Makalu

Sabbin Makalu

View All

Matsayin kunya a rayuwar Bahaushe a yau

 • Idan mai karatu na biye da mu a makalunmu na baya mun yi magana ne akan matsayin kunya a al'adar Bahaushe sannan daga bisani kuma muka gangaro muka duba asalin wadanda shi wanna al'adar tafi shafa a cikin al'umma. Yadda kunya ta kasance a rayuwar Bahaushe jiya, ba haka ta ci gaba da kasancewa a yau ba, domin kuwa ta samu ‘yan sauye-sauye, sakamakon mu’amalar wasu da wasu bakin kabilu da suka shigo kasar Hausa, suka mamaye. Manyan al’umma da suka fi tasiri a kan rayuwar Bahaushe su ne Larabawa da Turawa.

  Larabawa

  Larabawa da suka shigo kasar Hausa, sun kawo Addinin Musulunci, wanda ya fidda rayuwar Bahaushe daga duhun kai na Addinin Maguzanci zuwa haske na Addinin Musulunci. Don haka akidun Balarabiyar al’ada wacce ta dogara kacokan kan koyar alkur’ani da sunnah ta yi tasiri a rayuwar Bahaushe. Akwai al’adun Bahaushe da aka watsar saboda sun saba wa ka’ida, akwai kuma wadanda aka cigaba da runguma sabo da sun dace da ka’ida. Cikin wadanda aka cigaba da rungumar “kunya” na ciki. Dalili kuwa yana cikin koyarwar Alkur’ani da Hadisi kamar yadda ayoyi suka tabbatar da hakan a baya. Don haka mu’amalar Bahaushe da Balarabe kyawawan sauyi aka samu cikin rayuwar Hausa.

  Kunya a Addinin Musulunci

  Addinin Musulunci shi ne addinin Bahaushe ya karba bayan fita daga duhun kai (Maguzanci) Musulunci ya yi tasiri sosai kan rayuwar Bahaushe wajen jaddada nasa bin umurni da hani na Allah (SWT) da kuma bin tafarki Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, (SAW). Kunya abu ne mai Muhimmanci da matsayi a Musulunci. Wannan ya tabbata ne cikin wasu ayoyin kur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) kamar haka:

              Allah madaukakin sarki ya ce

  “Lalle wannan yana cutar da Annabi, to yana jin kunyarku alhali kuwa Allah ba ya jin kunya da gaskiya…” (kur’ani 33:53) (Fassara Gumi)

  Haka kuma cikin alkur’ani mai girma, an kawo kissar Annabi Musa, wajen da taimaka wa ‘ya’yan Annabi Shu’aibu shayar da dabbobinsu. Saboda wannan taimakawar ne mahaifinsu ya umurce su, da su kirawo ya zo, zuwa gare shi. Allah (SWT) ya ce

  “Sai dayansu ta je masa tana tafiya a kan jin kunya, ta ce “Ubana yana kiran ka, domin ya saka maka ijarar abin da ka shayar, saboda mu” ......... (kur’ani 28:25) (Fassarar Gumi)

  Wadannan duk ayoyi ne da ke jaddada “kunya” cikin Alkur’ani Mai Girma. Hakazalika Hadisan Manzon Allah ma, sun jaddada muhimmanci da matsayin ‘kunya’ a Addinin Musulunci kamar yadda cikin hadisi an ce:

  “Daga Abu Sa’idul Khudri, Allah ya kara masa yarda yace “Manzon Allah (SAW) ya fi kowa jin kunya, mukan gane abin da ba ya so ne ta fuskar sa”.

                                                                                                              (Muslim ya ruwaito)

  Haku kuma wani ruwaya ta Bukhari an ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce

  “kunya daga cikin imani ne shi kuma imani daga cikin aljannace” (Bukhari ne ya Ruwaito)  

  A wata ruwaya kuma an ce

  “Manzon Allah (SAW) ya ce “kunya da imani an hada su wuri guda idan aka dauke dayan to shi ma dayan zai tafi”

  (Muslim ne ya ruwaito)

  An kuma kara fadin Manzon Allah (SAW) yana cewa

  “lallai kunya da imani akida ne na Musulmi”

  (Minhajul Muslim)

  Dukkanin wadannan ayoyin Alkur’ani da Haidisai jaddada matsayi da Muhimmancin kunya ne suke yi cikin Addinin Musulunci.

  Turawa

  Kamar yadda zuwan Balarabe kasar Hausa ya kawo tasiri ga rayuwar Bahaushe, haka zuwan turawa. Duk da cewa zuwan Bature ya kawo tasiri ga rayuwar Bahaushe ta samar da wasu kayayyakin more rayuwa da, da can baya bai san su ba, amma kuma sun kawo tarnaki ga wasu al’adun Hausawa, wadanda daga cikin su akwai “Kunya”.

  Zuwan Turawa kasar Hausa, ya sa Bahaushe na daukar wasu al’adunsa, a matsayin rashin wayewar kai musamman masu ilimin boko. Don haka za a taras daidaiku ne daga cikin mata a yau ke iya kinayar sunayen mazajensu. Hakazalika boye sunan dan farko ma ana daukarsa rashin wayewa don haka yawancin mata na kiran ‘ya’yan fari da sunayensu. Haka kuma ‘yan matan zamani kan furta wasu kalamai da be kamata ba musamman a cikin fina-finai amma kunya ba ta kama su. Raye-raye tsakanin maza da mata duk abubuwa ne na kunya amma a yau ya zama ruwan dare a al’umma. Don haka al’ada da addini ba su amince da rashin kunya, kuma duk mara kunya ana daukarsa ne a matsayin mutumin banza. Kuma duk abin da ya yi ba zai zamo abin mamaki ba. A fadin wani hadisi Manzon Allah Tsira da amince Allah su tabbata a gare shi na cewa

  “Yana daga cikin abin da mutane suka riska daga kalaman Annabawan farko, idan ba ka da kunya, ka yi abin da ka ga dama”

  Mai karatu na iya duba ci gaban wannan tattaunawa akan al'adar kunya a makala ta gaba, inda za mu yi dubi ga illar rashi kunya a wajen al'umma

Comments

0 comments