Makalu

Nazarin waƙoƙin baka: Muhammadu Ɗan'anace a waƙar Garba Nagoɗi

 • Gabatarwa

  Kiɗa da waƙa a ƙasar Hausa wani ginshiƙin abu ne da ake aiwatarwa don ilmantarwa ko sadarwa ko nishaɗantarwa ko bayar da gudummuwa ta musamman, (Gusau, 2005). Don fahimtar wannan hanya ta isar da saƙo a sauƙaƙe. Wannan aiki zai yi nazarin waƙar “Garba Nagoɗi” ne na Muhammad Bawa da aka fi sani da Ɗan'anace.

  Ko mece ce waka?

  Masana da dama sun ba da ra’ayoyinsu a kan ma’anar waƙa. A ra’ayin Yahaya (1997), a iya cewa waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomi da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum ba. Waƙa saƙo ne da ake gina shi kan tsararriyar ƙa’ida da baiti, ɗango, rerawa, kari, amsa-amo da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, (Ɗangambo, 2008).

  Kenan, waƙa saƙo ne cikin furuci da lafazi wanda ake gabatar da shi ta hanyar daidaitattun kalmomi waɗanda ake rerawa cikin kalmomi masu tsari da kuma ƙa’ida da sauran dabaru masu jawo hankali (Mukhtar, 2006). Idan muka lura, duk a ma’anonin da masana suka ba ‘waƙa’, kalmar saƙo ta fito. A taƙaice a iya cewa waƙa salo ne na isar da saƙonni cikin raha da annashuwa, wanda ake rerawa ko dai ta hanyar amfani da kayan kiɗa domin ƙara wa saƙon armashi ko kuma rerawa ba tare da ƙiɗa ko kayan bushe-bushe ba. Waƙa ta ƙunshi wani babban rukuni na adabin al’umma, domin hanya ce ta jawo hankalin jama’a maza da mata, babba da yaro.

  Waƙa ta bambanta daga taɗi na yau da kullum. Aba ce wadda ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna ƙwarewar harshe. Harshen waƙa a bisa kansa cikakke ne duk da yakan kaucewa wasu ƙa’idojin Nahawu, (Gusau, 2005). Waƙa ba kamar zube take a shimfiɗe ba, tana zuwa ne gunduwa-gunduwa da siffar baitoci.

  Kamar yadda adabi ya kasu zuwa kashi biyu, na gargajiya da na zamani, waƙa ma ta kasu kashi biyu, rubutacciya da ta baka. Waƙar ‘Garba nagodi’ na Muhammadu Bawa Ɗan Anace ta faɗa cikin waƙoƙin baka. Dubi tarihin wakokin baka na Hausa da wanzuwarsu

  Waƙar baka zance ne sarrafaffe, aunanne wanda ake aiwatar da shi ta bin hawa da saukar murya. Waƙar baka, ita ce ake rerawa da fatar baki, kai tsaye ba tare da an rubuta ta ba, ana rera waƙar baka haka kawai ko kuma da kiɗa. Rubutacciyar waƙa kuwa tsara ta ake yi a rubuce, sa’an nan a rera ta a zamanance kuma akan rera ta da kiɗa.

  To tun fil azal gargajiya ita ta haifi waƙa da mawaƙan Hausa. Su kuma mawaƙan su suke raya al’adun gargajiya. Har ila yau ana amfani da waƙa wajen haɓaka al’adu ta hanyar faɗakarwa da nishaɗantarwa. Saboda haka, dangane da wannan aiki, zan yi nazarin waƙar Garba Nagoɗi ne wanda makaɗa Muhammad Bawa da aka fi sani da Ɗan'anace ya yi.

  To kamar yadda aka sani akwai hanyoyi guda biyu da ake bi wajen nazarin waƙa. Wato hanya ta gargajiya da ta zamani. To bisa wannan waƙar zan yi nazari ne ta hanyar amfani da hanyar zamani don samun sauƙin fahimtar abubuwa da za su zame wa wannan aikin turke.

  Saboda haka wajen nazarin wannan waƙar zan bi waɗannan matakai ne kamar haka: 

  Hanyoyin nazarin waƙar

  1. Tarihin mawaƙi
  2. Bayanin diddigi/salsalar waƙa
  3. Zubi da tsarin waƙar
  4. Jigon waƙa
  5. Furucin gundarin jigo
  6. Warwarar jigo da shimfiɗarsu
  7. Salon waƙa

  Nazarin waƙar Garba Nagoɗi

  Tarihin Mawaki (Muhammad Bawa Ɗan'anace)

  An haifi Muhammad Bawa Ɗan’anace a garin ‘Yar tsakuwa ta ƙasar Gandi, wadda ke ƙaramar hukumar Raba a yanzu. Mahaifin Ɗan’anace ba mawaƙi ba ne, manomi ne. Ɗan’anace ya koyi ƙida ne a wurin ƙanin mahaifiyarsa Anace, wanda ya taso a hannunsa. Shi kuwa Anace, wani shahararren makaɗin ‘yan dambe ne, kuma shi ne sarkin ƙidan ‘Yar tsakuwa a wannan lokaci. Saboda tashin da ya yi a hannunsa ne, shi ya sa ya fara sana'ar ƙidin Dambe, tun Anace na da ransa.

