Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Rayuwa da Zamantakewa » Ba boka ba malam: Mallaki mijinki cikin sauki

Ba boka ba malam: Mallaki mijinki cikin sauki

 • Yana daga cikin dabi'u na mata, neman hanyar da za su mallaki miji. Irin wannan lamari kan ba wasu mata matsala wajen gane yadda za su bi su mallaki miji cikin sauki. Wasu daga ciki gani suke, zuwa wurin boka ko malam a samu wasu siddabaru a matsayin taimako domin mallake miji shi ya fi sauki. Wasu sukan dace a hakan, wasu kuma akasin haka ne. Ga wadanda suka yi dace siddabarun ya yi masu amfani, zuwa wani dan lokaci kalilan zai daina amfani a koma kiyayya. Dubi: Rike sirri shi ne ginshikin zaman aure

  Mata ga hanya mafi sauki wajen mallakar miji wanda aka tsara bisa koyarwa manzo. Kamar yadda maluma na addini ke nasiha da tuni kan cewa, Aljannar mace na karkashin kafar mijinta. Kawai ki dukufa kan wadannan ababe da ma wasu don mallakar miji cikin sauki:

  • Ya kasance duk magana da zai fita daga bakinki mai dadi ne a kunnen mijinki wanda zai sa shi murmushi da jin dadi.
  • Ki kasance mai sakin fuska ga mijinki a duk lokacin da ya shigo gida ya same ki cikin frinciki ko da akasin haka ne.
  • Ki kasance a kullum kin dauki mijinki tamkar sarki ne ta wurin mutunta shi, da juriya wajen daukar laifinsa ya dawo kanki saboda bashi girma ko da ke ce da gaskiya.
  • Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi shi ne kofa na kowane sharri.
  • Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi hakkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matukar bai sabawa wa addini ba ki yi mishi.
  • Ki nuna wa mijinki komai naki nashi ne komai nashi kuma nashi ne, ki nuna baki da iko a kai sai abin da ya yi.
  • Ki kasance mai kula da abubuwan da yake dubawa a jikinki in ya shigo gida, ina idonsa ke kallo a jikinki. Bayan kin yi kwalliya. Idan kirji ne sai a gyara mashi su da kyau. Idan bayanki yake kallo sai nan ma a gyara domin a dauke masa hankali. In kuma kin tabbatar duk lokacin da ya dawo yana neman buta ne, to ki kula da sanya ruwa a cikin butar.
  • Ki kasan ce mai yawan godiya kan duk abin da ya kawo miki gida komin kankantar abin kar ki raina, sannan ki nuna masa kokarinsa a kana bin da ya kawo.
  • Kar ki sake ko ki yi kasa a guiwa wajen girmama duk wadanda kika san yana girmama su, kama daga iyaye har ‘yan uwa da abokan arzikinsa.
  • Kar ki yawaita tambayarsa daga ina kake ko me kake yi sai yanzu kake dawowa?
  • Ki kasance mai boye sirrinsa wajen iyayenki da sauran al’umma.
  • kar ki yadda duk lokacin da ya kiraki ki kawo masa wani abu ki tura wani ko wata ta kawo, ki je ki yi da kanki.

  Mai karatu na iya duba makalunmu na baya da muka wallafa akan makamantan wannan maudu'i, makala kamar aure a lokacin maguzawa

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Kansar mafitsara na daga cikin ire-iren kansa da su ka yawaita a cikin al’umma. Ita kansar mafitsara kamar yadda sunanta take ta na farawa ne daga cells din mafitsaran mutum. Mafitsara dai kamar yadda muka sani wani ma’aji ne a can kasan cikin mutum wadda amfaninsa shi ne adana fitsari. ...
 • Kansar mama ko cutar daji cuta ce ta kansa da take yaduwa a cells din nonuwar mace (breast). Baicin kansar fata (skin cancer), kansar mama ita tafi ko wacce irin kansa da mata ke dauke da ita a kasar Amurka. Kansar mama na iya kama mace ko na miji amma ta fi kama mata nesa ba kusa ba akan maza. Yad...
 • Bismillahir Rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai juya zukata yadda Ya so. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya kwadaitar kan hadin kai, kuma ya hana rarrabuwar kawuna. Kuma ina shaidawa lalle Annabi Muhammad bawan Allah ne, kuma manzonsa ne, wanda y...
 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
View All