Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Amfanin ganyen yadiya ga mata masu juna biyu

Amfanin ganyen yadiya ga mata masu juna biyu

 • Yadiya: 'Raina kama ka ga gayya'. Yadiya wata ciyawa ce ko 'ganye mai yado' tana nan kaman ganyen dankali. Wannan ciyawar ba shuka ta ake yi ba. Tana fitowa ne a bayan kasa da ikon Allah. Ciyawa ce mai matukar muhimmanci ga al’umma wanda kuwa tuni wasu suka dauka a matsayin magani mai taimako, musamman mata masu juna biyu.

  Amfanin ganyen yadiya ga mata masu juna biyu

  Da zarar mace ta samu juna biyu, kuma ya kai wata bakwai (7), yana da kyau ta samu ganyen yadiya ta tafasa ta mayar da shi ruwan shanta har sai ta haihu. Domin kuwa yana zubar da duk wani datti dake tattare a mara ko zakin da mace ta sha lokacin da take dauke da juna, wanda wannan zakin duk zai zuba kafin ta haihu. Sai ya ba wa yaro damar fita cikin sauki. Sannan yana wanke dattin jikin jariri tun yana ciki. ana haifar jariri za a ga jikin shi ya yi tas. 

  Allah sa mu dace.

   

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Kansar mafitsara na daga cikin ire-iren kansa da su ka yawaita a cikin al’umma. Ita kansar mafitsara kamar yadda sunanta take ta na farawa ne daga cells din mafitsaran mutum. Mafitsara dai kamar yadda muka sani wani ma’aji ne a can kasan cikin mutum wadda amfaninsa shi ne adana fitsari. ...
 • Kansar mama ko cutar daji cuta ce ta kansa da take yaduwa a cells din nonuwar mace (breast). Baicin kansar fata (skin cancer), kansar mama ita tafi ko wacce irin kansa da mata ke dauke da ita a kasar Amurka. Kansar mama na iya kama mace ko na miji amma ta fi kama mata nesa ba kusa ba akan maza. Yad...
 • Bismillahir Rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai juya zukata yadda Ya so. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya kwadaitar kan hadin kai, kuma ya hana rarrabuwar kawuna. Kuma ina shaidawa lalle Annabi Muhammad bawan Allah ne, kuma manzonsa ne, wanda y...
 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
View All