  Makaɗa Ɗan’anace ya sha wahalar ƙida, kuma ya sha wahala kafin ya shahara. Domin da ya fara ƙidan Dambe, sai ya watsar ya shiga ƙidan noma. Ya sha wahala ƙwarai kafin ya karɓu a wurin mutane, har sai da ya yi waƙar Salisu Sarkin noman Yar tsakuwa. A ɓangaren noma dai wannan waƙa ita ta fara fito da shi.

  Daga nan ne, Ɗan’anace sai ya watsar da ƙidan noma, ya kama ƙidan Dambe gadan gadan. A cikin yawon ƙidan ne, ya ci karo da Shago a garin Mafara. Ɗan’anace kamar yadda ya shaida wa Farfesa Graham Furniss, ya tsani Shago a rayuwarsa. Shi kuma Shago Allah ya jarrabe shi da son Ɗan’anace. Duk abin da zai yi Ɗan’anace ya yi masa ƙida, ya yi, amma Ɗan’anace ya ƙi yadda ya saurare Shago. A wata shekara, sai Shago ya yi noma, ya tattara, duk abin da ya noma, ya kai wa Anace, wato kawun Ɗan'anace. Ya ce yana roƙon arziki, da ya sa Ɗan’anace ya yi masa waƙa. Anace ya umarci, Ɗan’anace da lallai ya yi wa Shago waƙa, inda shi kuma saboda biyayya ya amince. Dubi aruli: kafafuwan waka cikin arulin Hausa

  Salsalar waƙar

  Wannan waƙar, waƙar noma ce, kuma an yi ta ne ga Garba Nagoɗi wani shaharraren manomi a garin sokoto.

  Zubi da tsarin waƘar Garba Nagoɗi

  Zubi da tsari a waƙa na nufin hanyoyin da aka bi aka tsara waƙa, wato siffar waƙa. Misali, baitocinta da yawan dango da kowane baiti yake da shi da amsa-amonta, da yadda aka buɗe waƙar da kuma ta wane tsari aka rufe ta? Waƙar ‘Garba Nagoɗi’waƙar baka ce kuma mawaƙin bai farad a amshi ba duka da cewa a waƙar baka yawanci abin da mawaƙin ya fara shi ke zama amshin waƙar to amma a wannan waƙar ba haka ba ne mawaƙin ya fara ne a ɗiya ta ɗaya da ta biyu kamar haka:

  Na gode manoma abincinku da rani kuka cire nai

  Dakata mani Garba Nagoɗi,

  Waƙar Garba Nagoɗi na da gunduwowi (70) sannan tana da ɗiyoyi guda (123) sannan kuma duk abin da mawaƙin ya faɗa ‘yan amshin suna ƙarasa mi shi ne. sannan kuma akwai maimatawar wasu gunduwowi misali daga ɗiya ta (26) zuwa (34)

  Jigon wakar Garba Nagoɗi

  Jigo dai shi ne manufa ko saƙo da mawaƙi yake so ya sadar wa jama’a. saƙon wannan waƙar shi ne ‘kirari a kan noma’ wanda mawaƙin ya yi wa shi Garba Nagoɗi a harkar noma. Marubucin ya fara warwarar jigonsa daga farkon waƙar kamar haka:

  Na gode manoma abincinku da rani kuka cire nai

  Dakata mani Garba Nagoɗi,

  Mawaƙin ya yi amfani da ‘furucin jigo’ kamar haka:

  Garba ya yi noma, ya yi karatu,

  Ya je gida zai gai da na bawu.

  A gai da Nagoɗi,

  Mazan jiran noma da ya hayya mai gida gona,

  Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  Ya kuma ci gaba da jaddadawa daga ɗiya ta 7-9 kamar haka:

  Maza suna ƙaunarka Nagoɗi,

  Mata suna son Garba Nagoɗi,

  Ko ni ina ƙaunarka Nagoɗi.

