Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Matsayin kunya a al’adar Bahaushe

Matsayin kunya a al’adar Bahaushe

 • Gabatarwa

  Tun gabannin cudanyar Hausawa da wasu, Bahaushe mutum ne mai kyawun tsari kan al’amurar da suka shafi rayuwarsa na yau da kullum. Mutum, ne mai kykkyawar riko ga al’adarsa ta gargajiya, musammam ga abubuwan da suka hada da addininsa, tufafinsa, muhallinsa, sana’o’insa, zamantakewarsa, tarbiyar sa da kuma umurni da hani, wanda ya hada da “kunya” a cikinsu. Ganin irin muhimmancin da Bahaushiyar al’ada ke da shi wurin Hausawa ne, ya sa za a dubi yadda al’adar kunya ta kasance jiya da kuma yadda ta sauya a yau, sakamakon cudanya da wasu bakin al’adu. Karanta: Illar rashin kunya ga al’umma

  Ma’anar kunya

  Wannan kalma ce da ke da mabambantar fassara daga mahangar masana al’adu. Kowane masanin da yadda ya dube ta, kuma ya ba ta ma’ana mafi dacewa da ita da haka ne:-

  Bunza, (2006:250) ya ce, “Kunya wata Magana ko wani aiki da ya saba wa tsarin kamun kai na al’ada, kuma al’ada ta zarge shi da muni na zubar da girma da mutunci. Da mai furta maganar ko aikata aikin da mai sauraronsa, ko mai kallonsa, duk suna shiga cikin hurumin wannan, jawabi a al’adance. Girma da mutunci mutun yakan zube idan Bahaushe ya fahinci bai nisantar daya daga cikin abubuwa da zai haddasa ire-iren wadannan abubuwan. Duk wani nauyin da al’ada za ta haddasa, ko wani kawaicin aikata wani aiki, ko fadar wata magana a wani wuri, ko a wasu wurare, ko a tsarin rukunin wasu jama’a na musamman duk ana sa shi aikin wannan ma’anar”

  Rabe-raben kunya

  Idan muka kula da ma’anar kunya da muka bayar, daga cikin ma’anar akwai abubuwan tsinta da za su iya zama rabe-raben kunya a idon Bahaushe. Bisa ga tsarin ma’anar kunya, Bunza (2006:261) ya kasa kunya zuwa gida kamar haka:

  1. Kunyar magana
  2. Kunyar aiki

  Kunyar magana

  Hausawa na cewa, wata magana surkuwar baki ce. Abin nufi a nan, ba kowace magana ake furtawa ba. Akwai maganar da mai fada da mai sauraro duk kowanensu zai ji kunya. Akwai wadda mai fada kawai zai ji kunya ba mai sauraro ba. Akwai wadda mai sauraro ne kawai zai ji kunya ba mai fada ba. Misali. 

  Maganar da miji zai yi da matarsa ta zamantakewa da more zaman aure idan dansu mai wayo ya ji su duka za su ji kunya. Fada da tsawar da miji zai yi wa mata na horo da hani, idan ?ansa ya ji yaron zai ji kunya ba uban ba. Idan mace na wasa da danta na fari idan wani ya girshe ta, ita za ta ji kunya ba wanda aka yi aikin gabansa ba. Maganganun da ke fita a baki a ji kunya suna da yawa. Daga cikinsu akwai, batsa da zagi na fitan albarka da makamantansu. Dubi: Matsayin kunya a rayuwar Bahaushe a yau

  Kunyar aiki

  Wasu ayyuka akan yi su gaban wasu mutane ba a ji kunya ba, amma idan aka yi su gaban wasu a ji kunya. Daga cikin ayyukan da ke haddasa kunya akwai:

  1. Iyaye su riski yaro na wasa da matarsa, ko yaro ya riski iyayensa na wasan miji da mata. A nan kowanensu zai ji kunya.
  2. Suruki ya riski surukinsa na wasa da matarsa, a nan kowanensu zai ji kunya.
  • Babba ya riski yaro na kwaikwayonsa kan wani abin ban dariya da ya yi. A nan yaron zai j i kunya.

  A idon Bahaushe wadannan su ne kashe-kashen kunya kuma kowanensu akwai abubuwan da ya kamata a lura da su kamar haka:

  1. Kunya da ake samu ta fuskar magana ba mai maganar kawai zai ji kunya ba. Kunyar in dai babba ce, to za ta mamaye bigere da dama, domin zata game abubuwa kamar haka:
  • Wanda ya furta maganar
  • Wanda ya ji maganar ana yin ta.
  • Wanda ya ji labarin maganar
  • Wanda ya kai labarin maganar
  • Wadanda suka shaida maganar
  1. Ta fuskar aikata aikin kunya kuwa, ba wanda ya aikata aikin kawai zai ji kunya ba. A wajen Bahaushe wa?anda kunyar za ta shafa sun hada da:
  • Wanda ya aikata aiki.
  • Wanda ya ga ana aikata shi.

  Matsayin kunya a al’adar Bahaushe

  Kunya al’ada ce da Bahaushe kan dauka da babban muhimmanci. Don haka kunya na cikin muhimman al’amura da suka shafi rayuwar Bahaushe ta kowane bangare. Bahaushe kan karfafa jin kunya da kuma guje wa abubuwa na jawo kunya cikin Addininsa, al’adarsa, adabi da sauransu harkokin rayuwarsa na yau da kullum. Bahaushe na da tasirin kunya cikin addininsa tun yana bamaguje kawo zuwa ga komawar sa Musulunci. Maguzanci addinine na Bahaushe (Bamaguje) da ya ha?a da bautar iskoki da wasu abubuwa da suka shafi tsafe-tsafe, koma bayan bautar Allah Ma?aukakin Sarki da kuma bin tafarki Manzannin Allah duk da cewa Bahaushe da ya kar?i Addinin Musulunci, addini ya yi tankade da rairaya da wasu al’adunsa ya zubar, amma al’adar kunya na tare da shi har yanzu.

  Har ilayau wasu ta’adodin al’adu da Addinin Musulunci ya dauke su munana kuma abin kyama, al’adar Bahaushe ya kyamace wanda ya aikata abin kunya na daga ciki. Misali: aikata zina na daya daga cikin abubuwan hani ga Musulunci to haka zalika a maguzanci kamar yadda Sudan (2015) ya ruwaito mana cikin bincikensa ga al’adun aure da haihuwan maguzawa. Al’adar maguzawan Gidan Bakwai (Kasar Faskari), idan za a kai amarya, dangin amarya sukan yi sihirce-sihircensu na kiran tsafi da suke bautawa. Sun nuna cewa, idan dangin amarya ‘yan magiro ne sukan kira shi ya yi wa amarya rakiya. Za a rika jin kuginsa a lokacin da ake tafiya kai amarya. Idan aka kira shi ya ki zuwa, wannan ya nuna amarya ba ta kai diyancinta ba. Rashin kai diyanci kuwa abin kunya ne, a cikin al’umma. Ya ishi uwa da ‘ya abin gori idan ana Magana. Da zarar haka ta faru, za a ga ba su shiga jama’a ana hira, gudun kar su samu sa?ani, da wasu su yi musu gori. (Sudan, 2015).

  Mai karatu dubi makala ta biyu don ganin wadanda kunya ta fi shafa cikin al’umma.

Comments

0 comments