Makalu

Bikin kalankuwa a Ƙasar Hausa

 • Da yawa daga cikin bukukuwan da Hausawa ke gudanarwa shekara-shekara, sukan yi su ne a cikin yanayi na musamman da zai dace don cim ma nasarar aiwatar da su a tsanake. Saboda haka ne za a ga cewa yawancin bukukuwa masu ɗaukar kwanaki ana yin su ne da kaka. Haka kuma a daidai wannan lokacin ne Hausawa suka fi samun sukunin gabatar da bukukuwan. Dalili kuwa shi ne saboda an girbe abin da aka shuka na albarkatun gona. wato kuɗi sun samu. Dubi abubuwa 10 da ke kawo mutuwan aure a kasar Hausa

  Bikin Kalankuwa biki ne na al’adar Hausawa, wato ba shi da wani tasiri da addinin Musulunci. Ana gudanar da shi ne shekara-shekara da Kaka bayan an kawar da amfanin gona. Wasa ne mai kayatarwa da nishaɗantarwa da kuma motsa jiki. Yawanci samari da ‘yan mata ne sukan shirya shi. kuma yakan samu karɓuwa a duk inda ake gudanar da shi, jama’a kan taru daga wurare daban-daban domin irin wasannin da bikin ya ƙunsa. Ta haka ne ma ake kyautata zaton ya samo sunansa wato "Kallon kowa”.

  Da zarar damuna ta fadi maza kan roƙi iyayensu su ba su. “gayauna” daga cikin gonarsu domin su noma abin da za su sayar da kaka su samu kuɗin shirin wannan bukin. ‘Yan mata kuma kan yi kiwon dabbobi su sayar su ma domin shirin wannan bukin, ko da yarinya ba ta yi wani ɗinki na kamar na sallah, za ka ga ta matsa wa kanta dole sai ta yi na bukin Kalankuwa. ‘yan mata kuma sukan yi tanadin abubuwa na musamman da za su yi wa samarinsu domin nuna bajinta da ƙauna da soyayya da sauransu.

  A wannan buki ne ‘yan mata ke bayar da ‘Badago’ ga samarinsu, su ma samarin su mayar shi da bayan kwana ɗaya. Yawanci akan zaɓi Sarkin Samari da Shugabar ‘Yan mata su huɗu tare da sauran abokai na ƙawaye domin yin shawarwari a kan lokaci da mawaƙa da kuma ire-iren ‘yan wasan da za a gayyata domin gudanar da wannan bukin. Yawancin Shugaban biki wato Sarkin Samari da Shugaban mata ke raba goron gayyata ga mawaƙa da maroƙa da ‘yan wasan da za a gayyata na nesa da na kusa bayan an tsayar da ranar da za a yi bukin, haka kuma a kasuwanni da ƙauyuka na kusa a matsayin gayyata. Haka kuma samari da ‘yan mata kan aika wa abokai da ƙawayensu na musamman irin wannan goron gayyatar. kuma su sukan zamanto masu masaukin baƙinsu.

  Idan lokacin ya matso ne ake gyaran wurin sauƙar baƙi da kuma filin gudanar da wannan buki. Kamar yadda yake waɗanda ako gayyata sun haɗa da yan kokawa da ‘yan dambe da ‘yan kiɗan duma da wasan dabo da ‘yan tauri da masu kiɗan kalangun ‘yan mata da sauran manyan baƙi.Dubi adabi: malamai a kasar hausa

  Yadda ake gudanar da bikin

  An fi gudanar da wannan bukin daga ranar Juma’a zuwa Lahadi akasarin wuraren da ake yin sa. Wannan zai ba kowa damar zuwa. Baƙi da masu wasanni na hallara ne tun ranar Alhamis da yamma domin safiya na yi ranar Juma’a bukin ke farawa. Samari da ‘yan mata na karɓar baƙinsu da a shirya masu abinci. Ana hidimomin abinci iri-iri wani lokaci Shugaba na mata haya don yin abincin baƙi kawai. A wannan ranar ne ‘yan mata ke ba samarinsu ‘Badago’ da yamma. wannan wani abinci ne na musamman da budurwa ke shirya wa saurayinta don nuna cewa shi take so. Yawanci takan haɗa da kaji da goro da sauran kayan lashe-lashe da tande-tanɗe da kuma tsotse-tsote.

  Bayan masu yin wasanni da safe sun gama da yammar wannan Jurna’ar ‘yan mata kan yi “Galma wuta”. A nan za ka ga ‘yan mata fiye da ɗari sun ci ado, sun taru wuri ɗaya tare da maroƙa. Kowace za ta ɗauki abincin da ta shirya wa saurayinta a kan ta ana tafe da makaɗa da maroƙa suna zagaya gari tare da kirare-kirare daga maroƙan baka. ‘Yan mata na rera waka da amshi, Bayan sun zagaye gari kaf sai a taro dukkan abincin nan wuri ɗaya a dandalin wasa. ‘Yan mata na komawa gida sai su sake cin wani adon da dare a fito wani taron, Wan kowa ya hallara sai makaɗan kalangu su Ɓarke da kiɗa.