  Salon Sarrafa harshe a wakar Garba Nagoɗi

  Salo hanya ce da mawaƙi ko marubuci ke bi domin isar da saƙonsa. Salo ya ƙunshi amfani da harshe da ƙulla tunani. salo shi ne asirin sihin waƙa (Yahaya,1999). Ko shakka babu an sami jeruntuwar tunanin mawaƙin a waƙar ‘GARBA NAGOƊI’, ya kuma yi amfani da miƙaƙƙen salo ya isar da saƙonsa kai tsaye (ya ɗinka tunaninsa, daki-daki. Misali, a gunduwa ta 5 kamar haka:

  Maza matu ciki, to sai ga nawa,

  Ku tai gida gaisheku magona mai gida gona

  Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  Ni wanga yaro ya shiga raina,

  Komi nikai sai nai magana tai mai gida gona

  Kantare na alkama Garba Nagoɗi. (gunduwa ta 10)

  Haka kuma a cikin wannan salo na shi ne ya yi wa kan shi kirari kamar yadda yake cewa a cikin waƙar kamar haka:

  To ni maraƙi nike ba ni da doka,

  Dodo na mai gona ka tarewa.

  Kammalawa

  Wannan aikin ya ƙunshi nazari ne kan waƙar Garba Nagoɗi wanda Muhammad Bawa Ɗan’anace ya yi masa a kan kirarin noma. To tun daga farkon wannan aikin mun yi ƙoƙarin kawo ma’anar waƙa, da kuma ma’anar salo. Daga baya kuma muka kawo hanyoyin da ake bi wajen nazarin waƙa. Daga ƙarshe ne muka kawo waƙar kana muka yi sharhi kan ta. Sannan mai karatu na iya duba cikas da illa da ake samu cikin arulin waka

  Manazarta

  Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000) Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation Ltd.

  Ambursa, M.S. (1986) Tarihin Mawaƙan Hausa, Kwalejin Ilmi ta Sakkwato.

  Ɗangambo, A. (1981) “Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa” Takarda da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

  Gusau, S.M. (1993) Jagorar Nazarin Waƙar Baka. Kaduna: FISBAS Media Service

  _________, (1995). Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kaduna: Fisbas Media Service.

  _________, (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

  Umar, M.B. (1980) "Waƙoƙin Baka: Mabuɗin Rayuwar Al’umma”. Takarda da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilmi, Argungu. 

  Rataye

  Waƙar Garba Nagoɗi ta Muhammad Bawa Ɗan'anace

  1. Na gode manoma abincinku da rani kuka cire nai
  2. Dakata mani Garba Nagoɗi,

                     Yau fa ruwa sun kai ga wuya na.

  1. Damina ta faɗi samari,

                     Kowa tsaya birni ya yi taushi mai gida gona.

  1. A gai da Nagoɗi,

                     Mazan jiran noma da ya hayya mai gida gona,

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Maza matuciki, to sai ga nawa,

                     Ku tai gida gaisheku magona mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Ni wanga yaro ya shiga raina,

                     Komi nikai sai nai magana tai mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Maza suna ƙaunarka Nagoɗi,
  2. Mata suna son Garba Nagoɗi,
  3. Ko ni ina ƙaunakka Nagoɗi,

                     Ba ni barin lada ta wuce ni.

  1. Ni wanga yaro ya shiga raina,

                     Komi nikai sai nai magana tai.

  1. Maza matucika, to sai ga nawa,

                     Mu je gida gaisheku magona mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Agaza mani Garba Nagoɗi,

                     Yau fa ruwa sun kai ga wuya na.

  1. Garba ya yi noma, ya yi karatu,

                     Ya je gida zai gai da na bawu.

  1. Inda karatu na hana kyauta,

                     Da ban zuwa gun Garko na roƙo.

  1. Ka ji daɗin nan duniyag ga
  2. Na nan ga duk ni ɗaya suka cewa,
  3. Kuma na nan ga duk ni ɗaya aka cewa,
  4. Kuma na nan ga duk ni ɗaya aka cewa,
  5. To yanzu na dai mai da gumi na

                     Yanzu dai na balle na hanga mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. To ni maraƙi nike ba ni da doka,

                     Dodo na mai gona ka tarewa.

  1. A yi dai ba don ta tsaya ba,

                     Taro ba haka dai taka so ba mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. In don jahannan ta ji kiɗi na,
  2. Dola kacin ba wani zaɓe,
  3. Arziƙi na kai mu waƙanga,

                     Ta tabba ba ni ka kiɗi ba.

  1. Kowaj ji daɗin na shiga roƙo,
  2. Damuna ta faɗi samari,

  Kowa tsaya birni ya yi taushi mai gida gona.

  1. A gai da Nagoɗi,

                     Mazan jiran noma da ya hayya mai gida gona,

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Maza matuciki, to sai ga nawa,

                     Mu je gida gaisheku magona mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Shi wanga yaro ya shiga raina,

                     Komi nike sai nai magana tai mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Maza suna kaunakka Nagoɗi,
  2. Mata suna son Garba Nagoɗi,
  3. Ko ni ina ƙaunarka Nagoɗi,

                     Ba ni bari lada ta wuce ni.

