Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Illolin amfani da magungunan mata ga mace

Illolin amfani da magungunan mata ga mace

 • Da yawa daga cikin mata musamman ma na Hausawanmu na yau, sun du?ufa wajen amfani da wasu sinadarai don ?ara wa 'ya'yansu mata ni’ima wajen gamsar da mazajensu. To ha?i?a, ba zai iya zama laifi in an yi ba, sai dai matsaloli da illa da yake haifarwa bayan an yi amfani da shi ya fi muhimmancinsa yawa musamman ga mace budurwa da ba ta ta?a auren fari ba. 

  Mata da yawa daga cikin iyaye, sun ma ?auki wannan hanyar a matsayin sana’a ta neman abin dogaro da kai, sukan kai tallar irin wa?annan magunguna gidajen mata musamman inda ake biki don tallata hajarsu.

  Kuna iya karanta: Tsangwama da mata ke sha wurin mazaje a shafukan sada zumunta

  Da zarar an ce mace an sa ranar aurenta, to iyaye da kuma ‘yan matan kansu, za su fara zuwa neman taimakon magungunan. Akan ?auki tsawon lokaci ana ha?a mace, maimakon a bar ta ta tafiyar da kanta a kan irin tsarin da Allah Ya tsara mata da irin wa?annan gamje-gamjen magungunan da ba su da asali wanda nan gaba za a samu rikirkicewar sha’awa domin yamutsa ta ?in da aka yi da wa?annan sinadarai. Daga cikin ire-iren wa?annan sinadarai akwai:

  • Na sha da madara ko a shayi
  • Na dafawa da kaji
  • Na ci da nama
  • Na ci da baru
  • Na mannawa

  Illolin da maganin ke haifarwa

  Gusar da ni’imar mace na asali da take da shi:

  Duk macen duniya, akwai ni’imar da Allah ya mata wajen gamsar da namiji, amma irin ni’ima da mata ke ?arawa kafin su yi aure na haifar masu da illa wajen gusar da ni’imar da suke da shi na asali. Domin da zarar wannan ha?in magunguna da suka yi ya gushe, to ni’imarta na asali da take da shi ne zai dawo, amma kuma ba lallai ne miji ya gamsu da ita ba. Domin wanda aka yi kafin auren da ma ba mai ?orewa ba ne kuma babu shi.

  Cire wa miji sha’awar matarsa

  Da zarar wannan ha?in magunguna da aka yi wa mace kafin ta shiga gidan mijinta ya gushe, to ni’imarta zai ragu da kashi 80% sai na asali da take da shi ya dawo, shi kuma miji ba zai ta?a jin tana gamsar da shi kamar da ba. Daganan sha’awa da yake mata zai fara raguwa, idan aka yi rashin sa'a sai ma ya haifar masa da sha’awan wasu mata a waje.

  Shawarwari

  A matsayin mace budurwa da ba ta ta?a aure ba, to ki guji duk wasu kayan da za su sanya miki ni’ima in kin sha, domin tun asali irin wadannan magunguna an yi su ne don matan da suka ?an jima cikin aure kuma zuumar sha’awarsu ta ?an fara sanyi.

  Amma a matsayinki na budurwa kina iya shan ‘ya’yan itatuwa da yawa gab da bikin naki, inda hali ma, kina iya daina cin duk wani abinci illa ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki ka?ai kamar ana sauran sati ?aya bikin naki.

  Haka ma magungunan Musulunci da aka samu ingancin warakarsu daga Manzon Allah SAW, irin su zuma, habbatus sauda, zaitun da sauransu. Wa?annan za su warkar da duk wani rauni ko cikas da ?ila mace ke da shi a lafiyar jiki da ta ruhi gaba ?aya wajen sanya ni’ima. Mai karatu na iya duba wannan makala da ke bawa mata shawara cewa, ba boka ba malam mallaki mijinki cikin sauki

  Ubangiji ya kare mana lafiyarmu baki ?aya.

Comments

1 comment