Makalu

Ire-iren auren Hausawa

 • Aure a kasar Hausa ya kasu kashi-kashi kamar haka:

  • Aren soyayya
  • Auren Dole (Tilas)
  • Auren Zumunta (Dangi)
  • Auren sadaka
  • Auren ɗiban wuta
  • Auren jingina sanda
  • Auren gayya
  • Auren ɗiban haushi

   Auren soyayya

  Wannan aure ne wanda yaro yake ganin yarinya ya ce yana son ta da aure ita kuma idan ta amince iyayen ma sun yarda da maganar sai a yi haramar sa ranar wannan auren. Dubi aure a lokacin maguzawa

  Auren dole (tilas)

  Musulunci ya shardanta cewa auren ‘ya mace budurwa, haƙƙin uba ne ya zaɓa mata mijin da zata aura, ba tare da sanin ‘yar ko uwar ‘yar ba. A ƙasar Hausa wannnan ya zama ɗabi'a ce tasu wadda auren fari bat a da zaɓi. Hakan kuma ta sanya wasu iyayen kan sanya wannan ikon har aurensu na biyu ko ma fiye. Amma wasu kuwa sukan bar mace ta zaɓi wanda take so bayan sun fahinci cewa zaɓinsu na farko bai yi ba.

  Wannan aure ɗayan biyu ko dai yaro ya ga yarinya yana son ta da aure ita kuma bata so. Iyayen ta kuma su zartar da wannan aure watau ko suna so ko sun ki. Har ma akan bawa yarinya ga wanda yake saan mahaifinta amma kuma ba ta so.

  Auren zumunta ko auren dangi

  Wannan aure ne wanda aka nema wa yaro ko yarinya daga cikin dangin uwa ko na uba ba tare da neman shawaran yaro ko rarinya ba irin wannan aure ana yin sa ne don ƙara danƙon zumunci tsakanin yanuwa.

  Auren sadaka

  Shi kuma wannan aure ne da ake baiwa yarinya ga wani saboda neman tubarraki kamar irin sadakar da ake ba wa malamai, almajirai musamman idan yarinyar ta girma ba ta samu ma nemi da wuri ba ana kuma yin auren sadaka don gudun kar a jawo ma iyayen ta abin kunya wani lokaci kuma idan mutum bai sami haihuwa da wuri ba ya kan yi alkawari cewa zai ba da ita sadaka in ya samu.

  Auren diban wuta (kisan bakin wuta)

  Wannan aure ne da ake yin shi in an sake mata saki uku alhali kuwa matan tana son mijin ta shi ma yana son ta dole sai ta aure wani mutum in sun rabu kafin ta samu daman komawa gidan mijinta na farko. To auren nan da ta yi, da ƙudurin cewa za ta dawo wurin mijin ta na da wannan shi ne auren ɗiban wuta.

  Auren jingina sanda

  Wannan shi ne auren da mutum zai auri mata amma kuma tana Zaune a gidan ta. Sai ya kasance baza ta iya tasowa tazo gidansa ta zauna ba saboda waɗansu dalilai. Haka shi ma bazai iya zuwa gidan ta ya zauna ba sai dai yaringa zuwa yana kwana idan ya je gidan sai ya dangana sardarsa idan ya tashi dawowa sai ya ɗauki kayarsa a kofan ɗakinta.

  Auren gayya

  Wannan ma aure ne wanda idan matan mutum ta fita, alhalin kuwa yana sonta ya dai sake ta ne kawai don ta addabe shi, to maza sai ya yi sauri ya yi wani aure kafin ya sake ta ko kafin ta gama idda ba don kome ba kuwa zai yi wannan auren ba sai dai kawai don ya huce haushin sa ko kuma don matan kada ta riga shi yin aure.

  Auren diban haushi

  Ana ƙiransa auren ɗiban takaici ko na kece raini. Idan matar mutum ta dame shi da fitina yakan tashi takanas yaje ya aure wata mace mai kyau ko mai dukiya ko mai asali ko mai addini fiye da wadda take gidan sa ko wadda ya saka domin ya maida haushi da takaici.

  Ku danna nan don karanta yadda ake aure a kasar Hausa daki-daki.

  Hakkin Mallakar Hoto (Photo Credit): Sugar Weddings

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

  Posted Fri at 4:38 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wan...

 • Yadda ake hada spring chin-chin

  Posted Thu at 10:16 AM

  Assalamu Alaikum. Barkan mu da warhaka. Ayau na sake zuwa mana da sabuwar makala ta girke-girke wacce ciki za mu koyi yadda ake soya spring chin-chin. Abubuwan hadawa Flour (4 cups) Baking powder (1 teaspoon) Butter (125grms) Mangyada Gishiri (1 teaspoon) Ya...

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

View All