Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Wadanda kunya ta fi shafa a cikin al’umma

Wadanda kunya ta fi shafa a cikin al’umma

 • In ana biye da mu a makalar da ta gabata mun yi tsokaci ne game da matsayin kunya a al'adar Bahaushe. To a wannan makalar za mu ci gaba ne akan inda muka tsaya game da wanna maudu'i namu na kunya. Bisa ga al’ada kunya ta shafi kowane Bahaushe. Amma, duk da haka, akwai wasu rukuni na mutane da kunya ta fi shafarsu a al’ummr Hausawa. Game da wannan kalma kuwa, masana sun kawo rukunin wa?annan mutane kamar haka:-

  Garba, R (2010) yana mai cewa “A al’adar Hausawa akwai ire-iren kunya wadda ake samu tsakanin mutane ko dai saboda nasaba ta jinni, ko auratayyako zamantakewa da dai sauransu”. Misali hakan ya ha?a da:-

  1. Kunya tsakanin saurayi da dudurwa
  2. Kunya tsakanin mata da miji
  3. Kunya tsakanin ?a da mahaifi
  4. Kunya tsakanin surukai.

  Bunza, A.M (2006:254), ya kawo rabe-raben rukukiunin mutane da kunya ta fi shafar su a al’ada kamar haka:

  1. Mutum da surkansa
  2. Mata da miji
  3. Babba da yaro
  4. Shugaba da mabiya
  5. Mutum da mutane

  Kunya tsakanin mutum da surkansa

  Alakar auratayyace ke haddasa surkuta acikin al’umma. Musamman ma ga bahaushiyar al’umma. Surkai kan iya kasance wa iyayen miji ko na mata ko mijin ‘ya ko matar ?a da sauran dangi da suka kasance iya-uwan iyaye, ko yayyin mata ko kuwa yayyin miji duk rukanin irin na wa?annan mutane da aka ussafta abokan kunya ne. iyayen miji naujinsu da kinyarsu da ake ji, ya fin a iyayen asali ga surka (mace) haka zalika ga surki. Ana girmamasu ne da kuma sakaya anbaton sunayensu. Wato sai dai akira su Baba (uban miji ko mata) mama ko Inna uwar miji ko mata da sauransu. Don haka surkai a kowance irin labara da akan gina, a jigon kunya ake aje su.

  Kunya tsakanin mata da miji

  Mata da miji mutane ne, da ala?a irin ta auratayya ke ha?a su, su kasance uba ga abin da za a haifa. Bunza (2006:256) ya nuna cewa, kunya da ke tsakanin mata da mijinta gabanin aure darajoji biyar gare ta kamar haka:-

  1. Idan aka tabbatar da an ba yaron ita aka yi baiko igiyar kunya daga ta tsinke saura hudu.
  2. Idan aka daura aure igiya daya ta tsinke saura uku.
  3. Idan aka kai ta gidan miji igiya daya ta tsike saura biyu
  4. Idan ta samu ciki ta haihu da shi igiya daya ta tsike saura daya.
  5. Daya da ta rage za a ci gaba da zama da ita iya rayuwa, ko da sun rabu, ko daya ya mutu ya bar ?aya igiyar, na nan ta kunya tsakanin mata da miji. Bunza, (2006:256).

  Har ilayau, mata a kodayaushe su masu mutunta mazajensu ne. ba gamutunta mazansu da mata ke yi, suna kuma jin kunyarsu, mafi yawan mata ba su Fadar sunayen mazansu. Irin wa?annan mata kan kira mazansu da “Malam” ko “Alhaji” ko “Shi”. Takance masa; “ba ya ji?” ko “Ina Magana ne” da sauransu. A da kuwa ko abinci ma, mata ba sukan ci a gaban mijinsu ba. Kuma da yawa idan mai gida na cikin gida mata ba sukan saki jiki su yi wasa da dariya ba (magaji 1999: 212). Karanta: Illar rashin kunya ga al’umma

  Kunya tsakanin babba da yaro

  Ga al’adar Bahaushe duk in da ya samu kan sa babba uba yake ga yaro, ko da ba wuri guda suka fito ba. Bisa ga dangantaka akwai kunya tsakanin wadda ko da yaushe babba kokarin kare maratabarsa yake don kar yaro ya raina shi. Kuma akasari babba gushewa aikata wani abu na zubar da girma, ko walakanta kai, kuma furta munanan kalamai yake a gaban yaro saboda idan har bai gujewa wadannan dabi’un ba, mutuncinsa da girmansa na uba ga da tsakaninsa da yaro duk za su zube. Kuma a fadin Bahaushe cewa ya yi, “Mutunci madara ce, idan ya zube yana da wuyan kwashewa”

  Kunya tsanin shugaba da mabiya

  Kunya tsakanin shugaba da mabiyansa iri guda ce da wadda ke tsakanin shugaba da mabiya ya fi nauyi wanan shugaba kan iya zamanto sarki ne, (shugaban sarauta) ko shugaban addini, ko shugaban sana’a da makamantansu. Irin wa?annan shugaba a kodayaushe, mabiyansa, masu biyayya ne da kuwa jin kunyarsu. Da kuma guje wa faruwar wata abin kunya daga gare su. Domin duk wata abin kunya ko mummunar abu da ta abku da shugaba yana iya sauka kan mabiyansa ya zamance abin goratawa. Hakan ya sa wasu sarakunan ?asar Hausa ke shan turare cikin abincinsu don gudun fidda da iska (tusa) a taro. Har ilayau shi ya sa sarki ba yawaita zama cikin talakawa (mabiyansa) don gudun aikata kowane abin kunya da kan iya kunyatar da masarautarsa.

  Kunya tsakanin mutum da mutum

  Akwai kunya tsakanin mutum da wani mutum gaba dayarta. Aikata abin kunya ko furta kalamai masu nauyi na kunya a gaban mutane da aka sani da wadanda ma ba a san su, duk kunya ce. Amma mafi nauyi shi ne aikatawa gaban wa?anda aka sani. Domin a dukkan lokaci za a rika kallon mai aikatawa da abun. Amma ga wadanda ba a san su ba, sai dai nauyi ga mace ta rika ratsa tsakanin maza tana wucewa ko da ba ta san su ba. Da kuma cin abinci idonsu ko fadin munanan kalamai da sauransu. Duk wadannan ababan kunya ne da kuma sabawa dokokin al’ada da addini.

  Mai karatu, dubi makala ta uku don ganin matsayin kunya a addini.

Comments

0 comments