa aiki ba duk da cewa yawancin mazan na so a ce matansu sun yi karatu sosai kuma sun waye da sanin abubuwan ra...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Mai Haƙuri Ya Kan Dafa Dutse. A ƙasashen ƙetare an yi wani ɗan Sarki ana kiran sa Bihizadu. Ya kasance kyakkyawa ne, kuma yana da kirki domin kuwa yana zama tare da talakawa da fatake da attajirai. Mutane suna son sa, sai dai yana da saurin ƙagauta a al'amuran ...
View All