  A nan ne kowace budurwa za ta yi shirin ba saurayinta ‘Badago’. Su kuma samari dama duk sun zo wurin wasa tare da baƙin abokansu, kowa zai zura ido ya ga ko shi budurwarsa za ta ba Badago ko wani. Yawancin ‘yan mata kan yi musayar Badago ne wajen raba shi. kowace ta faɗa wa ƙawarta saurayin da za ta ba abincinta. Saboda haka wannan za ta ɗauki na waccan.

  A nan filin za a nufi saurayi da abinci daga budurwarsa. zai yi murna da kuri ga sauran samari musamman abokan takararsa a wajen yarinyar. Duk saurayin da aka ba Badago zai raba shi nan take ga abokansa kuma za su ba shi ‘yai gudummawa gwargwadon hali shi kuma zai aje kwanukan wurinsa kafin ranar mayarwa ta zo. Daga nan sai a goce da kiɗan kalangu ‘yan mata na rawa samari na kashe kuɗi, wani na yin tambaya wani kuma na yin kari haka za a yi ta kashe kuɗi ana gasa har sai an ga wanda za a ƙuro. haka za a ci gaba da wannan gasar har sai kiɗa ya tashi.

  A rana ta biyu. wato ranar Asabar nan ma wasanni za su ci gaba. Da hantsi fili zai taru cika. Da zarar fili ya cika sai a ba ‘yan kokawa fili su fara. Makaɗa na ta kaɗa Gunduwa”, waɗannan wasu manyan ganguna ne masu ƙarar gaske. ana kaɗa wa ‘yan kokawa takensu suna titoya suna tsima suna ihu da kirari, suna tarar juna ana gwabzawa ana liƙa kuɗi. Wata sa’a kuma ana sa “Kazar ƙarfi” ga ‘yan kokawar. Ba a cika barin ‘yan gari ɗaya su kara ba, sai dai tsakanin na wannan gari da wancan. Wani sa’a kuma ana iya tambaya ga mai karfin gaske da akc ƙira ‘Ƙaura’. yawancin duk wanda aka naɗa Ƙaura ya gama yin kokawa sai dai ya zo kallo.

  Sauran wasanni da akan gabatar sun haɗa da na Gangi, na manoma, da na bishi (kiɗan mafarauta da wasan ‘yar gambara da wasan shanci wato na ‘yan dabo da sauransu. Bayan wasannin yamma idan an koma gida kowa ya ci abinci an huta. sai kuma a ɗunguma zuwa wurin kiɗan kalangu na ‘yan mata ba dare. A nan ne kuma samari aiki ya koma kansu.

  A daren ne samari za su mayar wa ‘yan mata kwanuknsu da aka kawo Badago. Saurayi kan sha wahala a wannan rana domin ba ya kai wa budurwa kwanukan haka nan, dole sai ya gwada irin tasa bajintar domin kuwa sai ya sayi kwalla ya zuba atamfofi da sarƙoƙi da ‘yan kunne da takalma da man shafawa da hoda da su turare da kayan tsotsc-tsotse har da su goro. wasu ma har da su rediyo. Idan saurayi ya kammala saye-saye yana tafiya da su cikin kwalla zuwa wurin kiɗa. Da ma ‘yan mata duk suna zaune kan kujeru a cikin fili sun ci ado, idan saurayi ya sa tambaya, yakan ba maroƙi wasu ‘yan kuɗi mai kiɗa kuma a ba shi masu ɗan yawa. Sannan ya ce a ba budurwarsa waɗannan kayan da wasu yan kuɗaɗe. Mai karatu na iya duba rage farashin aure a kasar Hausa: gyara ko batawa

  A nan ne ake cewa saurayi ya mayar da Badago. A irin wannan wuri ne ake yin ɗaurin ‘yan mata kowace budurwa ba ta da ikon ta tashi sai saurayinta ya kwance ta, a nan ma akan yi gasar har sai an ƙure wani. A cikin ‘yan mata kuwa duk wadda ta rasa wanda zai kwance ta akan yi mata ba’a da waƙe-waƙen rashin jin daɗi har kiɗa ya tashi. A ranar Lahadi ma wasanni kan ci gaba kamar sauran ranaku ammna daga nan ne bikin Kalankuwa ke zuwa ƙarshe.

  AL'ADA DA DAƊI GUN MASU ITA.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

  Posted Fri at 4:38 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wan...

 • Yadda ake hada spring chin-chin

  Posted Thu at 10:16 AM

  Assalamu Alaikum. Barkan mu da warhaka. Ayau na sake zuwa mana da sabuwar makala ta girke-girke wacce ciki za mu koyi yadda ake soya spring chin-chin. Abubuwan hadawa Flour (4 cups) Baking powder (1 teaspoon) Butter (125grms) Mangyada Gishiri (1 teaspoon) Ya...

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

View All