Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Sunayen iskoki boyeyyu da dalilan kiransu da wasu sunayen

Sunayen iskoki boyeyyu da dalilan kiransu da wasu sunayen

 • A al’adar Bahaushe akwai wasu abubuwa da ake so a boye sunansu na asali a furta wani daban da ake iya ganewa. To sunayen iskoki na daga cikin wadannan abubuwa da ake yi wa lullubi. Dubi: Sunayen kabilun iskoki a wurin Bahaushe. A kasar Hausa, sunayen iskoki an kasa su kashi biyu:

  • Na gargjiya: wanda aka taras tun gabanin saduwa da Larabawa
  • Na zamani:- wanda aka samu sakamakon zuwan Larabawa (‘yan kasuwa da masu yada addini)

  To wadannan sunayen na gargajiya su ne:

  • Mutantani
  • Mutanen boye
  • Mutanen kogo
  • Kayehi
  • Kwankwamai
  • Masu abu
  • Su wa?

  Dalilin da ya sanya Hausawa kiranasu da wadannan sunaye shi ne

  Mutantani

  Wai sun yi kama da mutane amma ba mutane ba ne, don haka aka ciro sunansu daga ‘mutum’ ya koma ‘mutantani’ ma’ana kamar mutum amma ba mutum ba.

  Mutanen boye

  An ce wai asalinsu mutane amma aka boye su ga barin ganin mutane domin a razana mutane idan suna son su yi fitina ko wuce gonad a iri. A koyaushe muna tare da su, suna gainmu, amma mu ba ma ganinsu. Don haka ne ake kiransu mutanen boye.

  Mutanen kogo

  Wai a tarihin Bahaushe a riwayar bokayen kasar Hausa, lokacin da Annabi Adamu ya haifi 'ya'ya Allah ya nemi a zo da su wani wuri a gansu. Gabanin ya isa wurin ya zabe masu kyau mata da maza ya boye cikin kogon tsamiya ko kuka. Da ya isa da sauran ya nuna. Ya dawo ya dauki wadanda ya ajiye a kogo sai ya taras sun zama “iskoki”. A nan ya barsu a kogon ya tafi abinsa, don haka ake ce masu mutanen kogo.

  Kayehi

  Tsofi da suka kware da sanin halin iska da ayyukansu, da ‘yan  bori da masu tsafi su suka fi amfani da wannan suna na iskoki. Kayehi na nufin buwayeyye, mai aikin al’ajabi, da ban mamaki, da buwaya da ya saba wa al’ada, da abin da hankali mutum ke iya hasashe. Dga cikin abubuwa da ya sa ake kiransu kayehi akwai tashi sama da sauri, da karfinsu, da buwayar dan Adam da suka yi.

  Kwankwamai

  Bahaushe na ce wa iska kwankwamai saboda dalilai biyu. Na farko cikin kwankwamin kwakwalwa suke shiga su gigita mai hankali. Na biyu ba za a kira su da wannan suna ba face idan gadonsu aka yi daga iyaye (musamman wajen uba).

  Masu abu

  Wannan suna na nuna isa ne ga iskoki a kan komai suka sa gaba za su yi shi kamar kiftawa gira yadda suke son a ganshi kai tsaye nan take, sha yanzu magani yanzu. Wa zai iya wannan abu in ba masu abu ba?

  Su wa?

  ‘Yan bori da matsafa da suka kai matuka ga bauta wa ‘iska’ ba su Ambato sunayen can bakwai (7) da muka bayyana a baya, domin girmamawa da biyayya ga iska, sai dai su ce, “Su wa” suna haka ne wai gudun kar su ambaci sunan da zai sosa musu rayuwa su yi barna ko su fushi da su, ta yadda inda aka neme su wata bukata suka yi da zarar an ce su wanda ya yarda da su ya san su.

  Mai karatu na iya duba wasu daga cikin makalunmu, kamar: Al'ada: Imanin Bahaushe a kan fatalwa

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma. An yi wani attajiri da ke da dukiya mai yawan gaske, ana kiransa Abu Tammamu. Saboda yawan dukiyarsa, bai san iyakacin abin da ya mallaka na daga gidaje da gonaki da dabbobi da bayi da sauran kadarori ba. B...
 • Ku latsa nan don karanta shafi na 12 da 13. SHAFI NA 14 Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana." Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse." Fati ta amshi wayar ta...
 • Zamantakewar aure, zamantakewa ce mai wahala, matuƙar wahala kuwa. Sai dai da zarar ka fahimci tana da wahalar, sai ta zama mai sauƙi a gare ka. Domin fahimtar tana da wahalar shi zai ba ka damar neman iliminta. Shi kuma iliminta sai ya ba ka damar samun sauƙin ta. A shirinshi da ya saba gabatarwa ...
 • An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti a ranar Asabar 15-10-1938, a Abekuta ta jihar Ogun. Iyayensa manyan mutane ne domin Mahaifiyarsa Fummilayo Ransome-Kuti, 'yar gwagwarmaya ce, mai fafutukar kwato 'yancin mata. Mahaifinsa Isra'el Olodotun Ransome-Kuti, babban limamin coci ne, shugaban ...
 • Idan aka ce Hepatitis, to ana nufin ciwon hanta kenan a Hausance. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta na...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Dogaro Ga Allah Jari. Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba s...
View All