Makalu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Tasirin camfe-camfen Hausawa cikin tarbiyyarsu (Na daya)

Tasirin camfe-camfen Hausawa cikin tarbiyyarsu (Na daya)

 • Gabatarwa

  Duk da kasancewar camfi mummunar al’ada ce amma suna tattare da wasu hikimomi da za a iya karuwa da su, ko da yake ba za su halatta amincewa da camfi ba. Idan aka dubi camfe-camfen Hausawa za a iya kutsa kai a lalubo wasu isharori da suka yi na kyautata rayuwa da suka danganci tarbiya, da koyar da dabi’u, da bunkasa tunani, da fadakarwa, da tunatarwa, da tsoratarwa, da nuni kan dogaro da kai. Sannan kuma camfi kan hana mutane aikata abubuwan ki da neman a guje musu. Wato ke nan a wata fuskar camfi dai wani kuduri ne na tarbiya, da horo, da hani, da kuma bunkasa tunani, da fadakarwa. Cikin wannan makala zan yi dubi ga kadan daga cikin ire-iren tasirin da camfi ya yi cikin tarbiyar Hausawa. Dubi rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo

  Ma’anar Camfi

  Akwai dirdado da yawa dangane da ma’anar wannan kalma ta “camfi”, wannan ma shi ne ya sanya, na dora hannuna kan wadannan ra’ayoyi na masana.

  Bunza (2006:58). Cewa ya yi "Camfi wata dadaddiyar al’ada ce da Hausawa suka tarar tun kaka da kakanni. Kuma masana da manazarta Hausa sukan yi wa camfi kallo ta fuskoki biyu, wasu na kallon camfi, al’ada ce kawai kamar irin kowace al’ada; a ganin wasu kuwa, abin ya wuce haka, ya kai matsayin addini daga cikin addinin gargajiyar Bahaushe”.

  El-shamy (1976) ya ce “Camfi yarda ne ko amincewa, ko yin imani da wani abu a matsayin an gaskata shi tare da abubuwan da ya kunsa”.

  Scott (1976) shi kuma cewa ya yi “Camfi shi ne, yarda ko amincewa da wani abu, ko aiwatar da wani abu, da aka gada, kaka da kakanni cikin duhun jahilci, saboda tsoro, ko nuna fargaba da abin da ba a amince da shi ba”.

  Dangambo (1984:38) ya ce “camfi shi ne mutum ya dauka cewa, in ya yi wani abu, ko ya ce wani abu, ko ya ji wani abu, to ya gaskanta wani abu zai faru, sakamakon haka”.

  Ma’anar Tarbiyya

  Yahya da wasu (1992:68). Tarbiyya wata hanya ce ta kyautata rayuwar dan-Adam da shiryar da shi ya zuwa ga halaye da dabi’u masu kyau, masu nagarta. Idan dan-Adam zai tashi da kima da mutunci da kwarjini da ganin kimar abokan zamansa, sannan zai dinga bai wa kowa hakkinsa daidai yadda ya kamata gwargwadon iyawa da hali, to za'a iya cewa yana da tarbiyya. Tarbiyya ta hada renon jikin mutum da ransa da abubuwa kyawawa masu sa kamala. Dubi illar kai yara aikatau don neman kudi

  Kamusun Hausa (2006:428) ya anbaci tarbiyya da cewa reno ne da ake yi wa yara domin tashi da halaye nagari su kuma kyamace munanan dabi’u.

  Funtuwa (1983:63) ya bayyana tarbiyya da cewa “Horo ne da iyaye ko manya nagaba ke yi wa yara don su tashi da halayen kirki. Duk yaron da ya tashi babu tarbiya, rayuwarsa na iya zama mai rauni ce, kuma ana koyon tarbiyya ne ta hanyoyi kamar fada da kwaba da hani da umarni da kwadaitarwa da duka sannan da sanya yara a makaranta don samun ilimi da halaye nagari”.

  Misalan camfi masu nuna tarbiyya

  Misalan da za su zo kadan ne daga cikin tasirin da camfi ya yi a tarbiyar Bahaushe.

  Camfi masu Hani/gargadi

  1. Idan aka doki maciji da karan rama, za a ga kafafunsa, amma za a mutu.
   2. Idan yaro na cin kwai zai yi sata.
   3. Cin kan kifi na sa dushewar basira.
   3. Idan mace mai ciki ta tsallake rafi to za ta yi bari.
   4. Ketarar wando na sa mata yawan mafarki
   5. Kallon majigi ga mai ciki, kan sa a haifi yaro mahaukaci.
   6. Yin shara da dare na kawo tsiya (talauci)
   7. Idan mace mai ciki ta debi ruwa a rafi da daddare aljanu za su musanya danta da nasu. Da sauransu.

  Idan aka dubi wadannan misalan za a ga cewa camfin ya nuna tarbiya ga mata ko mutane inda yake hani ga barin wasu abubuwa da sauransu.

  A makala ta gaba za mu kawo misalan tasirin camfi cikin rigafi da kiwon lafiya, da nuni ga addini da sauransu. Sannan mai karatu na iya duba yadda wakokin yara ke gina tunanin rayuwar al'ummar Hausawa

Comments

1 comment