Makalu

Nahawu: Tsira da kumburar kalma a Hausa

 • Tsira da kumburar kalma na daya daga cikin ilmin ginin kalma, kuma su ne wadanda ake amfani da su wajen samarda wasu sababbin kalmomi domin bunkasa harshe, a bisa wannan ne ake cewa duk wani harshe daba ya iya tsirarwa ko kumbura kalma ta asali ana daukar wannan harshen tamkar mataccen harshe ne. Dubi: Hausa harshe ne ko kabila?

  Saboda haka idan ana maganar tsira da kumburar kalma, to tilas ne a danganta su da ilmin gini kalma, wanda kuwa shi wannan ilmin ya danganci abubuwa ne da suka hada da: Saiwar kalma da dafi. To don samun kyakkyawar madogara kan wannan aikin, zan so na bayyana tare da yin sharhi kan wadannan muhimman abubuwan wajen haifar da sabon ma’ana ta kalma. 

  Dafi: - dafi shi ne irin karin da ake yi wa kalmomi wadda ake hadawa a farko ko a karshe, ko kuma a tsakiyar kalma, domin ya ba da wata ma’ana. Ana yin amfani da karin ne a kalma domin ya kumbura ta, ko kuma a gina wata sabuwar kalma.

  Dafi ya rabu kashi uku (3) ne kamar haka:

  1. Dafa-goshi
  2. Dafa-ciki
  3. Dafa-keya

  Dafa-goshi:- shi ne abin da ake lika wa saiwar Kalmar, ko kari a farko don a gina kalma. Misali:

  Dafa-goshi      Saiwa    Kalmar

  1. Ba-           Gobir        Bagobiri
  2. Ba-          katsin        Bakatsine
  3. Ba-          Hausa        Bahaushe
  4. Ba-          Kano          Bakano
  5. Ba-          Chamba     Bachambe
  6. Ma-          Wak          Mawaki     
  7. Ma-          Dink         Madinki
  8. Ma-          aiki           Ma’aiki      
  9. Ma-          gini           Magini
  10. Ma-          Saka         Masaka

  Dafa-ciki:- tsiara ce da ake samu a tsakiyar kalma, wato cikin kalma ko lika wa saiwar kalmar daga ciki don a gina wata kalma. Misali,

          Saiwa          dafa-ciki

  1. Bawa           baiwa
  2. Baki             bakake
  3. Fari              farare         
  4. Garma         garemani
  5. Garwa          garewani
  6. Gurgu          guragu
  7. Kurtu           kurata
  8. Kwalba         kwalabe
  9. Murfi            murafe
  10. Karfe            Karafa                 

  Dafa –keya:- tsiara ce da ake samu a karshen kalma domin ya kumburata, ko kuma shi ne abin da ake lika wa saiwar kalmar daga karshe don a gina kalma. Misali:

           Saiwa     dafa-keya

  1. Aboki       abokantaka
  2. Adali        adalci
  3. Boka        bokanci
  4. Dangi      dangantaka
  5. Magaji     magajiya
  6. Mugu       muguntaa
  7. Mutum    mutuntaka
  8. Shekara   shekaru
  9. Yaro         yara
  10. Yaro         yarinya

  Mai karatu dubi: Bitar ma'anar kalmar Hausa a karni na 21

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Dec 7

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All