Rubutu

Blogs » Kiwon Lafiya » Amfanin man zaitun ga rayuwar bil'adama

Amfanin man zaitun ga rayuwar bil'adama

 • Man zaitun dai mai ne da ake amfani da shi tun zamanin Kaka da kakani musamman a wurare da aka san amfanin shi. A wasu sassan ana amfani da man a abinci ko a shafa yayin da aka sami wani rauni. Manazarta a fannin kiwon lafiya sun bayyana wasu daga cikin alfanun man zaitun ga rayuwar bil'adama, wanda suka hada da:

  1. Man zaitun na magance cutar kansa (cancer): Kamar yadda wata kungiya masu kula da fannin kiwon lafiya a kasar Espaniya (Spain) suka tabbatar man zaitun na matukar taimako wajen rage barazanar cutar kansa sabili da sinadarin "antioxidants" da yake dauke da shi.

  2. Man zaitun na kuma magance cutar suga (diabetes): Kwararru a fannin yaki da cutar suga sun tabbatar da amfani da man zaitun na rage yiwuwar kamuwa da cutar suga mai lamba 2 wanda ke da matukar hatsari ga rayuwar bil'adama sabili da wasu sinadaran da ke dauke a man na zaitun.

  3. Man zaitun na kuma kone kitse: A wani nazari da aka gudanar a jami'ar Navara dake garin Las Palmas dake kasar Espaniya (Spain) ya tabbatar da duk mai amfani da man zaitun wajen cin man, da cewa man zai taimaka mishi ta hanyar kone akasarin kitse da zai iya illa ga rayuwar mutumin. Kana har ila yau hakan zai samarwa mai amfani da man natsuwa a kwakwalwar shi.

  4. Man na kuma gyara fata tare da samar da sumar gashi. Masana sun tabbatar da amfani da man na zaitun na taimakawa fatar jikin bil'adama saboda yana dauke da sinadarin vitamin A da Kuma vitamin E wanda dukkannin su suna taimakawa fata. Har ila yau kuma sun bayyana man zaitun da yana taimakawa wajen samar da sumar kai. 5. Man zaitun na kuma magance cutar ciwon zuciya: A bayyanai da dama da manazarta suka gudanar sun tabbatar da cewa man na zaitun na taimakawa wajen rage barazanar cutar ciwon zuciya musamman ga tsofaffi.

  Wannan na nuna cewa amfani da man na zaitun zai taimaka gaya wajen kare lafiyar mutum.

Comments

0 comments