Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Tarihin al'adar sa rawani wurin Buzu

Tarihin al'adar sa rawani wurin Buzu

 • Al’ada ita ce hanyar da mutane suke bi donmin tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum, kuma hanya ce ta tayuwa wadda al’umma suka saba da ita ta kuma kasance karbabbiya. Samuwar al'ada na biyo bayan dalilai da dama. A cikin wannan makala zan yi bayanin yadda al'adar sa rawani ya samu ga al'umar Buzaye wanda ya zama wani muhimmin abu kuma alamu da kowa ke gane su. Dubi dangantakar Hausawa da wasu kabilu a cikin gida Nijeriya

  A rayuwa ta duniya, duk lokacin da mutum ya tsinci kansa a wata matsala ta rayuwa, kokarinsa a kullum shi ne ya sama wa wannan matsalar magani ko mafita a gare shi. A kokarin samun wannan mafitar in har ya yi dace, wato ya samu nasara a kan abin da yake damunsan nan, to fa zai riki wannan hanyar hannu bibbiyu, kuma daga karshe in ya saba yi sai ta koma masa al’adarsa. Da wannan ne masu iya magana ke cewa “Sabo turken wawa, Sabo jini ba ya sauyawa, Kowa ya saba da kai gida ba ya fasawa, Hannu ya iya jiki ya saba (Bunza, 2006).

  Irin wannan misali shi ya kai ga Buzaye suna sanya rawani.

  Kamar dai yadda ya zo a bisa da cewa, su Buzaye mutane ne da aka san su da zama a kasar Nijar da wasu sassan kasashen da ke kewaye da kasarsu ta asali. Ita kuma kasar Nijar kasa ce ta sahara, wanda take da yawan fili, babu itatuwa ko tsaunuka ko kuma tuddai. Wannan yanayi nata ya sanya iska ya yawaita a wadannan wuraren da Buzaye ke zama, kuma duk lokacin da wannan iskar ta busa ta kan zo ne tare da kasa da kura masu yawa, wanda wannan kuran kan shiga wurare masu muhimmancin a sassan jikin wadannan mutanen da ke zaune a wannan saharar, wuraren kamar: hanci, da baki, da idanu, da kunne.

  Ganin irin wannan illar ne ya sanya Buzu nema wa kansa mafita don kare kansa. Sai ya ga babu abin da zai yi illa ya nemi abin da zai tare wadannan wuraren, sai ya ga cewa rawani ne kawai zai yi amfani da shi wajen kewaye dukkan sassan nan. D aya yi hakan kuma sai ya ga ya samu kariya ainun. Shi ke nan shi kuma sai ya dauki wannan hanya a matsayin kariya, kuma ya saba da wannan, ga shi kuma Buzu mutum ne da ke son ado da bakin tufafi. Da haka ne wannan sabon ya zame masa al’adarsa, kuma har abada in ka ga Buzu za ka same shi da nadin rawani komin wuya komin zafi. Saboda haka rawani ya zamo wa Buzu al’adarsa babu babba ba yaro ko namiji ne ko mace ce.

  Wannan shi ne dalilin samuwar rawani a wurin Buzu. Da hake ne ma Hausawa suke da wani karin magana da ke cewa “sai mun ga abin da ya ture wa Buzu nadi. Dubi gudumawar harshen Hausa a matsayin harshen uwa

Comments

0 comments