Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Illolin shaye-shayen kwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

Illolin shaye-shayen kwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

 • Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin al'umma musamman ma matasa maza har da ma mata, masu aure da wadanda ba su da shi shaye-shaye na nufin duk wani yanayin da bil'adama zai sa kan shi don sauya yanayin tunaninsa ko nazarin shi ta yadda ba zai iya bambanta ya kamata da akasin hakan ba.

  Shaye-shaye na zuwa ne a yayin da mutum ya afka cikin shan kwaya sabanin yadda aka kayyade a sha shi, ko kuma shan giya ko tabar wiwi da dai sauran nau'ukansu wadanda za su bugar da mutum ko su kai shi ga maye.

  Wasu daga cikin nau'ukan shaye-shaye:

  1. Shan maganin da doka ya hana amfani da shi.
  2. Shan magani barkatai, batare da izinin likita ba.
  3. Wuce umurnin likita wajen shan kwayoyi
  4. Shan giya da duk wani abin da zai bugar da mutum.

  Wasu daga cikin dalilan da ke sa shaye-shaye:

  1. Jahilci
  2. Matsalolin Rayuwa
  3. Al'adu
  4. Hulda da abokan banza
  5. Sakacin iyaye
  6. Yanayin wurin zama
  7. Aikin karfi
  8. Samun kwayoyin cikin sauki

  Wasu daga cikin miyagun kwayoyi da akafi amfani da su wajen shaye-shaye:

  Biyo bayan shan giya da tabar wiwi da sholishon da hodar ibilis wajen buguwa ko maye, mashaya har ila yau, na amfani da wasu kwayoyi don buguwa wadanda suka hada da:

  1. Valium tabs
  2. D5 tabs
  3. Diazepam tabs
  4. Exol 5 tabs
  5. Tramadol tabs
  6. Pemoline tabs
  7. Emzolyn expectorant
  8. Tutolin expectorant
  9. Codeine syrup
  10. Benalyn syrup
  11. Pacaline syrup
  12. Pento injection
  13. Legatine injection

  Wasu daga cikin matakan shaye-shaye:

  1. Matakin farawa ko gwaji:- wannan shi ne mataki na farko wanda mutum zai soma kusantar ko soma mu'amala da masu shaye shaye har ta kai shi ga soma tabawa kadan.
  2. Shaye-shaye a matakin ganin dama:- Wannan matakin mai shaye shayen yana sha ne lokacin da ya ga dama, ba ya saya da kudinsa, sai an samu na banza ko na bati.
  3. Matakin Shaye-shaye ba kakkautawa:- wannan shi ne matakin kama shaye shaye gadan-gadan, ko da kudi ko babu sai an sha.
  4. Matakin dogaro da shaye-shaye:- wanda ya kai wannan matakin to lallai ba zai iya komai ba sai ya sha idan bai sha ba kuwa ba ba zai iya zama lafiya ba, wanda ya kai wannan matakin kullum za ka same shi ko same ta cikin maye, a wannan matakin ana iya sata domin a sayi kayan mayen.

  Wasu daga cikin illolin shaye-shaye:

  Biyo bayan kawo rashin karbuwa a wurin mutanen arziki da zubar da mutumci, shaye-shaye kan janyo:

  1. Talauci da jahilci,
  2. Ciwon huhu
  3. Ciwon hauka
  4. Ciwon hanta
  5. Ciwon kansa
  6. Ciwon suga
  7. Ciwon sanyin kashi
  8. Ciwon sankarar mama
  9. Yawan tunani mai tsanani da muni wanda zai kai ga ciwon hawan jini da zuciya
  10. Yana kawo lalacewar mazakuta
  11. Yana kawo lalaci, yadda mai shaye shaye baya iya'yin komai sai ya sha.

  Wasu daga cikin hanyoyin da za'abi wurin magance shaye-shaye

  Bayan hubbasar gwamnati a matakai daban-daban wajen hana fasa-kwabrin kwayoyin, har ila yau ya zama dole iyaye su tashi tsaye wurin kula da tarbiyyar yara da matasa, sannan su dinga kula da harkokin yaransu na yau da kullum, su kuma kula da irin abokan da yaransu suke hulda da su. Dole ne sarakuna da malaman addinai su ma su tashi tsaye wurin tsawatarwa da fadakar da al'umma bisa illar shaye-shaye ta mahangar addini da rayuwa. Dole ne kuma al'umma su ba da hadin kai wurin taimakawa jami'an tsaro da jami'an yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi wurin gudanar da ayyukansu.

  Mai karatu na iya duba: Illolin shan miyagun kwayoyi ga matan aure da makamantasa.

Comments

0 comments