  1. Ni wanga yaro ya shiga raina,

                     Komi nikai sai nai magana tai mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Maza matucika, to sai ga nawa,

                     Mu je gida gaisheku magona mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Agaza mani Garba Nagoɗi,

                     Yau fa ruwa sun kai ga wuya na.

  1. Garba ya yi noma, ya yi karatu,

                     Ya je gida zai gai da na bawu.

  1. Inda karatu na hana kyauta,

                     Da ban zuwa gun Garba na roƙo.

    38. Ka ji daɗin nan duniyagga

    39. Na nan ga duk ni ɗaya suka cewa,

    40. Kuma na nan ga duk ni ɗaya aka cewa,

    41. Kuma na nan ga duk ni ɗaya aka cewa,

    42. To yanzu na dai mai da gumi na

                     Yanzu daina balle na hanga mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. To ni maraki nike ba ni da doka,

                     Dodo na mai gona ka tarewa.

  1. A yi dai ba don ta tsaya ba,

                     Taro ba haka taka so ba mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. In don jahannan ta ji kiɗi na,
  2. Dola kacin ba wani zaɓe,
  3. Arziƙi na kai mu waƙanga,

                     Ta tabba ba ni dai ka kiɗin ba mai gida gona

  1. Kowaj ji daɗin na shiga roƙo,

                     A zazzaga,

  1. A ce mutum ba komi ne ba,
  2. Ranar mutuwa to ya lalace,
  3. Ka so mutun sannan ka rasa shi
  4. Ka yi ƙira bai amsa ƙira ba,

                      Sai mutuwa ne adda hakan ga.

  1. Ka koma ƙira, bai karɓa ƙira ba,

                     Sai mutuwa ne adda hakan ga mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Ko can gidan dubu, nan ka ga suna,
  2. Tun dag ga kaka har da uwaye,

                     Wanga gida bai san wahala ba.

  1. Ga ni ina roƙonka Nagoɗi,

                     Inda irin gero a ga bara mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Bakura na zo, na yi kiɗi nai,

                     Ai kare ko bi ga kiɗi nai.

  1. Na kwana Dambo na yi kiɗi nai,

                     Ai kare ko bi ga kiɗi nai mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Na yamma ja ga Garba na Jano,

                     Mai cin hakkin gona da haƙora

  1. Agaza mani Garba Nagoɗi,

                     Yau fa ruwa sun kai ga wuya na.

  1. Ko ba ni gida, ko na tahiya ta,

                     Ko ayyi mai koyo a hwaɗa ma mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Ko ba ni gida, ko na tahi yamma,

                     Ko ayyi mai koyo a hwaɗa ma.

  1. Ai nan kiro arnan walala,

                     In ba kiɗa na ta da iyagi.

  1. Na gaji da yau ba ni iyawa,

                     Rikke kaban gambu ta yi auri.

  1. Nawa arme, ba ya macewa,

                     Sai na ga alƙali da idona mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Kwak auri matata da agola,

                     Kar ya bari ɗa na ya yi rama mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Agaza mani Garba Nagoɗi,

                     Yau fa ruwa sun kai ga wuya na.

  1. Kyawun Bahaushe noma,

                     Kyawun ba ruddufe yanka a rikice.

  1. Ha ba fa in ya yanke,

                     In bafaje ku jawo nai ku yi kai ma.

  1. A karkata,

                     Kowa ya rihicce

                     Yanzu don kowa ka na kai nai.                   

  1. Ka ga suna

                    Ya ya da ƙafafu maigida gona.

  1. Yai gaba kama,

                     Mazan jiran noma da yahayya.

  1. Na gai da wane ran nan ya ƙi taɓa man,

                     Hala ba kai ka hwaɗi a wazze.

  1. Taƙama da iko,

                     To wane in baka ba ni komai kar ka matsa min.

  1. Sarki adda gari, shi adda mutane,

                     Shi ka aje kuɗi kabi kani

  1. Ai wadda ag ga girman kai,

                     Hulla ba ta kyau garai sai dai ya yi malfa,

                     Ga asirin wane ya tonu.

  1. Kowayyi ɗa nai shi ka kiwo nai,

                     Ba a zuwa aure da agola mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

  1. Uwargida daɗa na tafiya ta,

                     Sai ya duk ya koma haɗa mu mai gida gona

                     Kantare na alkama Garba Nagoɗi.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

  Posted Fri at 4:38 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wan...

 • Yadda ake hada spring chin-chin

  Posted Thu at 10:16 AM

  Assalamu Alaikum. Barkan mu da warhaka. Ayau na sake zuwa mana da sabuwar makala ta girke-girke wacce ciki za mu koyi yadda ake soya spring chin-chin. Abubuwan hadawa Flour (4 cups) Baking powder (1 teaspoon) Butter (125grms) Mangyada Gishiri (1 teaspoon) Ya...

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

View All