Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Sunayen sha'awa na Hausawa

Sunayen sha'awa na Hausawa

 • Sunayen sha'awa su ne sunayen da aka same su da harshen Larabci amma ba na musulunci ba ne su, kuma an bar na Hausa. Sannan akasari irin wannan mata ne suka fi amfani da wadannan sunaye. Misali bayan an sa wa yaro ko yarinya suna mai asali daga cikin irin suna da musulunci ya zo da shi. Ya Allah uban ya yi wa mahaifiyarsa ko mahaifinsa ne takwara, sai kawai iyaye mata ba su son wannan sunan, gara su canza sunan, sai su tafi su dauko sunayen Larabci yadda ransu yake so ba don sun san ma'anar ba. Misali za su dauko sunan da suke ganin dan uwan sunan ne a wajen ma'ana ta Hausa.

  Misalai idan an sa ma ta Huraira sai su ga gara su kira ta da Shamsiyya ma'ana Umbrella (Lema), idan kuma Hajara ce, sunan matar Annabi Ibrahim sai su canza su kira ta da Samira ma’ana abokiyar hira ko wanin haka.

   Ga dai ire-iren sunayen sha’awa da ma'anarsu

  1. Asad                =          Zaki
   2. Fahad              =          Dare 
   3. Mal'una           =          Tsinanniya/la’antacciya
   4. Kamariyya       =          Wata
   5. Fauziyya          =          Mainasara
   6. Kalbu               =          Kare
  2. Saddam           =          Mairushewa
   8. Kullaybu           =          Dan kare
   9. Kursiyy             =          Kujerar zama
   10. Khatam           =          Zobe
   11. Ridah              =          Mayafi
  3. Ni’aal              =          Takalmi
   13. Kutayyib          =          Karamin littafi
   14. Niraan             =          Wuta
   15. Hamamatu       =          Tattabara
  4. Ghazala           =          Barewa
  5. Nuwaira          =           Karamin wuta
  6. Hammam         =          bayan gida/maisai (toilet)
  7. Samir              =          Abokin hira
  8. Laila/Lailatu     =           Dare

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Mene ne zazzabin cizon sauro? Zazzabin cizon sauro wato malaria cuta ce da ta ke damun mutanen duniya, musamman mutanen Afrika, kuma wannan cuta tana daya daga cikin cututtukan da suke damun mutanen Nigeria. Tana iya shafar yara, manya, tsofaffi, maza da kuma mata. Ma'anar maleriya Maleriya cuta ...
 • Maza da mata jinsi ne guda biyu mabanbanta da ke da bambancin halaye. Maza da mata suna da yanayi daban-daban, amma da fatan wannan makalar za ta taimaka wajen fayyace abubuwa da samar da kyakkyawar fahimta game da irin wadannan bambance-bambancen.  Ya kamata maza da mata su yaba wa wadannan ba...
 • Ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce da ke addabar mata. Akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da yan mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata da yawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce 'ciwon sanyi'. Mene n...
 • Mece ce cutar sikila (sickle cell disease)? Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban – daban, kamar su plasma, Red Blood Cells (RBC), White Blood Cells (WBCs), Platelets da sauransu. Cutar sickler ko amosanin jini tana faruwa ...
 • Brain tumor wani tudun tsiro ne na abnormal cells (wato wasu kwayin halitta) da ke samuwa a kwakwalwan dan adam.  Akwai kala daba-daban na wannan brain tumor din. Wasunsu basa kaiwa ga kansa (benign) sanna wasunsu kuma sukan kai ga zama kansa (malignant). Brain tumor kan fara ne daga kwakwalwa ...
 • Matashiya Zazzaɓin Typhoid (taifod) cuta ce mai saurin yaɗuwa a jiki wacce wata bacteria ce mai suna Salmonella enterica serotype typhi ke haifarwa. Zazzaɓin taifod yana da alamomi wadanda suka shafi cutar kuma suke nunawa. Manya-manyan alamominta sun haɗa da zazzaɓi, da ciwon gaɓoɓin jiki, da yaw...
View All