Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Al'adar haihuwa a kasar Hausa

Al'adar haihuwa a kasar Hausa

 • Al'adar haihuwa a kasar Hausa

  “Haihuwa maganin mutuwa, ba don ke ba da iri ya kare!" Wannan shi ne kirari da ake wa haihuwa. Kuma sukan kara da cewa, “Kyan gida da magaji!” kirarin haihuwa kirari ne na karuwa. Ma’anar haihuwa ita ce, yayin da miji da mata suka sami karuwa da samun da ko ‘ya. Ma somin haihuwa kuwa shi ne, lokacin da mace ta samu juna biyu, wato ta sami ciki, bayan an tabbatar da igiyar aure tsakaninta da mijinta. karshen haihuwa kuwa shi ne yayin da jariri ya fito daga cikin uwarsa ta hanyar al’ada. Tun daga wannan lokacin ne iyaye za su shiga tattalin abin da suka samu, har sai ya girma ya kai munzalin mutane, wato ya kama kansa. Dubi tasirin zamananci kan sutura da abincin Hausawa

  Neman taimako

  Da zarar mace ta samu ciki (juna-biyu) sai iyayenta ko masu lura da ita su dukufa wajen neman taimako don ta sauka lafiya. Akan kuma kafa mata dokokin da zata kiyaye, kamar kada ta rika cin abinci, ko abin sha mai zaki, kamar zuma da sukari ko rake ko muzarkwaila ko alawa, saboda saukin nauyin fitowa abin haihuwa wanda yake faruwa da ciwon zaki. To, kuma akan umurce ta da ta rika shan magani a kai a kai, kamar sabara da bauri. Da kuma wasu tadodi na mai ciki kamar rashin fita da dare ba tare da wani makami ba, kamar wuka ko lauje ko kan makoki ko mashinjiri ko dagi, saboda shu’umi da aljani.

  Goyon ciki

  Wannan shi ne yarinya ta tafi gidan iyayenta don ta haihu, amma idan haihuwar ta farko ce, saboda a taimake ta, a kuula da ita sosai da sosai, don gudun hadari da barkwanci wajen haihuwa, da rashin iya yin wankan biki kamar yadda ya dace. Dubi matsayin maganin gargajiya a wurin Bahaushe

  Nakuda

  Anan in an ga alamar cewa haihuwa ta kusa, sai a shiga neman maganin saukin guiwa, kamar shan rubutu da jike-jike. Sai a aika a kirawo wata mace, watau arbiki ko ungozoma, don ta kula da mai haihuwa. Kuma in ta sauka lafiya a kula da abin da aka Haifa. Kuma ta yanke cibiya, ta binne uwa, watau mahaifa. Kuma ba za a ba da sanarwar haihuwa, sai in an ga faduwarta, kana arbiki ko ungozoma ta kan ce “ Alhamdu Lillahi, barka da arziki!” da sauran maganganu ko addu’o’i da a kan yi bayan mahaifar ta fadi.

  Guda

  Akan yi guda sau uku (3) idan na miji aka samu. Idan mace ce kuma guda hudu (4) wannan guda tamfar shela ce, cewa ga irin abin da aka Haifa.

  Lugude

  Sai a kama yin lugude don a sanar wa makwabta an sauka. Na nesa kuma a aika musu da manzo takanas. Lugude daka ne da akan yi shi cikin raha, ana yi ana guda kada turmi, da kwarya , da sauransu. Akan taru a yi gayya wajen dakan luguden. Baicin sanarwa ana kuma yin maganar boye ta hanyar lugude. Masu lugude suna iya yi wa makwabta ba’a ko zambo ko wani abu makamancin haka. Su kuma idan sun gane, sai su girka nasu luguden, don su mayar da martini.

  Wankan biki

  Wannan wani irin wanka ne na tilas da yarinya take yi ko ake yi mata, da cewa ta sauka lafiya, wannan wanka ana yin sa ne da tafasasshen ruwa mai zafin gaske, tare da ganyen runhu ko sabara ko kuma darbejiya, saboda maganin sammatsin ciwon sanyin Haihuwa, wanda ya kan sukukuce yarinya ya kuma gadar da kurumta da sumkwita da susuta. Wani lokaci ma yakan aukar da barna fiye da haka. Yarinya dai takan yi wankan sau biyu a yini safe da maraice, tun daga ranar Haihuwa har ta yi kwana arba’in (40) sa’anan ta mayar da shi sau daya a yini da safe kawai ko da maraice. Har ma ta bari sam idan aka amince da cewa wata cuta ta sanyi ba za ta bijiro mata ba faufau. Wannan wankan muhimmi ne kuma wajibi ne ga duk mai Haihuwa. Domin sau da yawa idan har aka kuskure, ba a yi shi da kyau ba, ko ma ba a yi shi bas am-sam-sam duk cutar da ta same ta sai a danganta da rashinsa. Har an masa kirari ana cewa:

  • wankan biki maganin sumbwita.
  • Yarinya daure ki yi shi ki huta.
  • In kin kuskure shi sai buzunki!

  Kunun biki

  Wannan wani irin nau’in kunu ne wanda ake dafa shi kana a sanya mi shi kanwa da kayan yaji citta da masoro da kanamfari da ka-ji-ji domin mai biki ta sha watau, ‘kunun kanwa’ tun daga ranar da ta haihu sannan a ci gaba da ba ta maganin kaikayin nono da sauran irin su.

  Kayan barka

  Wannan kaya ne da miji ke kaiwa bayan an haihu da kwan uku (3) na barka da Haihuwa, wadanda suka kunshi kayan yaji da hatsi da ita ce da man fitila da kayan yaji da kayan jinjiri da na mai Haihuwa da kudin sayen nama.

  Kauri

  Sayen ganda ko langabu na sa ko na tunkiya, ko Ma a yanka tumkiya, ko dan bunsuru, ga mai hali, wannan shi ake kira kauri. Daga nan sai a rarraba shi ga ‘yan’uwa da abokan arziki, musamman ma wadanda ba a kai musu kunun biki ba. 

  Wannan a takaice ke nan game da al'adan da ke tattare da haihuwa a cikin al'umman Hausawa. Mai karatu na iya duba kitson Hausawa na gargajiya da na zamani.

Comments

0 comments