Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Allah daya gari bambam: Labarin al'ajabi na wani malami

Allah daya gari bambam: Labarin al'ajabi na wani malami

 • A wani gari an yi wani shahararren malami mai ba da karatun littattafai na addini. Allah ya yi wa wannan malami baiwa matuka, ilminsa ya kai matsayin duk yankinsu ba wanda bai san ilminsa ba.

  Wata rana wannan malamin bayan ya ba da darasu gaf da sallar magriba, a cikin karatun da suka yi na wannan ranar yake ba wa almajiransa wani labarin cewa, cikin ikon Allah, Allah zai iya shafe wannan duniya da abin da ke cikinta, cikin kifta ido da budewa, sannan ya kagi wasu halittu da ba mu ne ba. Kamar yadda wannan aya take cewa 'INNAMA AMRUHU IZA ARADA SHAI’AN AN YAKULA LAHU KUN, FAYAKUN.' Dubi labarin wata budurwa abin al'ajabi a rayuwa bai karewa

  To gaba daya almajiran sai suka yadda, shi kuma malamin sai ya sa wasiwasi a cikin zuciyarsa. Bayan sun gama lokacin sallah ya yi sai malam ya shiga gida don ya taba ruwa ya yi alwala ya fito sallah, lokacin da ya dauki buta ya bar matarsa tana yin rude/talge na tuwo. Shigansa bayan gida, ya tsuguna kenan sai duhu ya rufe shi, bayan yayewar duhun sai ya tsinci kan shi a wata duniya ta daban, malam bai san ina ne wurin ba, juyawarsa sai ya hangi wata bishiya mai inuwa ya je ya yi zamansa a gun. Malam na wurin har yamma, da dare ya yi sai ya koma kofar wani gida kusa da inda bishiyar take ya kwana.

  Bayan kwanaki sai mutanen garin suka fahimci cewa wannan fa malami ne, sai suka rika zuwa wurinsa suna daukan karatu. To kofar gidan da malam yake zama suke karatu maigidan ya rasu, bayan matan gidan ta gama takaba sai almajiran malam suka ce to malam ya kamata fa a daura muku aure da wannan matar kai ma ka koma cikin gida da zaman da kake yi a nan. Malam bai ki ba, sai aka daura musu aure malam ya tare ya koma cikin gida. Shekara na zagowa sai malam ya samu karuwa da da namiji. A wannan zaman dai malam suka haifi 'ya'ya biyu da matan wanda ya kai shekaru goma (10) har yara sun girma. Dubi wannan labari na dolaki karambana

  Wata rana kawai sai ga malam na kuka, sai matar ta tambaye shi me ya same ka ke ke kuka kuma? Sai malam ya kwashe labarin duk lamarin da ya same shi har ya tsinci kan sa a garin. Sai matar ta ce Allah sarki, to mu je gurin ka nuna min, da suka je sai ta ce to mu yi addu’a ko Allah zai maida kai inda ka fito, amma kafin nan, ka ride wannan yaro a hannunka, sai ta ba shi dansa na farko kamar an tsaga kara da malam. Sai malam ya rufe ido suka yi addu’a kawai sai ga duhu ya sake rufe su lokacin da haske ya bayyana sai ga malam a cikin bayan gidansa da yaro a hanu. Yana fitowa ya ji ladan (mai kiran sallah) bai kammala ba, ya samu matarsa da take rude tana gindin murhu bata tashi a wurin ba. Mamaki ya damu malam. Yaro daga zuwan shi ya kama wasa kaman da ma a gidan yake, to kuma kowa ya san malam bai taba haihuwa. Daga nan malam ya yi alwala ya fita masallaci suka yi sallah, sai bayan an idar da sallah yake tambaya shin shigansa gidan nan ya jima ne? suka ce a’a malam ba yanzu ka shiga ba?

  Al’amari ya ya sake damun malam, rannan yana karatu da almajiransa sai wani almajiri daga ciki ya ce malam da ma kana da yaro (da) ne gashi kun yi kama kuma ba mu san shi ba? Nan ne fa malam ya kwashe duk abin da ya faru da shi a wata duniya ya gaya musu. Ya ce in kun tuna shekaru goma kenan rabon mu daku ko sai suka ce a’a malam ai kullum muna tare. Sai ya yi shiru ya ce “to akwai lokacin da na baku labari cikin karatunmu cewa, Allah zai iya shafe wannan duniya da abin da ke cikinta, cikin kifta ido da budewa, sannan ya kagi wasu halittu da ba mu ne ba, suka ce “eh ka fada kuma shekaran jiya ne” sai ya ce “to ni na yi shakku ne cikin wannan lamarin shi ne Allah ya nuna min kamar yadda na baku labarin abin da ya faru da ni din. kowa mamaki ya kama shi. Daga nan kowa ya fahimci malam, yaro kuma ya zama dan malam. Da ganin haka malam ya ce tab wannan shi ne "Allah daya gari bambam." 

  Mai karatu na iya duba wannan makala da ta yi magana akan adabin Hausa, makalar ita ce, labaran tarihihi daga cikin azuzuwan adabin gargajiya

Comments

0 comments