Makalu

Blogs » Zamantakewa » Rike sirri shine ginshikin zaman aure

Rike sirri shine ginshikin zaman aure

  • Wani ne mahaifinsa ya masa aure, sannan shi kuma ba ya son matar. Don tsabar kiyayya da yake nuna mata don su rabu, ba irin walakanci da ba ya mata. Amma ita ko ta kula da shi, abin da ta sa a gaba shi ne biyayyar da iyayenta suka ce mata ta yi wa miji tun daga gidansu shi ta ke yi. Ba ta taba kai karar mijinta a gida cewa ga abin da yake mata ba. Duk da haka, ba ta taba gaya wa iyayen mijin abin da yake mata ba, duk da duka da zagin da yake mata da maganganu na cin fuska, ba ta kulawa. Dubi macce 'yar wuta cikin matan aure

    Wata rana ya zo fita zai tafi wurin aiki, sai ta zo kamar kullum yadda ta saba, ta ce mishi maigida a dawo lafiya Allah ya ba da sa’a. Juyawarsa ke da wuya sai ya shimfida mata mari a fiskarta. Nan take hawaye suka fara zubowa, hannunsa har ya kwanta a fiskar. To ashe akwai wani a waje yana sallama, suna amsawa ashe abokin mijin nata ne ya shigo har cikin PALOUR. Nan take matar ta share fiskarta ta nuna kamar ba wani abu da ya faru tsakaninsu. Shi kuma ashe abokin ya ga fiskarta kamar ba lafiya ba, don idanunta sun yi ja ba kamar yadda ya saba gani ba. Sai ya tambaye ta, Amarya lafiya na ga fiskar haka idon ki ya yi ja? Sai ta ce “kwaro ne ya shiga mani idanu na muttsuke shi yake damu na yanzu a ciki. Sai bai ce komi ba, da ya ga tana kokarin boye wani abu, shi kenan sai suka sallameta suka fita, ta kuma cewa maigida Allah ba da sa’a sai kun dawo.

    Wannan abu da ta sake fada ya yi matukar ba wa mijin mamaki, nan take ya ce wa abokin nasa ya dawo ya ba wa matarsa nan hakuri kan abin da ya mata. Suna shigowa sai ta ce lafiya na ga kun dawo? Sai mijin ya kwashe duk abin da yake mata tun farkon zamansu da ita har wannan abin da ya kasance a wannan lokacin ya gaya wa abokin nasa, ta ce a’a maigida wallahi ba ka min komi ba ni kam. Shi dai abokin yana ta ba ta hakuri. Tun daaga wannan lokacin bai sake nuna mata walakanci ba, sai kuma ya fara nuna mata soyayya fiye da yadda take mashi.

    Da fatan za mu kasance daga cikin masu rike sirri dake tsakaninmu da abokan zaman mu daga mazanmu har matanmu, Amin. Sannan mai karatu na iya duba wannan makala da ta yi bayani ga wasu sirrantattun matsaloli dake kawo cikas a shimfidar aure

Comments

1 comment