Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Fassarar wasu sunaye daga harshen Fulatanci zuwa Hausa da karin haske cikin harshen Turanci

Fassarar wasu sunaye daga harshen Fulatanci zuwa Hausa da karin haske cikin harshen Turanci

 • Suna dai lakabi ce da ake sanyawa mutun, ko wuri, ko dabba, ko wani abun don banbanta wannan abun daga sauran dangin abubuwa. A sau dayawa mutane kan sawa ya'yan su suna saboda sha'awa ko wani dangin yanayi mai alaka da hakan.

  Shi dai suna kamar yadda addini ya hukunta dole ne ga uba ya radawa dan'shi ko yar'shi suna da al'umma zasu ke amfani da shi wajen alaka da juna. A bisa wannan dalilin kabilu dayawa na amfani da wani yanayi na murna ko al'hini wajen radawa ya'yan su suna.

  A kabilar fulani akwai sunaye da dama cikin yaren fulatanci da ake radawa yara yayin da aka haife su. Cikin wannan takaitaccen rubutun munyi kokarin zakulo muku wasu daga cikin sunaye da fulani ke sanyawa ya'yan su, tare da fassaran wadannan sunayen cikin harshen Hausa dama karin bayani ko haske cikin harshen Turanci. Wadannan sunayen sun hada da:

  1. Ardo Shugaba (The Leader).

  2. Gidado - Masoyi (The Loved One).

  3. Barkindo - Albarkantacce (The Blessed One).

  4. Chubado Zabebbe (The Choosing

  5. Gaabdo - Farin-ciki (The Joy).

  6. Chenido - Mai hakuri (The Persevere) Not too sure.

  7. Modibbo - Malami (The Lettered One).

  8. Labbo - Takobi (Sword).

  9. Bodéjo - Ja (Red)

  10. Balewa/Baleri - Baki (Black).

  11. Danejo - Fara (White).

  12. Manga/Maudo - Babba (Big/Senior).

  13. Petel/Peto - Karami (Small especially a brother or a sister).

  14. Adda Manga - Babbar yaya (senior sister)

  15. Adda Petel - Tokwaran uwa (this name is usually given to a daughter that namesake her mother's or Father's junior sister)

  16. Baldo - Mai taimako (helper).

  17. Bello - Kyakyawa (Sweetness).

  18. Gaji - Dan'auta (Last born).

  19. Muido - Mahakurci (The Patience one).

  20. Iya - Uwa (A senior brother).

  21. Hamma/Bobbo - Wa/Yahya (A senior brother).

  22. Chuto - Dan'takwaye (A twin).

  23. Dadda/Adda - Babbar yaya (A senior sister).

  24. Lamido - Sarki (King).

  25. Jauro - Yarima (Prince).

  26. Jagordo - Jagora (A Lieutenant).

  27. Dada - Uwa (A mother).

  28. Ba-Petel - Tokwarankaka (Grandpa's namesake).

  29. Ba-Manga - Tokwaran wa/kanin kaka (Grandpa's senior or junior brother's namesake).

  30. Garga - Gwarzo (Champion).

  31. Buba - Amintacce (Trustworthy person).

  32. Shatu - Jagoran mata (Women leader).

  33. Kwairanga - Alheri (Blessing)

  34. Geedè - Rabo (Success)

  35. Jungudo - Dalili (fate)

Comments

0 comments